Sashe 32
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baya ta yi a ta faɗi Hajiya Babba ta yi saurin taro ta tana faɗin “Subhanallahi! Me ke faruwa Khadija?”
Jikinta né ya ɗauki rawa amma ta riƙe wayar gam tana kokowa da numfashi da yake ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinta, da gudu Hassana ta je ta ɗebo ruwa ta kawo Mamma da ke tsaye kanta suna tambayar ta ta amshi ruwan ta shafa mata a fuska tana salati. Dogon numfashi ta sauke baki na rawa ta ce “Mamma zan mutu ki taimake ni ya dawo ni ba na son tafiyar nan da ya yi.”
Zama Mamma ta yi a gefen ta ta amshi wayar ta ga an kashe, Andizo ta ɗora hannu biyu a ka ta fashe da kuka tana miƙa wa Mamma hannu ta ce “Don Allah ki bani wayar na kuma kira naji, Wallahi zuciyata za ta buga in ban ji muryarsa ba..”
Ganin yadda ta birkice sai Mamma ta ba ta wayar tana kallon ta cike da tausayawa, saurin danna mishi kira ta yi kafin ma ya gama ringing farko aka ɗaura. Ƙaran bindigar da ta ji ya sa ta ƙara miƙewa tsaye ta ce “Hello don Allah kai waye? Kuma ina mai wayar yake?”
A ruɗe ya amsa da cewa “Abdoul ne.”
Dafe ƙirji ta yi ta ce “Alhamdu Lillah har naji sanyi ina yake mai hankalin! Ba shi na masa magana.”
A wannan lokacin fuskar Abdoul ta yi baƙi kamar an zuba mishi gawayi, yana cikin wani rami wanda bishiyoyi biyar suka kewaye ramin, ɗago kai ya yi ya leƙo waje ya ga abokan aikinsu sun gama kashe 'yan ta'ada sai mutum ɗaya da suka kama aka ɗaure shi a jikin wata bishiya. Sauke kai ya yi ya miƙe tsaye ya fito, ganin shi ya sa da gudu suka nufo shi ɗaya daga cikin su ya ce “Ina Oga yake? Fatan dai komai lafiya ko?”
Girgiza musu kai ya yi yana musu alama da su yi shuru, gane hakan ya sa duk suka koma gefe wasu suna harhaɗa bindigun 'yan ta'adda da duk wasu muyagun makamai. Dawowa ya yi cikin ramin ya kira mutum biyu suka fito da Salim da jini ke ta zuba ta gefen cikinsa, kansa ma duk ya ɓaci da jini dai runtse ido yake yana cije lips. Kwantar da shi suka yi a filin wani ya buɗe jakar da ke goye bayanshi ya fito da maganin wanke ciwo ya iso gaban Salim, kama shi suka yi suka cire rigar wadon ma suka cire sai na ciki suka bar mishi nan aka shiga ƙoƙarin wanke masa ciwuka.
Dogon numfashi Abdoul ya sauke ya koma gefe ya sauke wayar jin yadda Andizo ke ta rusa kuka ana rarrashin ta, girgiza kai ya yi ya kashe kiran ya sake kira ta ɗauka, a murya can ƙasa ya ce “Khadija ki kwantar da hankalinki Salim yana nan da ransa ciwo ne ya ji a ƙafa ana wanke masa ne, idan suka gama zan kira ki na ba ki shi ku gaisa kin ji ki daina kukan kar ciwo kema same ki, kinga idan kika yi haka ba zai ji daɗi ba idan ya samu labarin kukan da kika yi..”
Ɗankwali ta sa ta goge fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da majina da hawaye, tana ajiyar zuciya ta ce “N.. Na fasa kukan ka ji Hamma Abdoul karka faɗa mishi na yi kuka, amma don Allah ku dawo gida yau ni ba na son wannan tafiyar taku.” Ta faɗa wasu hawayen na silalowa daga kwarmin idanuwanta.
Wani abu mai ɗaci Abdoul ya haɗiye ya kalli in da Salim yake magashiyan sai aiki ake a kanshi, wayarsu ta ma'aikata ce ta soma ƙara Abdoul ya kalli ɗaya daga cikin su ya ce ya ɗaga shi kuma ya dawo ga Andizo.
“Khadija ki ba wa Mama waya ba mu da lokaci duk cikinmu wayar wannan ta Salim kaɗai ce aka ba mu izinin kunnawa, to yanzu da an jima za ki ji ta a kashe bani Mamma na mata magana.”
Jiki a saɓule ta miƙa wa Mamma wayar ta kwanto kan cinyarta, har yanzu jikinta bai daina rawar sanyi ba. Kara wayar Mamma ta yi ta ce “Abdoul wai don Allah me ke faruwa ne da ku? Ina fatan dai lafiya ko?”
Zama ya yi ya jingina da bishiya ya ce “Mamma gamu nan za mu dawo gida ƙila gobe da safe mu sauka, amma dai gaskiya..” Ya yi shuru dan bai san wani yanayi za ta shiga ba.
“Amma dai me Abdoul ? Ka sanar da ni komai karka wani damu ni fa musulma ce nasan ƙaddarar Ubangiji a kan bawansa..”
Hakan ya ba shi ƙwarin ya soma magana cikin wani kalar yanayi.
“Mamma mun yi nasara kama waɗannan 'yan ta'adar da shekarun baya suka addabi ƙauyukan da ke kewaye da mu ciki kuwa har da ma haifar su Khadija, yau dai mun ci nasara da kansu duk mun kashe shegu mutum ɗaya muka bari da rai shima dan ya yi bayani ne da ya gama mu kashe shi, amma maganar gaskiya Mamma Salim sai addu'a.”
Gaban Mamma ne ya buga da ƙarfe ta ɗan runtse ido dan kar Andizo ta gane akwai matsala, gyaran murya ta yi ta ce “To ina jin ka Abdoul ci gaba”
“Ba zan iya ce miki komai ba Mamma sai mun je gida, yanzu dai ga su nan ana ƙoƙarin tsayar mishi da jinin amma yaƙi tsayuwa, saura minti ɗaya su ɗauke connexion ɗin wayar ki faɗa wa Khadija Salim ya ce zai dawo tun da ba ta so.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “To shi kenan Abdoul Allah ya kaimu goben sai an jima.” Ta faɗa tana kashe wayar.
Kallon ta duk suka yi ta danne kukan da ke ƙoƙarin zo mata da kyar ta ce “Khadija ki daina kuka Salim ya ce zai dawo tun da ba ki son tafiyar..”
Murmushi ta yi ta amshi wayar ta ce “To Mamma gara dai ya dawo dan ni gabaɗaya hankalina bai kwanta da tafiyar nan tasu ba..”
Sai da Hajiya Babba ta lallaɓa ta ta raka ta banɗaki ta sa mata ruwan wanka ta ƙulle kofar ɗakin sannan ta dawo palo, Aminatou da tuni jikinta ya ba ta mijinta ba lafiya ba ta yi tagumi tana kallon su, so take ta yi kuka ko za ta ji sauƙin abin da take ji a zuciyarta amma kukan ya ƙi zuwa, kallon da Mamma ta yi ta ruƙo hannayenta ta ce “Nasan ke kin san me ake kira da ƙaddara da kuma haƙuri da juriyar abin da kake so in wani abu ya same shi, ke ba kamar ita ba ce kina da hankali da hangen naisa shi ya sa na ce ma ki zauna, domin ko na miki dabara ba za ki yarda ba irin na Khadija ke babba ce, mijinku dai ya samu raunika sosai a jikinsa shi ya sa gobe za su dawo, amma a yadda Abdoul yake mini magana da wahala ma in mutuwa Salim ya yi ya ƙi ya sanar da mu sai dai ya zo mana da gawarsa, amma dai Allah ya kaimu goben karki damu kin ji ki yi ta addu'a karki saka tashin hankali a ranki.”
Wani irin abu ne mai nauyi ya danne wa Aminatou ƙirji ta runtse ido tana faɗin “Lahaula wala ƙuwata illa billahil aliyun azim! Allahuma ajurni fi musibatee wa'akalifili khairan minha! Allah ya ka dubi marayun Allah ka tashi kafaɗun mijinmu, shi ne gatanmu Allah ya dube mu kar ya tafi ya bar mu a lokacin da muke tsananin buƙatar shi, Allah sarki ashe shi ya sa tun shekaranjiya ya sa mu a gaba yake kallo kar mai mana kallon ƙarshe, waiyo Allah ni Aminatou ni ba kaina nake ji ba halin da Khadija za ta shiga in ta ganshi a mawuyacin hali..” Ta sa kuka marar sauti ta ƙunshe bakinta da gefen mayafinta, Husaaina ta ruƙo ta tana rarrashin ta itama kukan take.
Haka suka zauna jugum-jugum har dare Abba ya dawo daga kasuwa ya same su a haka, tambayar su ya yi ko akwai abin da yake faruwa, Hajiya Babba ta ja shi ɗakinsa ta sanar da shi komai. Shi kansa ya firgita da wannan labarin abin sai ya tuna mishi da shekarun baya ya yi baya ya zauna yana ta salati, nasiha Hajiya Babba ta dinga mishi ya samu sassauci sannan ta fito..
Ranar a gidan ba, wanda ya yi baccin kirki kusan a zaune suka kwana sun ƙagara gari ya waye.
Ƙarfe takwas daidai Abdoul ta kira Mamma ya sanar mata sun iso amma su same su a asibiti dan an yi gaba da Salim, to ta ce mishi ta kashe wayar ta ɗauko hijabi suma su Hajiya Babba duk suka shirya, so suke su tafi kafin Andizo ta farka sai dai suna gama shiri ta fito itama sanye da hijabi tana kumbura baki ta ce “Shi ne za ku tafi ku barni?”
Kamo hannunta Hajiya Babba ta yi suka nufi harabar gidan. Babbar motar gidan suka shiga Ahmad ne ke ja shi kuma Abba tuni ya riga su tafiya..
Babbar asibitin garin suka isa inda tun daga bakin asibitin sojoji ne a kewaye da motocinsu, zaro ido Andizo ta yi tana leƙawa ko za ta ga Salim a cikin waɗanda suke tsaye amma har suka zo shiga ciki ba ta ga mai kama da shi ba ma. Suna paka motar wani soja ya buɗe musu suka fito yana gaishe su suka amsa, shi ya musu jagora suka isa har bakin ƙofar ɗakin da yake ciki. Zama suka yi suna jiran a ba su izinin ganin shi, Abba ya kira Abie yake sanar mishi suna asibiti Salim ne ya samu jikkata, hankalin Abie a tashe ya ce zai dawo Niger Abba ya ce a a ya zauna tukun kar ya dawo, ba dan ya so ba ya haƙura..
Ƙarfe 11:am likitocin da suka dukufa a kanshi suka fito ɗaya bayan ɗaya, na karshen ne ya tsaya a wajen su ya ce “Su waye iyayensa.”
[6/11, 2:25 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
33
Da sauri Mamma da Abba suka amsa a tare “Mu ne iyayensa likita.”