Sashe 31
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari rana na ɗagawa Andizo ta fita gari yawo ganin gari, ai kuwa duk inda ta bi yara cu sai sun bi bayan ta ana faɗin “La ga Andizo ta zama ƴar gayu har ta kusa haihuwa.”
Ita kuwa in ba dariya ba babu abin da take yi in ta ji sun ce mata haka, sai da ta zo saitin da Saminu yake sayar da fanke ta yi saurin jan hijabinta ta gyara, kallo wajen ta yi sai ta ga sai Lado a zaune a wajen kayan, nufar shi ta yi tana wani haɗe fuska. Lado na ganin ta ya saki baki yana kallon ta, yau Andizo ce yake gani ko kuwa dai gizo ne take magana ga ta ta zama babba har da hijabi a jikinta? Sake murza ido ya yi ya ga dai da gaske wannan fuskar ta Andizo ce. Tana isowa bakinta ɗauke da sallama ya amsa, kuɗi ta miƙa mishi ta ce “Lado a ba ni fanke a talatin, amma ina Saminu yake ne?”
“A a sannu da zuwa Andizo mutanen birni, Saminu ai tun da kika bar garin nan shima ya bar gari, shi ne da zai tafi ya bar mini kayan sana'arsa nake yi.”
Fuskar damuwa ta yi ta ce “Allah sarki Saminu, amma dai neman ilimi ya tafi ba yawon duniya ya tafi saboda da rashina ba ko?”
Girgiza kai ya yi ya ce “Gaskiya neman abu biyu ya tafi, ya haɗa kudaɗensa bakiɗaya jika ɗari da tamanin ya tafi da su, ya ce zai je can birni ya fara neman sana'a sannan zai koma makaranta boko da arabi, amma ya ce duk wata uku zai ke zuwa ganin gida..” Ya faɗa yana miƙa mata fanken da ya ƙulla.
Amsa ta yi tana faɗin “Allah sarki Saminu, to Ubangiji ya ba shi abin da ya je nema.”
Amin Lado ya ce ta sake miƙa mishi kuɗin ya ce “Ki barshi ai ko ba komai kina da daraja a wajen abokina ba zan karɓi kuɗinki ba.”
Godiya ta mishi sannan ta juya ta yi gidan su Hajaru.
Wanki ta samu Hajaru na yi ai kuwa ta zo a guje za ta rungume Andizo Innar Hajaru ta yi saurin shiga tsakanin su ta ce “Ke meye haka? Ba ki ga yadda take ba ne?”
Ja baya Hajaru ta yi tana kallon Andizo, ganin ta da ƙaton ciki sai ta sa dariya ta matso kusa da ita tana fadin “Ƙawata ashe mun girma? Kai Allah sauke ki lafiya zan sake zuwa Niamey a karo na biyu.”
Dariya Andizo ta yi ta kama hannunta Innar Hajaru ta shinfida musu tabarma suka zauna, ita kanta mamakin Andizo take ganin yadda take magana a nutse kamar ita ba.
Ganin Innar Hajaru ta tashi Andizo ta matso kuma da Hajaru ta ce “Wai Hajaru ashe Saminu ya bar gari.”
“Hmm bari kenan ƙawalliya, Wallahi ba ki ga ba yadda Saminu ya koma abin tausayi duk wanda ya ganshi sai ya yi kamar ya zubar masa da hawaye, bayan tafiyar ki rashin lafiya ta kwantar da shi ashe ciwon sonki ne ke addabar zuciyarsa kuma ya hana Lado ya faɗawa kowa, har asibiti aka kwantar da shi a nan ne ma suka ce yana gaf da kamuwa da ciwon zuciya matsawar bai daina zurfafa tunani ba, amma yaƙi hi kullum photonki a ƙirjinsa yake kwana da shi ciwo ya sake dawowa, sai da ya ga Innarsa na kuka tana rokon shi ya rufa mata asiri shi kaɗai gareta kar ya mutu ya barta sannan ya rage abin da yake, to ƙarshe dai ta yanke shawarar tura shi wajen wani abokin babansa da ke can Niamey yana kasuwanci, ke har ma da makaranta ta ce idan ya je duk ya koma ya samu ilimi mai inganci dan wasu abubuwan da yake har da rashin ilimi ma..”
Goge hawaye Andizo ta yi tana jinjina irin son da Saminu yake mata, addu'ar samun nasara ta mishi sannan suka ci gaba da hira. Ba Ta dawo daga gidan su Hajaru ba sai kusan magariba, gabaɗaya labarin Saminu ya sa jikinta ya yi sanyi jin yadda ya sha wahala duk saboda da ita, ranar ko Salim bai samu fuskar yin waya da ita ba da ya kira sai ta yi shuru sai ya ɗauka network ce ya kashe y sake kira, sai da suka yi haka kusan sau goma sannan ya gane yau 'yan surutun ba sa kanta ya haƙura ya barta. Shi ɗin ma dama Aminatou ce ta takura mishi sai ya kira mata ita sun gaisa ta ji ya ta sauka shi ya sa ya kira..
Kwanci tashi ba wahala wajen Ubangiji har Andizo ta yi sati a garinsu, tun safe aka haɗa mata kayanta kamar sun san Salim zai zo da wuri. Ƙarfe goma na safe sai ga shi ya iso, ba ta wani ja da nisa ba duk ta musu sallama suak ce sai sun zo suna tana rufe fuska ta shiga motar, tsarabar da suka mata aka jibge mta ita a bayan mota suka tafi su Maigari na ɗaga musu hannu..
Tun da suka kama hanya da suka gaisa ta soma ba shi labarin abubuwan da ta tarar a ƙauyen sai bacci y yi gaba da ita, kallon ta ya yi ya girgiza kai ya ce “Nana Khadijana kenan ke bacci ba ya miki wahala ba ruwan ki.”
Ko da suka iso gida ba ta tashi ba ya kashe motar ya fito, zagayowa ya yi ya buɗe set ɗin ta ya ɗauke ta cak suka yo part ɗin ta. Aminatou da ta fito ta sa dariya tana faɗin “To ke kuma sai bacci ina nan ina ta jiran ki, to tashi maza.”
Buɗe ido Andizo ta yi ganin ta a gidanta ta waro idanu ta ce “Kai, wai har mun zo kenan?”
“Ga, zahiri kin gani.” Cewar Aminatou suka yi part ɗin ta.
Zama suka yi suka dasa hira Salim ya yi tagumi yana kallon su sai murmushi yake, ganin kallon ya yi yawa Aminatou ta ce “Haba mijinmu ko mun canja maka ne wai? Na ga tun da yau ta yi ka sa ni a gaba kake kallo, yanzu kuma Khadija ta dawo ka saka mu duka a gaba ka yi tagumi kana kallo lafiya dai?”
Sauke tagumin ya yi ya ce “Wallahi ba na so na tafi na barku har na kwanan wata ban ganku ba, da za su ɗauki wani a madadin hakan da ya mini daɗi.”
“Haba dai Mai hankali shirin Allah, ai sati ɗaya kamar kwana ɗaya ne a wajen Allah nan da nan za ka ga ya yi ka dawo gida. Fatan mu dai Allah ya kaiku cikin sa'a ku dawo da tarin nasara..” Cewar Andizo.
Dariya ya yi ya ce “Ke wai ba za ki daina ce mini mai hankali shirin Allah ba?”
Dariya suka yi a tare Andizo ta ce “To ai gaskiya ce mai hankali ne kai ɗin.”
Tashi ya yi ya fita su kuma, suak ci gaba da zama..
Da dare bai bari sun yi girki ba ya ɗauke su suka tafi wajen cin abinci suka ci a can, har da takeaway ya yo musu ya ce ko ya tafi da safe su cikar su yi girki, su dai da ido suke bin shi ya ja su suka nufi wani babba shagon sayayya, duk wani abin da yasan za su buƙata sai da ya sayo musu wanda har ya je ya dawo zai ishe su sannan suka dawo..
Gajiyar da Andizo ta yi tasa yau da ya zo mata ta yi kamar gawa ta bar shi shi kaɗai ya yi komai da kansa, da kyar ta tashi ya taimaka mata suka yi wanka sannan suka koma bacci.
Washegari ƙarfe takwas ya shirya suka fito bakin mota duka 'yan gidan suka mishi rakiya, Ahmad shi ya ja motar zai kaishi airport din su da duk wani sojan da yake cikin wannan tawagar tafiyar ta su tuni ya je, shi ne ma ya ɗora minti biyar a kan lokacin da aka diba musu, sai da Ahmad ya ga tashin jirginsu sannan ya dawo gida.
Ko da ya zo Andizo tana kuka wiwi da ta ganshi ta miƙe da sauri ta ce “Har ya tafi ko?”.
Dariya ya yi yana zama ya kalli Aminatou ya ce “Ke ba ki kukan ba Aminatou, ai sai da suka tashi sama sannan na dawo gida.”
Addu'ar sauka lafiya suka mishi sannan suka ci gaba da lamuransu, ita kuwa Andizo wuni ta yi ranar tana kuka da an jima sai ta danna mishi kira sai a je wayar a kashe take, gabaɗaya ta hana su sukoni Ahmad y samu ya lallaɓa ya ɗauki wayar Salim ɗayar da ya ba shi ya ce ya dawo da ita gida, text message ya turo mata ya ce _“Ma femme Idan muka huta zan kira ki video call kin ji, kuma in naji labarin kin yi kuka zan daina kiran ki har na dawo.”_
Gani suka yi kawai ta sa dariya hawaye na bin kuncinta ta kalli Aminatou ta nuna mata saƙon ta ce “Kin gani ko Adda ya ce zai kira video call da ya huta.” Ta faɗa tana zama a kusan Aminatou.
Murmushi ta yi ta kalli Ahmad ya mata ƴar ido ta kawar da kai, ta ga lokacin da yake tura mata saƙon. Tun da ta samu, wannan saƙon sai ta ji zuciyarta ta samun salama ta kwanta bacci y ɗauke ta..
Har kusan La'asar ba ta farka ba, ana kira Sallah ta zabura a firgice ta tashi tana salati, Hajiya Babba ta yi saurin riƙe ta ta ce “Subhanallahi me ya faru Khadija?”
Dafe ƙirji ta yi ta ce “Ina wayata take?”
“Ga ta can a caji da kika sa.”
Saurin sauka ta yi daga kan kujera ta je kan wayar ta miƙa hannu za ta ɗauka kamar jira ake ta tsaya sai ga kiran Salim ya shigo, da hanzari ta ɗauka cike da farin ciki ta ɗaga kiran ta ce “Hello mai hankali an je lafiya ya gajiya?”
“Ba shi ba ne...
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/10, 11:08 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
32