Sashe 7
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A bakin mota ya same su suna jiran fitowar shi, Ahmad ya yi murmushi ya ce “Angon Andizo ba gaba da gaba ba ko da ta baya sai dai mutum ya zo da zamba dan Gyatumarsa, kai ka ji wani kalar ƙamshi da kake na musamman kamar an tsamo ka daga inda ake sarrafa turare? Dama nasan wannan wankan sai amarya ita kaɗai za ta kalla ta yaba a ji daɗi.” Ya ƙarashe maganar yana kallon ƙofar part ɗin Salim ganin Aminatou na tsaye tana kallon su, murmushi ya saki yana mata kallon ko da magana ne?
Kwafa ta yi tana aiko masa da saƙon harara ta yi baya ta koma ciki zuciyarta kamar ta buga, ta rasa yadda za ta yi da Ahmad a gidan nan, shi ba shi da buri illa ya baƙanta mata zuciya kawai dan ba ya sonta da yayansa. A fusace ta fito ta shiga mota ba wanda ankare da ita sai ƙaran tashin motar suka ji duk suka juya suna kallon ta har ta fita..
Murmushi Ahmad ya yi ya kalli Salim ya ce “Yaya ina kuma matarka za ta tafi da safiyar nan? Kuma na ga kamar ranta a ɓace yake.”
Girgiza kai Salim ya yi ya ce “E ta ce gidansu za ta je ta wuni tun da ba na gida yau, amma ba ta ce yanzu za ta fita ba sai wajen goma muka yi da ita, ina ga ko dai 'yan'uwanta sun fara zuwa ne aka soma kiran ta shi ya sa ta fita, ku shiga mu tafi ko ma meye in na dawo zan ji daga bakinta.” Ya faɗa yana shiga mazaunin direba..
Dariya Abdoul ya yi ya kamo shi ya fito da shi yana faɗin “A'a rufa mana asiri angon Nana Khadija kar ka je ta ce kana warin man mota kasan hali dai tsaf za ta faɗi..”
Dariya shima ya yi yana hasko yadda za ta tare shi da murnar ta ta kira shi da mai hankali shirin Allah, babu abin da ya fi birge shi game da ita musamman irin yadda take yabon shi, lumshe idanu ya yi lokacin da ya ji sun fita daga gidan yana jin wani matsanancin fari ciki ba ƙara mamaye zuciyarsa.
Maganganunsu na baya yake tunawa, ya yi missing rashin kunyar ta da ɗan ƙaramin bakinta wanda a kullum yake shan baƙin kwalli da mai ya yi ta maiƙo, idanuwanta farare tas masu narkar da zuciyarsa yana son ya yi ta kallon su tana masa fari da su musamman in tana sanar da shi lefin Ahmad, da yadda take riƙe ƙugu in za ta yi masa rashin kunya. Ajiyar zuciya ya sauke Abdoul ya taɓa shi yana dariya ya ce “Angon Dije wai duk tunanin ta ne ya hana ka cewa komai?”
'Yar dariya ya yi yana shafa ƙirjinsa irin farin ciki ya masa over ɗin nan ya ce “Ai Khadija ta musamman ce a zuciyata Abdoul, ba za ku gane hakan ba ko na faɗa saboda kun ganta ƙarama, ni kuma duk duniya ban ga wadda ta kai ta kwarjini da samun matsayi a zuciyata ba, ni kaina mamakin kaina nake yadda soyayyar ta take hana ni sukoni har na kasa gane komai lokacin da ta ɓata. Iya gaskiya ta nake faɗa muku ina son Khadija son da ban taɓa yi wa wata 'ya mace ba.”
Dariya Ahmad ya yi ya ce “Gaskiya ka zauce a kan ɗalibar nan tawa, ya kamata kake gyara kalaman ka kar wata rana ka faɗa a gaban Aminatou ka haɗa fitina a gidanka nan gaba.” Ya faɗa yana kuma yin dariya saboda ya ji daɗin maganar.
“Allah ya kiyaye, ai in sha Allah ba zan taɓa faɗa a gaban Aminatou ba, ko mutuwa ai tana tsoron ido ballantana Aminatou da ta nuna mini so da ƙauna, duk da dai ba ni naje na ce ina son ta ba ita ta kawo kanta ta ji matuƙar daɗi ranar da ta tare ni ta ce mini tana so na kuma so na aure, to don Allah me ya fi wannan daɗi a ɗaga baki a ce ana sonka?” Cewar Salim.
“Gaskiya babu abokina, duk wanda zai ce yana sonka ai ba abin yadawa ba ne ka riƙe shi hannu bibbiyu.” Abdoul ya faɗa yana kallon hanya.
Jinjina kai Ahmad ya yi yana wani yatsine fuskar dan shi gani yake ba tsari mace ta tunkari namiji ta ce tana son shi su yi aure, ya fi ganewa namiji ya je ga mace ya fara furta mata kalmar soyayya ya nemi su yi aure. Gyara zama ya yi ya ce “Ni kuwa a tsarina na fi gane dai namiji ya ce yana son mace.”.
Tsaki Abdoul ya yi ya ce “Kai dama wa yake sa taka da ba ka da alƙibila, to Nana Khadija matar Manzon Allah (S. A. W) ita ta ce tana son shi, hamshakiyar ƴar kasuwa ce mai arziki amma da ta ji tana son ɗan gatan Allah ta ce a faɗa masa tana son shi, a lokacin ta girme shi nesa ba kusa a shekaru, shi yana matashi ɗan shekara 25 kuma ya aure ta. To meye aibu a ciki dan mace ta ce tana son ka? Ba haramun ba ne.”
“Haka ne, amma ka sani 'yan matan yanzu sai sun samu mai kuɗi su dinga bibiyar shi suna cewa son shi suke, wasu fa ba son tsakani da Allah suke yi ba soyayyar ta dan yana da kuɗi ce.” Ya faɗa yana hura hanci kamar an masa lefi..
“Haka ne Ahmad, amma dai ai duk lalacewa ba za a rasa ta gari ba, kuma nasan Aminatou na ɗaya daga cikin mataye na gari waɗanda suke son mutum da zuciya ɗaya, in da dan kuɗi ta so Salim da tuni ya gano hakan ai.”
Bai sake ba cewa komai ya soma danna wayarsa, jin ya yi shuru suma duk suka rabu da shi dan sun san shegen taurin kai irin na Ahmad a kan ra'ayinsa...
Girki Maigari ya sa a yi na tarbar su Salim, Andizo sai murna take yau za ta ga mai hankali ta ba shi labarin abubuwan da ta gani. Ruwa ta ɗumama ta shiga wanka ta dirje jikinta tas da soso da sabulun da Mom ta sako mata a cikin kaya. Sabulun yana da ƙamshi sosai har lumshe idanu take tana shaƙa, buɗe ido ta yi ta tuna irin wannan ƙamshin sabulun ai a jikin Sultan ta ji shi, tsaki ta yi ta ci gaba da wanka tana cewa “Yo to ni ina ruwana ma ba Mom ta ba ni ba?”
Tana fitowa ta shige ɗaki inda Hajaru ke jiran ta, suna ganin juna suka fasa ihun murna suka rungume juna cike da farin ciki, Andizo ta ce “Jiya na zo nake ta neman ki aka ce kun tafi biki.”
Kallon ta Hajaru ke yi tana shafa jikinta ta ce “Ƙawata kin ga kuwa yadda jikinki ya yi kyau? Kai amma dai waɗanda suka sace ki abincin 'yan gayu suke ba ki?”
Dariya Andizo ta yi ta shige lungun tsakanin gado da kayansu ta saka riga da siket ɗaya daga cikin kayan da Mom ta zubo mata, fitowa ta yi ta ce “Na yi kyau kuwa?”
“Kai Alƙur'an ƙawata kin zama ƴar birni.” Hajaru ta faɗa tana taɓa kayan.
Ledar ta janyo ta buɗe ta ce “To kema zaɓi guda ki saka ki raka ni in su mai hankali sun zo.”
Ba muso ta ɗauki wata doguwar rigar abaya da mayafinta, sakawa ta yi ta ɗaura ɗankwali Andizo ta yi dariya ta ce “Alƙur'an kin ba da kala Hajaru.”
Murmushi ta yi tana shafa kayan ta ce “Na gode ƙawata..
Su Salim na isowa ƙauyen aka kai su masauki, sai kallon ƙofa yake dan ya ƙagara ya ganta su Abdoul sai tsokanar shi suke yi. Giɗaɗo da Umar suka kawo musu abinci da ruwa da duk wani abin buƙata, amma Salim ya kasa cin komai dan shi ba ta abinci yake ba.
Tun kafin su iso yake jin maganar Hajaru can kasa-kasa, murmushi ya yi yana gyara zama.
Andizo na baya ta ɓoye a bayan Hajaru ta rufe fuska wai irin zuwan bazata za ta yi wa mai hankali sai cewa take “Ɓoye ni Hajaru.”
Suna zuwa ƙofar ɗakin Andizo ta fito ta yi tsallen murna ta ce “Mai hankali shirin Allah.” Ta faɗa tana ruguwa a guje ya miƙe ya taro ta ya yi sama da ita yana juyi a tsakar ɗakin suna dariya.
Gabaɗaya baki suka saki sunan kallon su, shi kuwa Ahmad waya ya ciwo yana musu video. Sai da suka ya gaji da kanshi ya sauke ta ƙasa ya ja ta suka zauna, ta matso kusa da shi tana faɗin “Ka rame.”
Hannu ya miƙa mata jikinsa a sanyaye, miƙa masa ta yi ya kama da wani irin sauri ya rungume tsam a jikinsa yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, dariya duk suka yi Ahmad ya miƙe tsaye ya ce “Abdoul ka ga tashi mu fita mu koma dakina waɗannan dai an gamu.”
Tashi Abdoul ya yi suka fita har Hajaru itama tana dariya ta koma ciki..