Sashe 70
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari misalin karfe 10:00am suka tashi daga baccin da suka koma bayan Sallah asuba, wanka suka shiga a tare wanda ya ɗauke su fiye da minti talatin, domin wasan ruwa suka dinga yi kamar wasu yara ya biye mata, idan ya watsa mata itama ta watsa mishi sai da suka gaji tukun suak yi wankan suka fito.
Suna fitowa suka samu an jera musu lafiyayyan abinci sai ƙamshi yake, Andizo ta shafa cikin da ya ke a ɗame kamar ba ta kayan ciki, nasa hannun ya kai ya shafa ya yi fuskar tausayi ya ce “Ya aka yi wife?”
Narke mishi ta yi a jiki domin yadda ya yi maganar da wani salo sai da wani irin shok a jikinta, “Amour yunwa.” Ta faɗa tana turo baki gaba, daukan ta ya yi da hanzari suka wuce wajen cin abinci. Zaunar da ita ya yi sai ga mai aiki ta iso ta gaishe su suka amsa ta haɗa musu tea mai kauri, kula ta buɗe farfesun kayan ciki ne ta zuba musu ta sake buɗe ɗayar kular ita kuma shinkafa da kaza ce sai tashi ƙamshi take, lumshe ido Andizo ta yi yawunta ya tsinke tana jikinsa a kwance mai aikin ta gama yin saving ɗin su ta wuce. Ɗago da ita ya yi ya fara ba ta tea ɗin, sai da ta shanye tas sannan ta janyo farces shima ya fara ba ta, ba ta ci mai yawa ba ta kawar da kai gefen ya kalle ta da mamaki ya ce “My wife ba dai Kim ƙoshi ba?”
Gyaɗa mishi kai ta yi sai ya aje cokali ya kwantar da kanta a ƙirjinsa ya ce “Na hutar da ke ciyar da ni yanzu dan na lura sai mu kwashe lokaci ba ki ba ni na ci na ƙoshi ba, ga shi kuma Taufik yana kirana a waya wai yaushe zan zo gidansa madam ɗinsa ta takura sai na kai mata ke.”
Ɗago da daradaran fararen idanuwanta ta yi ta kalle shi, yadda yake tauna abinci sai tsji ya birge ta ta kai hannu ta shafa sajansa mai ƙara mishi kyau da kwarjini ta ce “Amour.”
Aje cokalin ya yi ya sunkuyo gabaɗaya ya ji abincin ya fita kanshi saboda yadda take shafe shi ga shi kuma tana kan cinyarsa sai mutsu-mutsu take taƙi zama ɗam, haɗiye abincin ya yi ya ce “My wife karki sa mu fasa tafiyar nan fa.”
Ƙara shigewa jikinsa ta yi ita kanta ji take kamar su dauwama a haka, gabaɗaya ta ji sam ba ta son barin jikinsa sai ma ci gaba ta yi da taɓa shi dole ya bar cin abincin gabaɗaya ya miƙe tsaye tana maƙale a jikinsa, baki ya buɗe zai yi magana ya ji shashshekar kukan ta ya ciro ta daga jikinsa a ruɗe ya ce “Me ya faru? Wani abu kike so?” Ya jero mata tambaya biyu a jere.
“Nima ban sani ba Amour.” Ta ba shi amsa tana komawa jikinsa.
Ɗaki suka koma ya cire mata kayan tafiyar ya kwantar da ita yana rarrashin ta, kasa jurewa ya yi da jin laushin fatarta ya rufe su da banket.
Sai ƙarfe 12:am suka sake yin wanka yana ta tsokanar ta in ta gaji ta sa mishi kuka ya rarrashe ta da kyale ya ci gaba. Suna fitowa tuni an fito da motar da za su shiga, baya aka buɗe musu suka shiga sai gidan Taufik.
Suna zuwa suka samu Taufik da matarsa da yaransa biyu a harabar gidan suna jiran zuwan su, da kanta ta iso ta buɗe set ɗin Andizo fuska ɗauke da murmushi ta ce “Oyoyo madam J.” Ta faɗa tana son ganin ta.
Andizo har za ta fito sai ta tuna maganar Sultana da sabuwan da ta koya mata yadda za ta ke tafiya da magana irin na masu class, musamman ita da take matar shahararren dan kwallo dole ta kame ta nuna ita babbar mace ce mai aji. Sai da Sultan ya zagayo yana faɗin “Matsa daga nan in ɗauko abata dan na ga ba mu kuka zo tarba ba.”
Riƙe baki matar Taufiƙ ta yi tana nuna zallar mamaki ta ce “Kai bro yau kuma ni kake yi wa haka?”
Bai kula ta ba ya kamo hannun Andizo ya fito da ita ta saki fuska ta sa hannunta a cikin na Sultan ta dubi matar, mara ce tana yanayi da Sultan kuma ba lefi tana da kyau, sai dai ba ta kai Sultan dinta ba.
Dariya ta yi ta ce “Matar bro zo mu je karki tsaya sai man ƙwabrinki ya ƙame, waɗannan in suka haɗu sai a hankali.” Ta faɗa tana kama hannunta suka ci gaba.
Sultan ya gyara tsayuwar shi yana bin Andizo da kallo yadda take tafiyar a yangance abin ya tafi da imaninsa, sai da suka shige sannan ya janye idanuwanta daga wajen ya kalli Taufiƙ tare da miƙa mishi hannu suka yi musabaha.
Dukan wasa Taufiƙ ya kai wa Sultan ya ce “Angon Dije uwar masu gari ba gaba da gaba ba.”
Dariya Sultan ya yi yana shafa ƙirji ya ce “Faɗi ka ƙara nine nan.”
Dariya suka yi a tare suna tafawa sannan suka shiga ciki..
A palo suka same su zaune suna magana kamar dama can sun san juna, Sultan ya riƙe ƙugu ya ce “Limart kar fa ki koyawa matata rashin mutumci irin naki, na ga sai wani magana kuke ƙasa-ƙasa.”
Kallon mijinta ta yi ta miƙe tsaye ta ce “Ka ga bro ba ruwan ka ku tafi in da za ku je ka bar mini ita a nan, kuma ni wani rashin mutumci ne nake da shi da har zan koya wa wani? Khadija zo mu je ciki mu bar su a nan tun da abin sa'ido ne.”
Sai da ta fakaici idon Limart da Taufiƙ ta yi wa Sultan gwalo, kanshi ya nuna ya mata alamar da shi take? Ta gyaɗa kai ta juya suka wuce.
Duk abin da suke a kan idanun su Taufiƙ gudun Sultan ya ce musu magulmata suka yi kamar ba su gani ba..
Ganin tafiyar da Andizo take kamar ba daidai ba ce Limart ta shiga toilet ta haɗa ruwan ɗumi, wardrobe ta buɗe ta ɗauko wata baƙar leda ta wuce Andizo dai na zaune a bakin gado tana jin yadda zazzaɓi ke nuƙurƙur ta, gabaɗaya ta gaji musamm da safe wanda ita ta janyo wa kanta. Tana fitowa hannunta ta kama suka shige toilet ta nuna mata ruwan tana murmushi ta ce “Ki shiga ki gasa jikinki za ki ji daɗi sosai ganyan magarya ne da bagaruwa za su taimakawa miki sosai, bari zan kawo miki towel.”
To ta ce ita kuma ta fita ta kawo mata sabon towel a ledarsa ita da kanta ta buɗe, fita ta yi ita kuma ta cire kayan jikinta ta shiga cikin ruwan ta zauna. Sosai ta ji daɗin jikinta sai da ta ji ya yi fara yin sanyi ta fita ta ɗarwaye jikinta ta sa towel ɗin ta fito kanta a ƙasa. Kaya ta gani a kan gadon ta gane ita aka ajewa ta ɗauka ta sa, tana zama Limart ta dawo hannunta ɗauke da wani cup mai ɗan girma ta ciko shi taf da kunu, miƙa mata tashi ta ce “Kin shanye shi tas karki bar saura.”
To ta ce duk da ba yunwa take ji ba amma ta ji tana son shan kunun, kurɓa ta yi ta ji wani mugun daɗi har tsakar kanta ai ba ta san lokacin da ta shanye ba sai jita yi babu komai a cup ɗin.
Sai bayan sallar Isha'i su Sultan suka dawo gidan, da za su tafi Limart ta sa Andizo a ɗaki ta dinga koya mata yadda za ta janyo hankalin mijinta cikin ruwan sanyi, ta haɗa mata turaruka da na gida da na jiki da kuma na wanka har da ganyan magaryar duk ta haɗa ta zuba mata a leda, godiya sosai Andizo ta yi mata suka fito.
Suna haɗa ido da Sultan ta sakar murmushi mai kwantar da zuciya, domin Limart ta ce ta fara gwada abin da ta koya mata daga yanzu ita kuma ta sa a ranta komai sai ta aiwatar.
Sai da suka zo tafiya Limart ta ce “Bro a ba wa madam izini ta ba ni number wayarta.”
Dafe kai ya yi ya ce “Oh my god! Ba ta da waya amma gobe idan mun dawo daga hospital za mu biya na sayo mana har ni, idan kuma kina son magana da ni ki amshi special number na sai ku yi magana.”
To ta ce ta ɗaga musu hannu direba ya ja suka tafi.