Sashe 29
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ya dawo bai samu Andizo ba a part ɗin ta sai ya wuce part Aminatou, a palo ya same su Andizo na yi wa Aminatou tausa sai sannu take jera mata, kallon su ya yi ya tsaye yana faɗin “Lafiya dai Khadija?”
“Wallahi tashi ne ta yi za ta shiga banɗaki ta zame za ta faɗi, Allah ya taƙaita ina nan na taro ta shi ne ta ce kafaɗar ta sage na matsa mata.”
Zaro ido ya yi ya matso kusa da ita yana jera mata sannu, a sanyaye ya ce “Don Allah ku dinga bi a hankali wajen tafiya musamman ma banɗaki kunga shi dai kasan shi ba ya rasa digon ruwa, to kuke tafiya a hankali karku ji wa kanku ciwo da Baby's ɗin mu..”
To Andizo ta ce dan ita Aminatou zazzaɓi ne ya rufe ta, tashi ya yi ya ɗauki tarkacan kayan maganin ta ya zo ya ɓallo kowanne ya ba ta ta sha. Da kanshi ya dauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar ya lulluɓa mata bargo sannan ya fito, yana fitowa ya ga ba kowa tuni Andizo ta tafi part ɗin ta.
Dawowa ya yi ɗakin ya buɗe fuskarta ya ce “Bari naje na yi mata sai da safe, sannan gobe zan kaiki gida ki musu kwana biyu..”
Duk da tana jin jiki amma albishir din da ya mata ya sa ta ji kwarin jikinta, murmushi ta mishi da kyar ta iya cewa ta gode ta mayar mata da bargon ya wuce...
Zaune ya same ta tana shafa cream a hannayenta, kallon shi ta yi tana murmushi ta ce “Allah ya taimaki Abban 'yan biyu.”
Dariya ya yi ya zauna a bakin gado ya ce “In sha Allahu sati mai zuwa za mu je garinku, ita kuma Aminatou gobe zan kaita da safe haka wajen ƙarfe takwas.”
Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, daɗi sosai ya rufe ta ta ce “Na gode sosai da ka amince na je na gado su Maigari, Wallahi ina matuƙar kewar su kamar ba gobe, amma zan raka ka mu kaita.”
Tausayi ta ba shi sai yanzu ya gane ashe duk tsayin lokacin nan juriya kawai take tana masa biyayya da ya ce ba za ta je garinsu ba, sai ta kwanta ya ja mata bargo ya tofe ta da addu'oi sosai sannan ya rage mata wutar ɗakin ya ja k'ofar yana ɗaga mata hannu.
Gari na wayewa duk suka shirya Aminatou sai washe baki take tana haɗa kaya a cikin ƴar ƙaramar Jakarta, kala huɗu ta zuba da duk abin da za ta buƙata. Andizo ta shirya itama ta shigo ta ɗaukar mata jakar suka fito a tare, hakan ya yi daidai da fitowar su Mamma su duka har da Hajiya Babba.
Kallon su Hajiya Babba ta yi ta ce “Yanzu don Allah kalle su gwanin birgewa, ai zaman lafiyar kishiyoyi ba ƙaramin kawo ci gaban miji yake ba, da farko Salim har wani baƙi ya soma yi saboda abubuwan da waccan duguwar matar tasa ta tsiro, yanzu da ta gane Allah ɗaya ne ta dawo kan hanya ba ga, shi suna zaman su kamar yaya da ƙanwa ba..”
Murmushi Mamma ta yi tana bin su da kallo, ita kanta suna matuƙar birge ta sosai musamman yadda suke taimakon junansu, Ahmad ma gyaɗa ya yi ya ce “Wato Hajiya Allah ne ya dubi Aminatou da idanun rahama ta gane gaskiyar abin da take ba daidai ba ne, kuma abin da ya birge ni ma da ta rabu da wannan muguwar ƙawarta ta mai yawon dare, duk ita ce ta dinga ɗora ta a hanya marar kyau tana duga ta ta tayar wa da mijinta hankali ta kuma bi kowacce hanya wajen ganin ta zauna ita kaɗai a gidan yaya Salim. Ba su san duk wani motsinsu a tafin hannuna yake ba, har wuraren bokaye da malaman da suke zuwa duk ina sane..”
Shiga motar suka yi ya ɗayar suka bar gidan, sai da suka yi nisa Mamma da ta riƙe baki saboda mamakin abin da Ahmad ya faɗa ta ce “Wai da gaske kake ko wasa Ahmad? Aminatoun ce ta je gidan boka?”
“Kina mamaki da lamarin ku na mata musamman aka ce za a muku kishiya in ba ku aje yaro ba, gani fa suke kamar za a zoa kore su daga gidan ne. Ku ne ba ku san Aminatou a baya irin ta'asar da ta aikata ba dan ma ina yawan nuna mata na fa san komai duk abin da take, to Alhamdu Lillah tun da ta gane gaskiya ta tuba ta koma ga Allah, yanzu ita kanta in ta tuna abubuwan da ta yi a baya sai ta ji ta muzanta..”
Turo baki Hassana ta, yi ta ce “Kai Yaya tonon asiri fa ba kyau, tunda dai ta tuba meye amfanin faɗa mana abin ya wuce? Ai, da ka yi shuru da bakinka kawai..”
Hararar ta ya yi ta madubi ya ce “Wallahi ki fita idona Hassana, saboda ƴar wajen ki ce shi ya sa ba ki son a faɗi abin da ta aikata na cutarwa wa ɗan'uwanki?”
“Ba haka ba ne yaya, na ga dai ai ta tuba sai ka rufe mata sirrin ta wanda ba kowa ya sani ba daga ita sai ƙawarta sai kai sai kuma mahaliccinmu, kai yanzu za ka rasa lefin da kake aikatawa ne nima sai na faɗi ka ji in da daɗi, yanzu da a ce maganar da ake tana ji za ka kashe mata kwarin gwiwa ta dinga yin ɗari-ɗari da shiga part ɗin mu, amma dai ba komai Allah ya yafe mana bakiɗaya.” Ta faɗa tana kawar da kai gefe, saboda ba ta so ya faɗa wa su Hajiya Babba abin da ba su sani ba marar kyau game da Aminatou, sarai halin hajiya babba watarana za ta iya mata gori da maganar kaɗan daga aikin ta ne..
Tsaki ya ja yana cewa babu ruwan ta tun da ba ita ya faɗawa ba, ta ce koma meye ai ta tuba ka manta da maganar kawai, sai da Hajiya Babba ta musu magana sannan suka daina musayar magana.
Mamma ta sauke tagumi ta ce “To Allah ya sa mu dace ya shirya mana zuri'a..”
Amin suka ce daga haka babu wanda ya sake cewa komai..
Su Aminatou na isa gidansu suka fito gabaɗaya suka shige gidan. Da murna Ummi ta tarbe su tana faɗin “Maraba lale sannun ku da zuwa.”
Murmushi Andizo ta yi suka zauna Ummi ta sa aka kawo musu ruwaai sanyi suka sha sannan suka gaisa, sai da suka jima Salim ya miƙe ya ce “To Ummi mu za mu koma gida nan da kwana uku zan zo na ɗauke ta.”
Ga in Andizo ta tashi ta ce “To ai da ka bar mana har Khadija a nan in yaso ka taso daga aiki sai ka zo ka ɗauke ta, ko ba haka ba Aminatou.”
Dariya ta yi tana kallon Salim domin ta san ba lalle ba ya bar Andizo ta zauna ba, ruwa ta kurɓa ta ce “E Wallahi Ummi sa mun wuni muna hira.”
Sosa kai Salim ya yi ya ce “Ummi kar nauyin ya miki yawa ga Aminatou kuma ga Khadija, ita fa Khadija ba ta ɗaukan lokaci take cin abinci ai ba, za ki iya, wannan wahalar ta girki ba Ummi.”
“Kai dai ba ruwan ka in dai za, ka barta girki ai ba mai wahala ba ne zan musu duk abin da suka so.”
Ba dan ya so ba ya amince ya fita ya bar musu gidan.
Hira sosai suka dinga yi Andizo na faɗa wa Ummi ta yadda aka shayo kan Salim har y barsu su zo gida, dariya Ummi ta yi ta ce “Salim akwai ɗan rigima Wallahi, ashe duk lokacin nan ba ki taɓa zuwa gida ba? Sai jiya Aminatou ke faɗa mini na yi ta mamaki.”
Turo baki ta yi ta ce “Wallahi fa Ummi kuma kullum so nake na ga su Hajja amma ba dama sai dai a waya.”
Suna tsaka da hira Abida ta dawo daga makaranta, b ba ta kalli inda suke ba sai da Ummi ta daka mata tsawa ta ce “Anya Abida ba a mini musaya ba a asibiti ba da na haife ki? 'yar'uwar taƙi ta zo ki kasa mata sannu da zuwa har ki dinga wani kawar da kai kamar kin ga kashi.”
Ɗaure fuska ta yi ta ce “Ni fa babu ruwana da ita Ummi, a gaban mijinta ta mare ni har sau biyu saboda wannan banzar kishiryarta ya ita ƴar miji daɗi, shi ne dan sun zo dan kula su? To babu ruwana da su ko ni na ce su zo mana gida?” Tana gama faɗin haka ta wuce fuu.
Da kallo suka bi ta Andizo ta ce “Ki rabu da ita Ummi watarana za ta gane abin da take yi wa Adda kuskure ne.”
“Amma dai da ciwo ƙanenka ya nuna ba ya son ganin ka.”
Ba komai Aminatou ta ce suka ci gaba da hura.
Sai bayan La'asar Salim ya zo ya ɗauke ta suka tafi gida.
Tun da Aminatou ba ta nan hidimar Salim ta yi wa Andizo yawa, wani hali ma da ya tsiro ya ce da zarar ƙarfe 12 ta buga na rana zai turo a kai masa abinci, haka take ɗin hidimar da ta ga ƙarfe 10:30am ta yi take tafiya daga part ɗin su Mamma ta je ta ɗaura girki, da haka har sai da Aminatou ta yi kwana biyar sannan ta dawo.
Ta dawo da kwana biyu itama suka ya shirya suka nufi ƙauye, sosai Andizo take murna yau dai za ta ga su Hammanta..
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/10, 12:58 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
31