← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 75

Sashe 51

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyara zama Hajiya ta yi ta ce “Tun daga wannan rana ba mu sake yin waya da su ba har aka shafe sati ɗaya sai abin ya fara damun mu, Zulai ta ƙara kiran babanta amma sai a ce mata wayar a kashe dole ta haƙura muka zuba wa sarautar Allah ido, sai da aka cika kwana goma sai ga Salim ya dawo daga Maraɗi wajen karatu, yadda muka ga ya shigo abin sai ya ba mu mamaki domin da shigowar shi da yin kukan sa duka lokaci ɗaya ne. Hankali a tashe na tarbe shi ina tambayar shi lafiya ko bai samu jarabawar ba ne shi ya sa yake kuka? Nan yake sanar da mu baƙin labari, “Hajiya su yaya ne aka ce za a kawo su gida suna hanya, wai sun samu raunika su duka shi ya sa za su dawo gida.”
Salati muka dinga yi Zulai har ta fara kuka muka zauna muna jiran mu ji sun kira sun ce an kai su asibiti,amma har yamma ba a kawo su ba har sai bayan magariba aka kira Salim suka sanar da shi ga su nan shigowa unguwarmu. Tun kafin ma su iso ƙaran jiniyar motocinsu ta sanar da mu zuwan su muka fito harabar gidan duk muka yi tsirko-tsirko, ko 'yan unguwar sai da suka tabbatar ba lafiya ba duk da sun saba jin jiniyar motar su Alyasa'a idan za su fita, amma na wannan karon sai ya ba, su mamaki yara suka fito suka biyo motar hr cikin gida. Wasu daga cikin sojoji suka fito aka buɗe mota suka kama suja fito da ɗaya, yadda muka ga an rufe su tuni jikina ya ɗauki rawa muka ƙarasa wajen su, hannuna na rawa na buɗe wanda yake kusa da ni, fuskar Alyasa'a na gani kamar yana murmushi gabaɗaya gefen kansa ya yi raga-raga an rufe wajen amma duk da haka jini bai daina zuba ba, tun daga nan naji kamar zan kurma ihu saboda na tabbatar Alyasa'a ya riga da ya mutu na rufe na yi gaba na buɗe ta kusa da shi. Ziya'ulhaƙ autana shi na gani cikin jini fuskarsa ta ɓaci da jini, na rushe da kuka ina kiran sunansa ina jijjiga shi amma ina rai ya yi halinsa, kamar ana tura ni na yi gaba ma buɗe na kusa da shi na ga ƙanen Zulai ne shima babu kyan gani na buɗe ta ƙarshe in da baban Zulai ne, ranar a gidan babu wanda bai suma ba saboda tashin hankalin da muka shiga musamman ma Zulai sai da aka ɗaure ta kamar mahaukaciya ta koma sannan aka ɗauke su aka shiga da su ciki, Musalle da Saddiƙu da kyar aka rarrashe su suka wanki Alyasa'a da Ziya'ulhaƙ da ƙanen Zulai da babanta, ranar mun ga tashin hankali wanda ba mu taɓa gani ba, domin Salim da ya yi arba da gawar yayansa da ƙanen mahaifinsa tun da ya suma har dare bai farka ba, haka sallace su aka kai su gidansu na gaskiya, su kansu mutanen unguwar nan sun sha kuka suna ta faɗin alkhairin Alyasa'a, sai bayan kwana biyu Salim ya farfaɗo nan ma wai tashin hankali muka ƙara shiga, ya ƙi cin abincin ya ƙi shan ruwa sai cewa yake shi dai a kai shi wajen yayansa ba mutuwa ya yi ba, da kyar Saddiƙu ya rarrashe shi ya ɗauke shi daga gidan ya kai shi can wai waje da ban saboda yadda yake sa mutane kuka da kalamansa, Zulai si ta dawo kamar kurma sai sai an, kwantar da ta sai an tayar ba cin abinci da kyar ake samu ta ci loma ɗaya shima sai ƙanwata ta yi da gaske take yarda ta amsa, ƙarshe ma kamar ciwon hauka ya so samun ta ta dinga surutai tana faɗin “Yarona da ƙanena da babana Wallahi ba su mutu ba dan ba ku sansu ne y sa kuka binne su da ransu.” Surutai dai makamantan haka ta dinga yi, sai da muka sa malamai suka dinga mata addu'ar dangana da kyar ta taimakon Allah muka samu ta dawo haiyacinta. Har aka yi shekara da mutuwar su Alyasa'a amma kullum sai Zulai ta yi kuka da zarar ta fito palo ta ga photonsa shi da Salim, hakan ya sa Musalle ya cire photon har na ɗakinta, duk wani abu da ya, san zai tayar mata da hankali game da Alyasa'a duk ya ɗauke ya ɓoye, muna ji ta dinga nema muka yi shuru har ta gaji ta haƙura. Da Salim ya gama karatu ya ce shi aikin soja yake so yana son ya kashe waɗannan 'yan dajin da suka kashe mishi ahali, Zulai ta yi rantsuwa da girman Allah ta ce in dai Salim ya ce sai ya yi soja to sai dai ya rama mata nononta da ta shayar da shi kuma babu si babu ita, hakan ya sa hankalinsa ya tashi ya ba ta haƙuri ya aje maganar ba dan ya haƙura ba. Bayan shekara ya sake tayar da maganar yana lallaɓa Zulai ta barshi ya yi aikin soja dan ya ɗauki fansar abin da aka yi wa su Alyasa'a nan ma taƙi, sai da ya haɗa ta da mamanta ta zo har gida ta mata nasiha ta nuna mata suma din kawai kwanansu ne ya ƙare shi ya sa suka mutu ta rabu da shi ya yi aikin tun da yana so, a ranar ƙin amincewa ta yi sai da mamanta ta yi zuwa uku tana rarrashinta sannan ta haƙura ta bar Salim ya yi aiki, ranar ya yi farin ciki ya zo ya mata godiya sai kawai ta sa kuka tana faɗin “Wato kai dai ka dage sai ka yi aikin sojan nan Salim ko? Kaima so kake a kashe ka kamar yadda aka kashe su Baba ? Ni dai Allah ya gani hankalina ya kasa kwanciya da aikin nan naka Salim, amma ba komai Allah ya dafa maka ya sa ka yi nasara a kan abin da kake son yi.”
Ya ji daɗi sosai ya mata godiya, bayan kwana biyu suka tafi tirenin ɗin aikin soja. Kullum sai ya kira a ƙalla sau biyar yana faɗa mana duk abin da aka musu, amma da zarar sun shiga aiki ba a samun shi, da ya zo shekarar ƙarshe in ba hai ya kira mu ba ba a iya samun shi Zulai ta so ta ɗaga hankali sai da Ahmad ya mata bayani sannan ta yi shuru. Haka ya dawo gida cike da tarin nasara an ɗauke shi aikin soja, muka taya shi murna ya kama aiki cikin nasara da sanin makamar aiki. Shekarar shi biyu da fara aiki aka aika su inda su Alyasa'a suka je ba su dawo a raye ba ranar Zulai ta tashi hankali ta ce ba zai je ba sam, da kyar aka rarrashe ta ya tafi. Sanin halin da ya baro ta da ya sauka ya kira ta ya ce ta mishi addu'a za su shiga daji yanzu daga nan ma'aikatar sojoji, sosai muka mishi addu'a sannan ya kashe. Bayan kwana biyu sai ganin shi muka yi ya dawo Zulai ta yi murna sosai ganin ɗanta ya dawo a raye, sai washegari ya sanar da mu sun yi nasarar kashe duk yan ta'addar da ke cikin dajin da suka addabi ƙauyukan yankin, mun ji daɗi sosai inda daga wannan tafiyar ne aka mishi ƙarin matsayi, wannan shi ne abin da ya faru.” Ta faɗa tana kallon Khadija, hawaye ta gani suna ta zarya kan fuskarta ta ce “Nasan dole ki yi kuka Khadija game da wannan labarin.”
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Gaskiya na tausaya muku musamman Mamma mutuwar mutum uku a lokaci ɗaya, shi ya sa ashe ta dinga kuka da ta ga Salim an nade mishi jiki da bandeji ba ta sani ashe shima tafiyar zai yi kamar su.” Ta ɗora kanta a kan kafaɗar Hajiya tana tuna shi..
Shi kanshi Sultan duk dauriyar shi sai da hawaye suka zubo mishi, irin wannan mutuwar tsayawa a rai gareta, hon ya yi aka buɗe mishi get ya shiga ciki. Suna fita Hajiya ta sa Maigadi ya ɗauko kayan su kuma suka nufi ciki, kiran sunanta ya yi sai ta tsaya taƙi juyowa, ganin haka sai ya girgiza kai ya iso inda take. Turaren da Halisa ta ba shi ya miƙa mata ya ce “Ki bai wa Ahmad wannan turaren ni ba irin wanda nake fesawa ba ne.”
Ɗago jajan idanuwanta ta yi ta zabga mishi harara ta ce “Ba zan kai, ba kai ka ba shi mana ba abokinka ba ne? Dan naje ya ƙara yi min muguntar da ya saba.”
“Ba sai kin je inda yake ba ki ba wa Hajiya sai ta ba shi, yanzu ni gobe jirgin safe zan bi na tafi Nigeria don Allah ki kula da kanki karki ƙara yin tunani mai zurfi, sannan kike cin abinci kinga yadda kika rame wuni ɗayan nan? Zan ke kiran ki amma ki kula idan na samu lokaci zan dawo lokacin da zai, zama na ƙarshe dan zan zo, da Mom da kuma kawuna a yi maganar aurenmu, yanzun ma dan kawai kin ƙi ba ni amsa ne da kafin na koma za a yi komai a gama na ɗauke ki mu tafi na kula da ke. Bye bye sai wani lokacin ko?”
Sunkuyar da kai ta yi ta amshi turaren ta ce “Na gode idan ka je ka gaishe mini da Mom da Farrah.”
Jinjina kai ya yi ya ce “Na manta kawo hannunki kuma ki rufe idanuwanki.”
Ji ta yi ba za ta iya mishi muso ba a wannan karan ta miƙa mishi hannun ta runtse ido tana addu'ar kar wani ya gansu, yatsarta ta kusan babbar ta ji a sa mata wani abu ta yi saurin buɗe ido, zobe ce sabuwa dal a cikin ƴar akwatin ta ruwan gold sai sheƙi take, baki sake take kallon shi sai kuma ta kalli zoben har ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba sai da ta ji karan camera ya ɗauke ta a photo, ƴar dariya ta yi ta ce “Thank you so much zan wuce ina jin jiri.”
Hanya ya ba ta yana bin da kallo har ta shige ciki sannan ya koma motarsa ya wuce. Duk abin da suke a kan idanun Ahmad yana ganin su daga tagar dakinsa kwafa ya yi ganin ta shigo shima sai ya fita daga ɗakin ya yo palo..
Chapter 51 · 0% Book details