Sashe 24
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Washegari sun tashi ya taya ta ta shirya suka shiga part ɗin Aminatou itama lokacin ta tashi tana karyawa suka same ta, ruwan tea mai zafi ta haɗa wa Andizo ta ce “Amshi maza ki sha nasan ba ku kai ga karyawa ba ma..”
Turo baki ta yi ta ce “To Adda wannan uban shayin duk ni kaɗai zan shanye?”
“Sosai ma in ba ki sha ba kuma na ce Salim kar ya kaiki makaranta.”
Jin abin da ta faɗa sai ta yi saurin amsa ta soma sha, Salim ya yi mata jinjina da hannu ta yi murmushi ta shige kitchen. Ba ra fi minti shida ba ta fito da soyayyan kwai a plate ta aje musu ta zauna itama, shima Salim shayi ya haɗa ya sha suka gama karyawa sannan suka tashi. Kallon Aminatou ya yi ya ce “Wannan ita ce mace tagari matata Aminatou kenan, Allah ya miki albarka.”
Daɗi ne ya rufe ta ta ce “Amin mijina gara ku yi sauri ita Khadija har ma ta fita waje..”
To ya ce mata ya fita tana ɗaga mishi hannu.
A mota ya same ta tana jiran shi, ganin ta canja ya ce “Lafiya dai na ga kin ɓata rai?”
“To ni sai yaushe za ka saya mini salula ne? Kai fa ka ce da na fara karatu za ka saya mini, ga shi ina so na kira ƙawata Farrah mun jima ba mu gaisa ba nasan za ta yi ta kira wayar Maigari a ce mata ban zo ba..”
Dariya ya yi yana gyara zaman hularsa ya ce “Nana Khadija tawa ni kaɗai, ai yau nake cewa zan saya miki waya sabuwa dal a kwali..”
Murmushi ta yi ba ta kuma cewa komai ba suka bar gidan.
Yana aje ta sai ga Amira suka shiga ciki a tare, Amira ta ce “Ka ga matar soja.”
Dariya Andizo ta yi tana rufe fuska, suna zama sai ga wani daga cikin ɗalibai ya iso gaban table ɗin su yana wani shafa kai, kallon shi Amira ta yi ta kawar da kai tana jan tsaki. Gyara tsayuwa ya yi ya ce “Yane Amira da dama? Wannan haɗaɗɗiyar yarinyar fa ƙanwarki ce?”
A fusace ta juyo ta ce “Kai ka kama kanka wannan ba tsarar ka ba ce matar aure ce, idan kuma kana son kwana a hannun sojoji to ka ci gaba da abin da kake ka gani..”
Dariya ya yi ya kalli Andizo ya ce “ 'Yan mata karki wani damu so ne take ta kashe miki kasuwa, saboda ni ba na son gajeruwar mace sai doguwa kamar ke..”
Idan table ɗin da suke zaune ya tanka masa to Andizo ta ba shi amsa, haka ya gama surutan shi ya koma ya zauna ganin malam ya tafo cikin ajinsu..
Bayan kwana biyu Salim ya kawo mata waya da layi da komai ya buɗe mata, ranar tun da ta dawo daga makaranta ta tsare shi ya dinga kowa mata abubuwan da ba ta gane ba har dare sannan ta rabu da shi ya bar part ɗin saboda ranar kwana Aminatou ne.
Washegari ta buɗe wata ƙaramar jaka ta fito da 'yar ƙaramar takarda, numéro ɗin Mom ta sa ta kira ta aka ɗauka.
Da murna Andizo ta ce “Hello Mom ina wuni ya gida ya iyali? Don Allah ki ba ni ƙawata mu gaisa..”
Mom ta riƙe baki tama faɗin “A a, wa nake ji kamar amarya? Kina nan ma Khadija? Farrah har ta gaji da kukan a nemo mata ke..”
Fuskar tausayi ta yi ta ce “Ayya Allah sarki ƙawata alƙur'an na yi kewar ta sosai, kinga fa sai jiya ya saya mini waya shi ne na sa lambar na kira..”
“Ai kuwa dai kin kyauta ga ta nan ma ta shigo bari na ba ta.”
Miƙa wa Farrah wayar ta yi ta ce Khadija ce da sauri ta amsa tana dariya ta fita a ɗakin.
“Hello Khadija ya kike ya angonki? na yi kewar ki sosai.”
Dariya ta yi suka dinga hira ana labaran abin da ya faru tun bayan rabuwar su, sai da suka yi awa uku cif suna hira shima ba dan sun gaji ba katin Andizo ne ya ƙare kiran ya yanke, sake kira ta yi ta ji ba ta shiga sai ta aje tana jiran Salim ya zo.
Yana zuwa ta miƙa masa wayar ta ce “Wannan wayar ba sabuwa ba ce ji fa daga kiran Farrah muna magana kawai ta fita, na sake kira kuma ba ta ƙara ta lalace ka kai a canja mini wata..”
Kallon wayar ya yi sai kuma ya amsa ya shiga layin da ta kira ya ga adadin lokacin da suka ɗauka suna waya, dariya ya yi ya ce “Kai kai kai! Ai kuwa sai kin kawo kuɗi za a gyara miki ita tun da ke kika ɓata..”
Dafe ƙirji ta yi ta ce “Waiyo yanzu kenan kana nufin ba zan sake yin magana da Farrah ba? A to bari na duba kamar dai ina da kuɗi da Hajja ta ba ni da zan tafo.” Ta faɗa tana wucewa ɗaki ya bi bayan ta da kallo yana lumshe idanu.
Dala dari ta kawo mishi ta ce “To a kai a gyara mini ina so gobe na kira ta akwai labarin da ban faɗa mata na makaranta, itama ta ce za ta faɗa mini wani abu sai aka hana ta magana..” Ta faɗa tana zama..
Amsar kuɗin ya yi ya ɗauki wayarsa ya turo mata katin dala ɗari, ya ce mata kar ta taɓa wayar ta bari sai gobe har whatsapp zai buɗe mata w kafin safe wayar za ta gyaru da kanta, murna ta dinga yi tana mishi godiya ta tafi kitchen ta dafo masa indomie da ruwa-ruwa ta kawo mishi. Kallon ta ya yi yana murmushi ya ce “Sannu da ƙoƙari Allah ya miki albarka.”
Amin ta ce ta ɗauke wayar ta kai ta can cikin kayan sawar ta ta duba tsakiyar kayan ta totsa ta tana jiran gobe ta yi ta fiddo ta, a cewar ta in wayar ba a ganin ta za ta fi gyaruwa da wuri....
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/4, 11:35 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
28
Can cikin dare ta farka ta tashi tana kallon lokaci, ƙarfe 3:am daidai na dare ta riƙe kai ta ce “Oh ni Dije, alƙur'an na ɗauka gari ya waye ashe tsakiyar dare ne.” Tashi ta yi zaune tana kallon waje ɗaya, kallon fegen ta ta yi ta kai hannu ta shafa inda yake kwanciya, hawaye ne suka cika mata ido sam ba ta son ya yi naisa da ita, ko bacci ne in ba a jikinsa ba ta ji ta duk ji take kamar a waje ta kwanta. Dogon numfashi ta ja tana goge hawayen da suka samu damar zubowa, sauka ta yi a gadon ta nufi banɗaki ta ɗauro alwala ta fito duk sai ta ji ɗakin ba ya mata daɗin zama, kabbara ta tayar ta gabatar da nafila raka'a shida sannan ta zauna, addu'a sosai ta yi wa iyayenta tana yi tana kuka har cikin sujjada sai da ta musu addu'a, tun da ya sanar da ita iyayenta sun rasu sai ta zama wata kala, lokaci zuwa lokaci sai ta yi shuru tana tunanin itama da yanzu da mamanta watarana da sai ta kawo mata ziyara dan ta ga lafiyarta irin na Ummin Aminatou. Jikin gado ta jingina tana jan carbi har bacci ya yi gaba da ita..
Ɗakin ya shigo sanye da farar jallabiya bakinsa ɗauke da sallama, tsayawa ya yi yana kallon ta ya saki murmushi, wani matsayi take ƙara samu a can cikin lambu zuciyarsa saboda yadda take ruƙo da ibada, duk rashin jin ta da shirman magana da lokacin sallah ya yi za ta bar komai ta je ta gabatar. Tsugunnawa ya yi a gaban ta ya kai hannu ya shafo fuskarta yana faɗin “Ma femme tashi ki yi Sallah an kira sai ki koma baccin.”
A hankali ta buɗe idanuwanta tar a kanshi, murmushi ta sakar masa ta miƙa hannu ta matso fuskarsa ta sumbace shi a goshi sannan ta ce “Barka da asuba mai hankali shirin Allah mijin Dijan Hamma.”
Dariya ya yi ya ce “Yau kuma da salon gaisuwar da aka zo? Gaskiya kina ƙara shiga raina ma femme, Allah ya bar mu har gidan aljanna maɗaukakiya, tashi ki yi Sallah ni zan wuce masallaci kin san yau ba a école Samedi ce, to daga yau za ki fara zuwa Islamiyar da na je jiya na samar miki gurbin karatu..”
Waro idanu ta yi ta miƙe tsaye ta ce “Waiyo daɗi ni uwar masu gari, Allah ya saka da alheri Ubangiji ya ƙara maka budi na alkhairi da ƙarfin imani, Allah saka ka a aljanna..”
Cikin jin daɗin addu'ar ya amsa da amin yana miƙewa tsaye, sai da ya ga ta shiga banɗaki sannan ya wuce.