Sashe 37
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“A'a Mama, ki tafi kar na tsayar da ke idan ta yi bacci ko ta ƙoshi zan kaita da kaina.”
“To shi kenan na wuce dama aiki nake duk ya buwaye mu da kuka na ce bari na kawo shi wajen uwarsa mu huta.” Ta faɗa tana dariya ta yi gaba.
Itama Andizo dariyar ta yi tana cewa ai ta yi ƙoƙari ma.
Duk kallon ta suka yi cike da mamaki, dan su yara biyu aka ce musu ta haifa mace da namiji, sai ga shi sun ga wani jaririn an kawo mata. Salame ta nisa ta ce “Hmm wai dama Andizo yara uku haifa? Mu fa biyu aka ce kin haifa ba uku ba.”
Murmushi ta yi tana kallon yarinyar ta shafa kanta, sosai take jin son babyn har ƙasan zuciyarta ji take kamar ita ta haife ta, kallon Salame te yi ta ce “Ke dai kin cika magana Salame to ɗiyar Adda Aminatou ce abokiyar zamana, uwar ba ta da ruwan nono ni ke shayar da su. Wallahi ni tausayi Adda take ba ni kullum sai ta yi ta kuka, sun je asibiti sun nemi na gargajiya a kwanakin nan amma shuru har yanzu ba ta iya shayar da ita.”
Fuskar tausayi duk suka yi suna yi wa Aminatou addu'ar samun lafiya tana amsawa da amin. Sai da ta yi bacci sannan ta janye ta daga shayarwar ta saɓa ta a kafaɗa ta ce “Zo mu tafi Hajaru ki raka ni.”
Tashi ta yi Salame ta ba za a barta a baya ba suka tafi Inna ta girgiza kai tana kallon su.
Suna isa suka samu Aminatou tana zaune ta yi tagumi, a hankali Andizo ta zauna a kusa da ita ta sauke baby ta rungume ta ce “Adda ki daina zurfafa tunani dayawa karki jayo wa kanki wani ciwon kuma, ke fa kike mini faɗan yin tunanin mai zurfi sai kuma na ganki yau kina yi, ga takwara ta yi bacci a samu a kwantar ta ita..”
Abida da ta iso hannunta riƙe da cup da magani ta ce “Faɗa mata dai Khadija ƙila ke da yake tana ganin girman ki ta ɗauki maganarki da muhimmanci.”
Sauke tagumin ta yi ta amshi maganin ta sha ta yi baya ta lumshe ido ta ce “Ku yi haƙuri Wallahi na kasa daina tunanin ne, ko na ce zan, kasa da na zauna ni kaɗai musamman a nan palon gani nake kamar zan ji Salim ya yi sallama ya kira suna na.” Ta faɗa tana goge hawaye.
Dafa ta Andizo ta yi ta ce “Haka ne, dama ai ba zai yiyu a ce ka cire wanda kake so a zuciyarka a lokaci ɗaya ba dole sai a hankali za ka rage tunanin shi, amma dai ki rage karki kamu da wani ciwon..”
“Zan rage Khadija in sha Allah, ni yanzu damuwa jaririyar nan da shayar da ita Allah bai ba ni iko ba, ga shi ke an dora miki nauyi a barki ma da yara biyu su kansu kina ƙoƙarin shayar da su ballantana kuma a ƙara miki da wata ɗiyar, Wallahi ina matuƙar ganin girman ki Khadija ban san da me zan saka miki ba da wannan hidimar da kike wa jaririyata, Allah barmu tare..”
Murmushi Andizo ta yi ta ce “Karki damu Adda ai nima ɗiyata ce zan mata duk abin da zan yi wa yaran da na haifa, ko kin manta mun yi masa alkawarin cewa za mu tarbiyantar mishi da yaransa tamkar uwa ɗaya uba ɗaya?”
“Ban manta ba kuma ke ce kika fara cika wannan alƙawari, Allah ya ba mu ikon cika mishi duk alƙawarin da muka ɗauka..”
Amin suka faɗa ta ba ta ɗiyar ta tashi har za su tafi Abida ta kira Andizo ta dawo ta zauna tana kallon su.
Saukowa ƙasa Abida ta yi ta kalli Andizo ta ce “Don Allah ku yafe mini ke da Anty abin da na aikata muku a baya, Wallahi sharrin zuciya ne da na sheɗan.”
Dariya Andizo ta yi ta ce “Haba Abida ai ni tuni na riga da na yafe miki ya wuce.”
Godiya ta mata sannan suka tafi..
Washegari gida ya cika, da 'yan'uwa da abokan arziƙe aka yi hidimar suna lafiya, da Yamma aka yi taron walima a harabar gidan. Ahmad shi ya yi anko iri ɗaya da su Andizo ya amshi namijin su kuma kowacce ta ɗauki ɗaya suka fito ya rako su har wajen zama.
Tun daga naisa Mamma ta kafe su da ido hawaye na bin kincinta, Salim kawai take gani a tare da matansa suna tunkaro ta.
Taro ya tashi lafiya waɗanda za su tafi gida suka tafi, masu kwana kuma suka tsaya.
Washegari 'yan ƙauye suka shirya aka gama musu sha tara ta arziƙi suka tafi gida aka bar Inna dan take kula da Andizo..
Sosai aka kula da Andizo duk wani nau'in abinci da gina jiki sai an yi mata shi daga na gargajiya har na zamani, hakan kuma ya sa ta yi haske ta murje har wata ƙiba ta yi kamar ba ita take shayar da yara uku ba. Sai da suka gama arba'in sannan aka shirya zama har lokacin Farrah tana nan dan ta ce ba ta shirya zuwa gida ba, har Mom ta kira ta ta ce an kusa gama hutu ta dawo ta su je kasuwa ta yi sayayyar komawa ta ce ita sam ba yanzu ba sai ya rage saura kwana biyu a koma za ta diro Nigeria, ba yadda Mom ta iya dole ta rabu da ita, shaƙuwar su da Andizo har mamaki yake ba ta.
Da misalin karfe 10:am na safiya duk aka taru a palo, suna nan zaune Abba da Abie suka shigo tare da Limamin unguwar. Bayan sun gaisa Abie ya buɗe taro da addu'a sannan ya fara magana.
“Allah gafarta malam dama mun kira ka ne ka yi mana bayani game da rabon gadon dukiyar da marigayi Salim ya bari, sannan ya matsayin takabarsu yake ko na ce idda?”
Gyara zama Liman ya yi ya ce “Iddar mace mai ciki ta na zuwa karshe ne da sauke abin da yake cikinta kawai, shin rabuwar saboda rasuwa ne ko saboda wanin haka ne, Allah mai girma yana cewa: (Mata masu ciki wa’adin iddarsu shine su haifi abin da yake cikin mahaifarsu) [Aldalaq:4] wannan ayar ta kunshi hukuncin macen da mijinta ya rasu ko wanin haka. Allah madaukakin Sarki ne mafi sani.
Sannan kamar yadda kuka sani shi rabon gado idan har mamaci yana da yara maza da mata to fa kason namiji linka na mace, idan an ba wa mace kaso biyu a gado to namiji yana da kaso huɗu ne, idan kuma an ba wa mace kaso ɗaya namiji kuma yana da kaso biyu, dan haka sai ki haɗa duniyar waje ɗaya daga kan fili kuɗi gida da duk wani abu da kuka san nashi ne, sannan in ana bin marigayi bashi ku diba a cikin dukiyar da ya bari ku biya mishi bashin sannan a raba gado..”
“Ma sha Allah mun fahimta yanzu kenan su matansa za su iya yin aure sun gama takaba?” Cewar Abie.
“Haka ne Alhaji ko yanzu miji ya fito za su iya yin aure.”
Tashi Ahmad ya yi ya ɗauko wata baƙar jaka ya buɗe, takardu ya fiddo ya aje a gaban su ya ce “Wannan takardun sun ƙunshi duk wasu kadarori na Yaya Salim, har bashin da yake bin mutane ya rubuta kuma da sa hannun wanda ya ci bashin da nashi sa hannun, yana da filaye guda huɗu da manyan shaguna uku a grand marché, da kudinsa da suke banki wanda zuwa yanzu ban san ko nawa ba ne sai dai a yi tattaki muje banki a duba tun da na san code ɗinsa.”
“To shi kenan yanzu abin da za a yi ku gama sanin adadin kuɗin in ya so gobe ko jibi sai a raba gadon kowa a ba shi haƙƙinsa.”
Da to suka amsa sannan liman ya tashi ya musu sallama zai tafi Abdoul ya dakatar da shi, juyowa ya yi ya dawo ya zauna ya dubi Abdoul ya ce “Abdoul shin ko kana da bin cewa ne?”
“Kwarai kuwa Allah gafarta Malam, lokacin da Salim ya kusa rasuwa ya yi wani rubutu ya ba ni ya ce na ba wa Ahmad, ya kuma yi guda biyu ya ce na bai wa matansa kowacce ɗaya. To ganin yadda suka shiga yanayin baƙin ciki da tashin hankali shi ya sa ba wanda na yi wa maganar saƙon, sai jiya da na kwanta na yi mafarkin Salim ya zo mini fuska ɗauke da damuwa yana sanar da ni cewa “Ya kai aminina kuma ɗan'uwana shin me ya sa ba ka isar da saƙon da na ba ka ba?”
Na firgita sosai na tashi a daren na ɗauko takardun na aje su a kusa da ni na ce yau da na fito zan kawo su dan na cika alƙawari.” Ya faɗa yana fito da takardar ya miƙa wa kowacce tata.
Dafe kai Ahmad ya yi ya ce “Ni kaina lokacin bai fi saura minti goma ya mutu ba ya ce na zo wajen ka na karɓi saƙo, to gabaɗaya na manta kwata-kwata..”
Hajiya Babba ta ce “To kowa ya karanta ya faɗa mana abin da takardar ta kunsa.”
Kowa buɗewa ya yi ya karanta duk suka ɗago a firgice suna kallon su, Mamma ta ce “Me aka rubuta Ahmad?”
Miƙa mata takardar ya yi bai iya ce mata komai ba. Amsa ta yi ta soma karantawa a hankali.
_“Ɗan'uwana wannan rubutun da nake maka Ian cikin tsananin ciwo tsakanin mutuwa da rayuwa, don Allah Ahmad ka kula da yaran da za a haifa mini, ka ba su tarbiya mai kyau ka musu duk abin da suke so matsawar bai saɓa wa addini da shari'a ba, sannan ina mai roƙon ka wata alfarma Ahmad idan su Khadija sun gama idda ka aure su gabaɗaya saboda ka kula da su dan ba na son su bar gidanmu ka ji ɗan'uwana.”_
Ɗago kai Mamma ta yi ta kalli su Andizo, hannu ta miƙa musu ta ce “Ku kawo taku na gani.”
Miƙa mata suka yi ta amsa itama ta soma karanta ta Andizo.