← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 75

Sashe 56

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yamma tana kwance a kan gado tana amsa kiran da Umma ta yi mata su Nour sai kwaranci suke mata tana ganin yadda suke ta guje-guje, gyara wayar ta yi ta tashi zaune ta ce “Khadijata kina so ki zo wajena?”
Dariya Umma ta yi ta ce “To ita da ba magana ta iya ba taya za ta ce miki eh ko a'a?”
Murmushi ta yi ta musu sallama ta kashe wayar, kanta ne ya ƙara nauyi ta dafe kan tana runtse ido, kira ne ya shigo wayarta ta ɗago da wayar, ganin mai kiran ta ja tsaki ta aje wayar amma kafin ma ta ɗauke hannu aka sake kira nan ma taƙi ɗauka, bayan ta gama ringing sai ƙarar shigowar saƙo ta dafe kai ta ɗauki wayar tana duba saƙon.

_“Khadija ni kike katse wa kira? Me na miki haka? Tun da na dawo kin ƙi ɗaukan kirana Allah ya sa dai ba wani abu marar kyau ba ne ya faru, please ki ɗauka ina so zan nuna miki wani abu ne.”_

Tsaki ta ja gani take duk ya bi ya takura mata, kiran video call ne ya shigo ta gyara ɗaurin ɗankwali sannan ta ɗaga kiran tana ɗaure fuska ta kalle shi.
Babu riga a jikinsa gashi ne kwance a faffaɗan ƙirjinsa baƙi ya yi luf-luf sai iskar AC ke fifita shi. Da wani irin yanayi ta yi saurin runtse idanuwanta tana kawar da kai gefe, dariya ya yi ya tashi zaune ya ɗago mata hannu ya ce “Hello.”
“Wannan ɗin wani irin abu ne ka sa riga in kana so na ci gaba da riƙe waya.”
Singlet fara ya ɗauko ya saka ya yi baya da gashin kansa kamar na mata har ma yafi na wata macen, gyara zama ya yi ya ce “My wife ina son na nuna miki kofin da muka ci jiya da na kira ki amma kika ƙi ɗauka, yanzu zuwa nan da sati biyu zan tafi Nigeria kinga sai mu zo da Mom har can garinku ayi maganar aurenmu.” Ƙara kallon ta ya yi ganin yadda ta rame ya ɗora da cewa “Ko ba ki da lafiya ne? Me yake damun ki?”
Kasa ce masa komai ta yi sai kallon shi da take, yadda ya yi magana cike da fara'a sai ta ji jikinta ya yi sanyi sunkuyar da kai ta yi ta ce “Please ba na jin daɗi yau ma an kaini asibiti sai an jima zan kwanta na huta, zan tura ma text yanzu da na kashe.”
“A'a tsaya ina so na nuna miki wani abu da na sayo miki nasan zai miki kyau sosai.”
Tagumi ta yi tana jiran ta ga me zai nuna mata, tashi ya yi ya fita bai ɗauki lokaci ba sai ga shi ya dawo hannunsa ɗauke da leda. Zama ya yi yana murmushi ya ce “Kinga wannan abayar jiya da na fita sayayya na ga ta mini kyau, shi ne na ce bari na ɗauko miki tabbas za ta dace da ke ya kika ganta?”
Kallon a bayar ta yi black colour mai masifar kyau sosai ta ji abayar ta birge ta, amma tuna yanzu tana gaf da shiga gidan wani sai ta ɗan ɗaure fuska, ganin yadda ta canja fuska sai ya yi saurin faɗin cewa “My wife ba ta miki ba ko? To kwantar da hankali zan bayar da ita na sayo miki wadda ta fi wannan kyau.” Ya faɗa yana kallon ƙofa jin ana kwankwasawa, kallon Andizo ya yi da take yi shirin kashewa ya ce “One minute zan kira ki abokina ne ya zo ni kuma ba na son ya ganki har sai lokacin da na kawo ki nan.” Ya faɗa yana tashi.
Tsaki ta ja ta kashe wayar ta tura mishi saƙon da ta faɗa masa ta aje wayar ta kwanta gaban ta na dukan uku-uku, wani irin gudu zuciyarta take ba ta san ba wani kalar hauka zai yi mata yanzu. Kamar ya san me take tunani sai jin kira ta yi ta duba ta ga shi ne sai taƙi ɗauka, jin sanyi yana shigar ta ta janyo bargo ta lulluɓa tana jin saukar ɗumin ruwan hawaye kan kumatunta. Kasa daurewa ta yi da kiran dan yau so take a yi ta ta ƙare ya kamata ta sanar da shi gaskiyar abin da ke faruwa ko zai fita daga rayuwarta ta huta. A hankali ta yi picking call ɗin ta yi shuru ta ji me zai faɗa, saukar numfashinsa ta fara ji a majiyarta ta yi saurin runtse ido, wani irin yanayi take ji gabaɗaya neman rasa nutsuwarta take tun ma kafin ya yi magana.
“Kha.. Khadija.. Khadijaaaa!”
Ya ja sunan da wata kalar murya da ba ta taɓa jin irin ta ba a gareshi, ƙara runtse ido ta yi tana addu'a ita dai burin ta ya taimaka ya rabu da ita, numfashi ta ji yana fitarwa da ƙarfi so yake ya mata magana amma sam ya ƙasa, can ta ji muryar wata mace tana faɗin “Mr J are you OK?”
Can kuma ta ji macen tana ruri ta ɗan yi nisa da wayar, shuru ta yi jin ba kowa sai motsin Sultan, can kuma ta fara jin muryoyi dayawa suna tambayar Sultan me ya same shi? Daga haka ba ta tsaya jin komai ba ta kashe wayar ta yi jifa da ita ta kwanta. Idan ta tuna yadda yake kula da ita sai ta ji ba ta mishi adalci ba, amma idan ta tuna ɗabi'unsa sai ta ji hankalinta ya rabu gida biyu, ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kanta da ya yi mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse hake take ji. Nan da nan zazzaɓi da ciwon kai irin na dare suka dawo mata ta ƙara lulluɓa da bargo rawar sanyi..

Har bayan sallar isha'i ba ta fito ba sai dai su zo su leƙo ta daga bakin kofa su gani tana bacci sai su koma, yayin da ita kuma ta tsinci kanta a wani yanayi bacci take amma kamar tana farke, so take ta tashi amma wani abu mai mugun nauyi ya danne mata ƙirji da ta yunƙura ta tashi sai ta ƙasa, jikinta ji take kamar ana zuba mata tafasashshan ruwan zafi idanuwanta ne kawai take suke aiki yadda ya kamata.

Ƙarfe 8:am Hajiya ta gaji da rashin ganin Andizo ta tashi ta nufi ɗakinta, kwankwasa ƙofar ta yi ta ji shuru hakan ya sa ta tura ta sa kai ciki, yadda suka bar ta jiya a lulluɓe haka ta same ta ko juyi ba ta yi ba daga wajen sai mamaki ya kama Hajiya, a hankali ta yaye bargon tana faɗin “Khadija wannan ɗin wani irin bacci ne tun jiya har yanzu ba ki tashi ba?”
Da kyar ta iya buɗe idanuwanta da suka yi jaju, bakinta ya buɗe ta kalli Hajiya sai hawaye shar, Hajiya ta kama ta ta tayar da ita tana jera mata sannu jin jikinta da zafi, ruwan da ke can gefe take kallo tana son ta ce za ta sha amma maganar ta gagara. Kallon inda take kallo Hajiya ta yi sai ta ga ruwa ta jingina ta da jikin gado ta isa ta ɗauko ruwan ta buɗe ta iso ta kafa mata a baki, bismillah ta yi a zuciyarta ta soma sha har ta shanye duka ruwan gorar. Kallon ta Hajiya ta yi sai kuma ta ce “In da buɗe bakinki Khadija mu gani.”
Da kyar ta buɗe Hajiya ta ga duk ƙuraje sun cika mata baƙi ga su nan felas, saurin fita ta yi ta nufi ɗakin Ahmad tana kiran shi ta ji shuru sai ta tuna ya tashi wajen aiki. Palo ta iso ta samu Abba na shirin tafiya ta ce “Tsaya Musalle karka tafi.”
Juyowa Abba ya yi ya ce “Hajiya lafiya na ganki duk a firgice?”
“Ina fa lafiya yarinyar nan Khadija ce rai a hannun Allah, ga ka yadda ta kara ramewa? Yanzu haka bakinta cike yake da ƙuraje kamar wata yarinyar goye, muje maza a mayar da ita asibiti.”
A tare suka shiga ɗakin Abba, Hajiya, Mamma Har da su Hassana.
A ƙasa suka same ta ta kifa kanta ƙasa hakan ya sa Hajiya ta yi sauri ta kama ta tana faɗin “Ka gani ko faɗowa ta yi daga kan gadon.”
Hijabi Mamma ta saka mata suka ɗauke ta su duka suka nufi waje Abba na biye da su, sosai hankalinsa ya tashi ganin yanayin da ƴar amanar tasu take ciki. Mamma da Hajiya da su aka tafi su Hassana suka koma ciki jiki ba daɗi, suna zama a palo Hussaina ta dubi Hassana ta ce “Gaskiya ni fa ban yarda Khadija Wannan ciwon nata ba na zuwa asibiti ne, ki duba ki ga daga jiya zuwa yau yadda ta koma kamar ƙashi anya ba aljannu ba ne suka shafe ta ba mu sani ba muke kaita asibiti?”
Tagumi Hassana ta yi tana gyaɗa kai ta ce “To nima dai abin da na gani ba za a gwada yi mata ruƙiya ba, bari Abba ya dawo shi za mu samu da maganar ko kuwa na Hajiya za ta yarda da maganarmu nan take fiye a Abba.”
To Hussaina ta ce suka ci gaba da zama.

Suna zuwa asibitin Mami ta ƙarbe su suka shiga cajin lafiyar Andizo, sun kusan minti talatin sannan Mami ta fito ta nemi da su bi ta office su duka suka bi bayanta. Bayan ta ɗan yi rubuce-rubuce a kan takardar da ke gaban ta ta kalle su ta ce “Hajiya gaskiya na gama cazar lafiyar Khadija ban ga ba komai ba sai abin da na musu bayani jiya da safe, sai ƙurajen baki kaɗai yanzu na mata allurar bacci an jima za ta farka za ku iya tafiya Allah ya ƙara lafiya.”
Duk shuru suka yi suna ta mamaki yadda suka kawo ta nan a galabaice wai a ce ba komai sai dai zazzaɓi da ƙurajen baki duk wannan firgitar da ta dinga yi tana mimmiƙewa kafin su iso asibitin? Godiya suka mata suka fito suka zauna suna ta jero wa Andizo addu'ar samun lafiya.
Chapter 56 · 0% Book details