Sashe 72
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanya suka tsaya jikin wani Restaurant, kallon ta ya yi hannunsa cikin nata ya ɗan murza ta turo baki tana kallon gefe, gefen wuyanta ya sumbata ya ce “Me kike son ci?”
Girgiza kai ta yi ya janyo daf da shi ya ce “Me ya faru na ga kin canja fuska?” Ya faɗa yana kallon in da take bi da ido, wata matashiyar budurwa ya gani ita da mahaifinta da mahaifiyarta sun saka ta a tsakiya suna ciyar da ita, idan wannan ya ba ta wannan ya ba ta sai shagwaɓa take zubawa son ranta. Fuskarta ya juyo gareshi ya ga hawaye na yin fareti a bisa kumatunta, cikin damuwa ya kwanto da ita jikinsa yana bubbuga mata baya. Sai da ya ji ta daina shashshekar kukan sannan ya ɗago da ita cikin tsananin kulawa yana share mata hawaye.
“My wife ƙi Kwantar da hankalinki don Allah ba na son ki saka damuwa a ranki har wani abu ya same ki, ba gani ba a tare da ke ni zan zame miki uwa, uba, miji, yaya, dangi, duk abin da kike so zan miki shi komin wahalar shi in dai kuɗi yana sayan shi.”
Komawa ta yi jikinsa ta ƙara fashewa da kuka murya na rawa ta fara magana.
“Amour ba za ka gane ba, Idan na ga iyaye na kulawa da ɗiyansu sai naji inama ni ce da nawa iyayen, sai kuma na tuna ni ɗin marainiya ce gaba da baya duk da na, samu gata da kulawa a wajen kakannina sun aurar da ni a in da aka ci gaba da kula musu da ni har na gane ni wace ce, lokacin da na gane ba su ba ne iyayena na shiga firgici da tashin hankali marar musaltuwa, a yadda Salim ya sanar da ni labarin mahaifana ba ƙaramar girgiza na yi ba, mamata ta ɗanɗani azaba biyu a lokaci ɗaya ta yi naƙuda ta haifi iya runguma ta kawai ta yi ta sadaukar da rayuwarta domin ta tseratar da tamu rayuwar, a wannan yanayi na ciwon haihuwa suka kashe ta. Babana kuma ni ban sani ba sun kashe shi ko sun tafi da shi ne? Har yanzu ina jin a jikina wata rana zan ga mahaifina domin a yadda na samu labari fantsama suka yi lokacin da aka kawo wa ƙauyenmu hari kowa yana gudun ceton rai, mamana ta tafi da yayuna da kuma ni da nake ciki tana tsaka da naƙuda ta, ya Allah ka jiƙan ta da rahama ka haskaka ƙabarin ta, babana idan yana raye Allah ya nuna mini shi kafin numfashina ya tsaya.” Ta ƙarashe maganar tana sa sabon kuka, ganin budurwar nan da iyayenta ya ƙara karyar mata da zuciya..
Wani mugun tausayin ta ne ya mamaye mishi zuciya, rarrashin ta ya dinga yi ya fara mata nasiha.
“My wife ƙi ɗauka wannan ita ce ƙaddararki ki rayu ba tare da ganin fuskar iyayenki ba ko da sau ɗaya ne, ki gode wa Allah da kika samu gata aka kula da tarbiyarki sannan kika auri miji jajirtacce kamar Salim, bayan Allah ya ɗauke miki shi kin yanke hukunci ba za ki ƙara aure ba har abada, a tunaninki ba za ki samu miji kamar Salim ba amma da yake Allah maji ƙai ne ya ba ki ni a matsayin miji na biyu, ko ta hana ai ya kamata ki daina kukan maraici domin Allah haskaka rayuwarki da ni'imomi kala-kala, dan haka ki ce Alhamdu Lillah.” Ya ƙarashe maganar yana yin kissing lips ɗin ta ya tsotsa kaɗan ya saki yana bin ta da kallo. Dogon numfashi ta ja sosai ta ji hankalinta ya kwanta ta ɗago kai za ta yi magana ya dora hannunsa a kan bakin hakan ya sa ta hadiye abin da take son faɗa. Fita ya yi ya zagaya ya buɗe mata ƙofa ta fito tana gyara zaman hijabinta, bodyguard ɗin sa suka firfito su shida biyu a gaba huɗu a bayan su haka suka shiga restaurant ɗin. Wajen da aka tanada domin cin abinci suka nufa mutane har sun fara ɗaukan su a waya, ita dai taƙi sakin jikinta sai manne mishi take tana ɓoye fuskarta dan kar su ɗauke ta, gane hakan ya sa ya buɗe handbag ɗin ta ya cire mata niƙaf ya kare ta ta ɗora, sai a sannan ta iya zama da kyau.
Masu kawo abinci suka zo su biyu suna tambayar su me za a kawo musu? Kallon nau'ikan abincin Sultan ya yi ya nuna wani gasashen nama, miƙa mata daftaran ya yi a hankali ya ce “My wife me kike so bayan gasashen naman?”
Wani juice wanda aka haɗa da madara ta nuna ta ce “Shi kadai nake so.”
To ya ce mata ya faɗa musu adadin da suke buƙata.
Suna zaune Andizo ta kalli mutanen da ke wajen can ta hango wasu mata biyu na son zuwa in da suke amma bodyguard sun hana su, da mamaki ta kalli Sultan ta ce “Amour su waye ke son zuwa in da kake ake hana su?”
Ɗago kai ya yi suka haɗa ido da Jennifer ita da Ruby, haɗe fuska ya yi ya sa aka sanar da masu restaurant ɗin su musu takeaway ba za su ci abincin a wajen ba, hakan ya yi mata daɗi domin ita Allah ya mata kishi mai tsanani musamman a kan Sultan, ji take ta ma fi jin kishin sa fiye da lokacin da ta yi rayuwa da Salim.
Bayan an gama musu komai suka biya kuɗin sannan suka wuce, sai da ya saka ta a mota ya juyo ya ji ta damƙo rigarsa ta baya, sarai ya gane ita ce sai ya juyo tare da faɗin “A'uzu billahi!”
Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta yi saurin sakin shi, bai ce da ita komai ba ya juya ya wuce ya shiga mota suka bar wajen.
Wani irin zafi ta dinga ji ƙirjinta na mata sai hasaso Jennifer take tana mamaki tsaurin idon ta, can kuma sai ta ce ƙila ko sun san juna ne shi ya sa hakan ya sa ta daure fuska tashi daga jikinsa ta koma can gefe tana hura hanci..
Ranar kasa gane kanta ya yi abincin da suka sayo ta ce ta ƙoshi ta shige ɗaki ta rufe, babu kalar rarrashin ta da bai yi ba amma taƙi buɗe mishi ƙofa sai shi kaɗai ya kwana a ɗakinsa.
Washe gari bayan Sallar Isha'i tana zaune tana kallon wani move wayarsa da ke aje a caji ta ji an kira, tashi ta yi da nufin ta kai mishi wayar amma, ganin sunan Jennifer ɓaro-ɓaro a kan screen ɗin wayar ya sa ta yi jifa da wayar ji kake tasss! Zama ta yi jagwab a kan kujera tun kafin sun zo gia jiya take ganin kiran Jennifer na shigowa a wayarsa.
Tsaye ya yi a kanta cikin wani irin yanayi ya rasa me take so ya faɗa wanda za ta yarda yanzu ba sa tare da Jennifer, ga shi Jiya ta azabtar na nisanta kanta da shi da ta yi da kyar ya yi bacci yana ta juyi.
Ji ta yi kamar ana kallon ta ta ɗaga kai suka haɗa ido da shi, tashi ta yi da sauri ta wuce ya bi bayan ta yana faɗin “My wife please ki tsaya mu yi magana.”
Kafin ma ya ƙarasa faɗa tuni ta faɗa ɗaki ta datse ƙofar da kye, bugawa ya dinga yi tana ji ta yi banza da shi har ya gaji ya dawo palo yana kallon yadda wayar ta yi ɗaiɗai, girgiza kai ya yi ya sunkuya ya dauki sim ɗin ciki ya kira mai aiki ya ce ta share gurin shi kuma ya wuce daƙinsa..
_Maman Nusaiba ce_
[7/22, 2:11 AM] Ummu Amjad: ADZ
51
Abu kamar wasa yau dai sun kwashe sati uku suna zaune a irin wannan yanayin, ta daina mishi komai idan ma ta ji motsin shi a palo ba ta fitowa sai ta yi zaman ta a ɗaki, gabaɗaya ta ji garin duk ya ishe ta saboda ko waya ba ta ita ballantana ta kira wani ko ta yi kallo, ga shi ba ta san yadda za ta kunna tv da ke cikin ɗakin ba. A ɓangaren Sultan kuwa ba ƙaramar azabtuwa yake ba, ya bi hanyoyi da dama domin su haɗu amma bai yi nasara ba, yana son ya fahimtar da ita su yi magana a nutse amma fir taƙi daɗi idan ya matsa da buga mata ƙofa sai ta tayar da aljannu tana ihun ya matsa mata daga bakin ƙofa, ganin abin na son fin ƙarfinsa sai ya tattara ta gefe ya zuba mata ido.
Sanye take da riga da sket na atamfa orange colour ta kafe ɗauri a gaban goshi, gashin kanta da ya sha gyara ta daure shi ta yo baya da shi, ba ta yi wata kwalliya me yawa ba hoda ta shafa ta sa kwalli sai man kaɗan da ta sa lip, sosai ta yi kyau ta ɗauki mayafi mai ɗan girma ta ɗora a kafaɗa tana kallon kanta a madubi. Ji ta yi ba za ta iya fita da mayafi ba dama can ita ba ma'abociyar sa shi ba ce, amma dan ta ba shi haushi dai ta zari handbag ɗin ta ta yo waje tana ɗora wani ɗan sirrin agogo a hannunta na hagu, ɗayan hannun kuma wani babbar warwaro ne mai kyau sai kyalli yake haka ta fito fuska daure tana taku ɗaiɗai kamar wata sarauniya.
Tun kafin ta ƙaraso ƙamshin turaren da ta sa ya kawo wa hancinsa ziyara ya lumshe ido cikin wani irin yanayi ya ce “Oh my wife kina son kashe bawan Allah.”
Miƙewa ya yi yana sakar mata murmushi ita kuma tana aiko mishi da harara har ta iso ta tsaya, sam ba ta son su fita tare amma ba yadda ta iya tun da kiran Limat ne, a gaban ta ya tsaya yana bin mayafin da kallo cike da mamaki. “My wife ya kuma na ga kin ɗauko mayafi?”
Wani irin kallo ta mishi ta kawar da kai gefe tana hura hanci, kai ya girgiza ya juyo da fuskarta ya ƙura mata ido, fisgewa ta yi ta dawo kan kujera ta zauna.