← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 75

Sashe 74

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai kawai take tana bin Limat da kallo, ashe haka yake son ta? Goge hawayen da suka zubo mata ta yi nan take ta ji wani nadama na shigar ta na ƙin tsaya ta saurare shi.
“In sha Allahu ni zan gyara mata zama tun da ta shigo gonar ni uwar masu gari, za ta ɗanyan aikin jikar Hajja yaushe ne ma za su buga wasa?” Ta faɗa tana huci.
Murmushi Limat ta yi ta mata jinjina da hannu ta ce “Yawwa ƙanwata ki zama jaruma, gobe ne za a buga wasan kuma nasan za ta zo domin in sun ci ta rungume shi kamar yadda ta saba a baya, musamman ma yanzu da ta san ba za ta iya ganin shi ba sai ta wannan hanyar.”
Kwafa ta yi ba ta sake cewa komai ba tana ta shawara da zuciyarta me ya kamata ta yi a goben.

Sai yamma suka dawo ya ɗauke ta suka wuce gida, tun a hanya ya ga canji daga gareta sosai ya cika da farin ciki, gira ya dage mata ya ce “My wife me kike son ci na biya na mana takeaway?”
Wani irin kallo ta mishi irin na masoya tare da sakar mishi tsadaddan murmushi ta ce “Amour ni ba na son komai mu je gida zan mana girki mai daɗi da ya fi da waje komai.”
“Allah da gaske my wife.”
Kai ta gyara mishi tana dariya, shi ma ya taya ta.
Daren ranar ya nuna mata shi ɗin masoyinta ne na haƙiƙa, ita kanta ta aminta da son da yake mata babu algus a cikinsa.

Washegari ya shirya ta shima ya shirya suka fito sai filin buga wasa, a mota ya ba ta rigar irin ta jikinsa mai lamba takwas a baya taƙi ta saka, sai da ya lallaɓa ta sannan ta saka ta yi rolin kanta da mayafin abayar jikinta.

Wasa aka fara bugawa bugun farko aka ci su Sultan, ita kuwa tana zaune a gaba tana kallon Jennifer da ke can gefe sai kiran sunan Sultan take kamar yadda sauran jama'a suke kiran shi ganin kwallo ta zo hannunsa, kawar da kika ta yi ta mayar kan su.
Ana ta fafatawa a filin daga har Sultan ya samu saka kwallo a raga har su uku su kuma waɗancan sau huɗu a haka aka tafi hutun rabin lokaci.
Wasu dakuna ta gani ya kama hannunta suka shiga ɗaya daga ciki ya faɗa kan gado buduf, haki ya dinga yi AC ba dukan shi sai jera mishi sannu take tana shafa kansa, ji ta yi ya ba ta tausayi sai gani ta yi ya tashi ya hau kan wani inji ya dinga motsa jiki sai da ya yi sharkaf sannan ya sauko ya zauna duk tana zaune tana kbin shi da na mujiya. Kwankwasa ƙofa aka yi ya ba izinin shigowa, wani kalar juice aka kawo mishi ya amsa ya shanye nan take ya koma ya zauna, fuska a haɗe ta ce “Ina fata dai ba giya ba ce ka sha?”
Miƙewa ya yi tsaye ganin time ɗin komawa saura minti biyu, kiss ya manna mata a goshi ya ce “Ki yarda da mijinki ya zama Ustaz.”
Murmushi ta yi ta miƙe ta rungume shi ya ce “Karki fara my wife muje, idan kuma za ki huta ni zan wuce in kin fito akwai wanda zai kaiki har wajen zaman ki.”
Ce mishi ta yi ita ba yanzu za ta fita ba ya yi gaba ita kuma ta zauna, ya fita kenan ta ji ana buga ƙofa ta tashi ta buɗe. Kafin ma ƙarasa buɗewa ta ji an hankaɗo ta ta yi taga-taga za ta faɗi ta tsaya, kallon su take cike da tsaurin ido ta ɗaga kai ta kalli samar ɗakin ta ga ba cctv sai ta matsa ta shigo.
A wulaƙance take kallon Andizo har ta zauna a kan gado, tsaki ta ja ta ce “Kin yi kuskure Khadija da kika yi sanadin raba alaƙa ta da Mr J.”
Dariya Andizo ta yi ta cire rigar da ya sa mata ta yi tsukiya da mayafin abaya ta ce “Ke zan cewa kin yi kuskure da kika shigo ɗakin nan, dama neman hanyar da za same ki nake sai ga shi kin kawo kanki cikin ruwan sanyi, yau sai na rarrabe miki tsakanin aya da tsakuwa.”
Kanta ta yi ta rufe ta da duka ta ko'ina, duk da Jennifer na ramawa amma ƙarfi wadda ta girma a afirca ba ɗaya ba ne da na wadda ta taso a turai. Sai da ta galabaitar da ita sannan ta juya tana neman abin duka, can ta hango cazar Sultan ta isa da gudu ta ɗauko ta dinga tsula mata, sai da ta ga da kyar take numfashi sannan ta daina dukan ta ta ja ta ƙiii ta zaunar ta jingina ta a jikin gadon, kunnenta ta damƙa ta murza da ƙarfi ta saki ƙaran azaba, a fusace ta ce “Za ki ƙara takura wa rayuwarmu?”
Girgiza kai ta dinga yi ta daka mata tsawa ta ce “Idan ba ki faɗa da bakinki sai na kakkarya miki ƙafafu, shegiya mai kama da ƙosai ke har kin isa ki ja da ni? Za ki sake bibiyar mini miji?” Ta sauke mata dundu a gadon bayan.
A wahalce Jennifer ta ce “Am sorry Khadija ba zan sake ba daga yau.”
Rankwashi ta kai mata a ka ta ce “Ki ma ƙara ki gani wannan zan miki gaba sai an kasa gane hatsari kika yi ko faɗowa kika yi daga bene mai hawa talatin, ai susar jiki na miki matuƙar ba ki kama gaban ki kin rabu da rayuwarmu ba, maza tashi je ki wanke fuskarki da hannu, kuma duk wani motsin ki a tafin hannuna yake duk in da za ki shiga akwai masu bibiyar ki.” Da kyar ta tashi za ta bar ɗakin ta kara daka mata tsawa dole ta shiga toilet tana tsaye ta wanke fuska da hannu ta goge da towel suka fito, sai da suka nufo wajen ta riƙe hannunta suka ƙaraso. Sai da ta kai ta har wajen zaman ta ta zaunar da ita a gefen Ruby Sannan ta dawo ta zauna a kusa da Limat.
Kallon ta Limat ta yi ganin yadda take huci, “Khadija ya na ganki ke da Jennifer kuma kina huci?”
Dogon numfashi ta ja ta ce “Zan miki bayani daga baya Anty.” Ta ƙarashe maganar tana murmushi ta mayar da hankalinta ga wasan.
A ranar su Sultan suka cinye kofi mabiyan su suka dinga ihu ana tafi, Andizo sai ta ga turawa na rungume ta ana taya su murna.

Bayan kwana biyu Andizo ta sanar da Limat abin da ta yi wa Jennifer, dariya ta dinga yi tana jinjina rashin tsoron ta ya ce “Lalle Khadija ba ki da tsaro, kuma kin ga ba ta shigar da ƙara ba.”
Dariya itama ta yi ta ce “Ta shigar mana ta ga yadda zan sake zuwa har gidanta na mata ɓalle-ɓalle a mazaunai.”
Dariya suka kuma sa wa suka ci gaba da hira.

A kwana a tashi su Andizo suka yi wata biyar a London suna shiga na shida ta kwanta rashin lafiya a lokacin ne kuma Farrah ta diro ƙasar, sun yi murna da ganin juna Farrah ta zama big girl ga class a daren ne zazzaɓin da ke zubo mata duk dare ya tsananta suka yi asibiti da ita, gwajin farko aka tabbatar musu tana ɗauke da ciki har na wata uku, ranar du kansu ma'aikatan asibitin sun san ɗan da zai fito a cikin Khadija ɗan gata ne, domin Sultan rabon kuɗi ya dinga musu yana ta yin sujjada yana gode wa Allah da ya albarkace shi da damun ƙaruwa, ganin yadda suke murna har tausayi suka mata Farrah har da kuka ta yi itama za ta samu ƙane ko ƙanwa..

Tun daga asibitin ya dinga kiran abokansa yana sanar da su matarsa n da ciki, sun taya shi murna waɗanda ba su samu damar ganin ta ba suka ce ai kuwa za su shirya walima suka sa rana, ita dai Andizo in suna wani abin tagumi take ta dinga kallon su, Farrah zuwa take ta dafa cikin ta dinga yin magana wai tana hira da ɗan'uwa ko 'yar'uwarta.
Ranar da abokansa suka zo kowa gift ya dinga ba ta, wasu kayan baby wasu sarƙa mai tsada wasu warwaro, wasu kuɗi haɗi da flower Mai ƙamshi an naɗe kuɗin a jiki, ranar sai da ta yi kukan kyautar da abokan mijin nata suka mata.
Bayan kwana biyu matayensu suka zo taya murna tun abin na mata mamaki har ta daina ji ta shiga cikin su wasu turawa ne wasu kuma Hausawa irin ta, da za su tafi duk suka amshi number ta aka saka ta a group ɗin manyan mata masu class da aji matan manyan mutane.

Cikin ta na cika wata tara ta haifo ɗanta namiji fari sol mai kama da ubansa sak da yamma aka ba su salama, bayan sun dawo Mom ta ce dole ya tarkata su dawo gida a kula da ita ba dan ya so ba ya cira musu ticket har da Limat suka nufi Nigeria.

Ranar suna an ga ɓarin kuɗi, masu rabo har da wayoyi suka samu gift din uban jego, canjin kaya kuwa sun yi ya fi kala shida shima dan ta ce ita ta gaji da canja kaya ne ya haƙura, yaro dai ya ci sunan Rudwan sunan yayansa wanda Andizo ce ta ce a sa wa jaririn, sosai ya family suka ji daɗin karar da ta musu.

Sai bayan kwana goma da zuwan su ya koma London cike da kewar su, ita kuma Mom ta ci gaba da gyara ta.
Bayan sun gama arba'in ta shirya ta nufi Niger ganin dangi. A Niamey ta fara sauka suka haɗu da Amira da katon cikinta har dare suna hira, sai washegari ta nufi Tilaberi inda dangi da 'yan'uwa suka dinga ɗaukan Rudwan har sai da Maigari ya hana kowa ɗaukan shi.
Chapter 74 · 0% Book details