Sashe 46
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani kalar murmushi Ahmad ya yi yana shafa kai ya ce “In ko haka ne ka kwantar da hankalinka faɗuwa ta zo daidai da zama, dama maganar auren ce nake so na sanar da kai kafin su Abba su zo. A taƙaice dai mun daidai ta kanmu ni da ita za mu yi aure, dama kuma in ba ka manta ba wasiyar da mijinta ya bari kenan ko da mutu kar ta auri wani na aure ta dan mu kula da yaransu.”
Cike da farin ciki Maigari ya iso ƙofar gidansa ya zauna yana faɗin “Kai amma dai wannan batu naka da daɗin ji yake Ahmadu, gaskiya na yi murna na yi farin ciki da jin hakan kuma nasan Hajja sai ta fini jin farin ciki saboda ƙawancansu ita da Hajiya, ina fatan dai tana sonka kaima ba dan cika wasiya za ka aure ta ba harda soyayya ma ko? Saboda idan ba ka sonta ba zan aminta ba duk da na jima ina, addu'ar Allah ya daidai tsakaninku hakan zai fi mana daɗi.”
Shima cike da kin daɗi ya ce “Haba ai Maigari sani ne ba ka yi ni na fara son Khadija kafin ma Yaya Salim ya ganta, to lokacin na yi zurfin ciki ne kuma kasan muna ƴar tsama da ita sau ta raina ni, to kuma da yake akwai rabo tsakanin ta da yayana shi ya sa duk ba wanda ya gane ina sonta ko ita kanta ba ta sani tun da lokacin ba hankali gareta ba. Yanzu dai mun gama fahimtar juna zan sanar da su Abba yau da an jima in na dawo zuwa nan da kwana biyu sai su zo a yi maganar auren.”
Jinjina kai Maigari yake yana murmushi har ya gama maganar sannan ya ce “Ka yi gaskiya Ahmadu hakan za a yi, gaskiya ina farin ciki Allah ya muku albarka itama zan yi magana da ita naji daga ɓangaren ta.”
Saurin tarar numfashinsa Ahmad ya yi ya ce “Ai ko ka tambaye ta ba za ta iya ce maka komai ba, ta ce min kunya take ji ba ta so ta ce komai a kan lamarin nan har a yi a gama ita dai ta amince mini.”
“A to shi kenan sai an jima bari naje na sanar da Hajja wannan daddaɗan labarin.”
“To na Hajja ikon Allah na gode sai an jima.”
Kashe wayar ya yi yana jinjina wa kansa tare da cewa “Idan kin san wata ai ba ki san wata ba, kaima Sultan zan yi maganin ka shi ne har da wani zuwa ka ɗauke ta a mota ina son na ɗauke ta, sai dai ka ji labarin an saka ranar bikinmu lokaci kusa.” Ya ja tsaki ya kunna motar ya hau kan hanya.
Tun da suka fara tafiya ba ta ɗago ba duk da tana jin ƙamshin turarensa mai sanyaya mata zuciya amma ta yi kamar ba ta ji ba, kallon ta ya yi ya ce “Khadija rigima.”
Jingina kanta ta yi da jikin kujera idanuwanta a rufe tana jin shi ta yi shuru, sai da ta ji sanyi a kumatunta sannan ta buɗe idanu ta sauke shi a kansa. Ido ɗaya ya kashe mata yana matsowa kusa da ita ya janyo ta ya manna mata kiss a goshi ta yi banza da shi sai kallon shi kawai da take, ganin haka ya sa ya ɗago da ita ya ɗora kanta a kafaɗarsa ya zagaye ƙugunta da hannu yana sauke ajiyar zuciya. Kasa taɓuka komai ta yi domin jikinta ya yi sanyi ta kasa gane Sultan wani irin mayen kiss ne, ga shi ba shi da kunya a gaban kowa ma zai iya taɓa jikinta abin na damun ta har mamakin kanta take ranar da ya zo gidansu ba ta masa rashin mutumci ba da ya rungume ta, ajiyar zuciya ta sauke tana danganta hakan da kara ƙawarta take ji shi ya sa ba ta iya masa rashin mutumci kamar Ahmad.
“Princess wai ba za ki yi min magana ba? Ko duk fushin ne kike da ni da na saɓa alƙawari?” Ya faɗa yana ɗago ta daga jikinsa, ƙoƙarin haɗa fuskarsa da tata yake ta kawar da kai tana turo baki, hannu ya sa ya shafo bakin cikin wani kalar shauƙi ya ce “Oh my god! Kina tafiya da imanina my wife.”
Sai a lokacin ta ji za ta iya magana ta ɗago tana hararar shi, “Wace ce wife ɗin taka? Dama kai kana da imani ne”
Nuna ta ya yi da hannu yana gyara zaman glass ɗinsa sannan ya kamo hannayenta ya ce “Kin taɓa ganin mutumin da ba shi da imani ko da ɗigo ne? Ya kamata a ce yanzu kin gane inda muka dosa na sanar da Mom a yi bikinmu ko na ɗauke ki mu tafi next month.”
Kasancewar yanzu tana jin turanci ta gane me yake nufi, tsaki ta ja ai kuwa ya damƙi bakin ta yi ƙara ya saki, wani irin kallo ya mata irin na mashaya waɗanda suka kai ƙarshe a buguwa, jikinta ne ta ji ya yi yam ta yi saurin rufe ido tana faɗin “Dalla can ni ka daina mini irin kallon nan ba kyau.”
Murmushi ta yi ya ce “To in ban kalli matata ba wacce mace zan kalla naji sanyi?” Ya faɗa yana gyara mata jakarta.
“Kai ka sani dai, a hakan ne kake tunanin za ka aure ni da ko Sallah ba ka yi.”
Saurin kallon ta ya yi da mamaki, maganarta sai ta tuna mishi lokacin da ya sato ta ta ce mishi baya Sallah, girgiza kai ya yi ya ce “Wa ya faɗa miki ba na sallah? Ni fa musulmi mai zai hanani yin Sallah da lafiyata da komai, jam'i ma nake zuwa masallaci tun shekarun baya da kika ce in dai ba na yin Sallah ba za ki so ni ba, na canja abubuwa da yawa da kika sanni da su Khadija, yanzu ko giya sai na yi wata biyu uku ban sha ba idan ma kika ga na sha to an ɓata mini rai ne na rasa wanda zai kwantar mini da hankali sai na sha na kore damuwa.” Ya ƙarashe maganar cikin yanayin damuwa ƙarara a kan fuskarsa.
A zuciyarta ta ji daɗi da yake Sallah, amma a fili sai ta yatsine fuska ta ce “Kana saya wa kanka cuta dai ba kore damuwa ba, jiya da sauran kayan shaye-shaye suna lalace kayan ciki kamar su huhu ƙoda, zuciya, kai har ma da ƙwaƙwalwa ita ce take fin komai samun matsala, idan ma ka faɗa dan naji daɗi ne ba ka birge ni ba sai na gani a, zahiri, ko yanzu wannan motar taku warin kayan maye take kamar kodin kamar giya.” Ta faɗa tana murguɗa baki daidai sun zo get din makaranta.
Za ta fita ya yi saurin ruƙo ta ya marairaice fuska kamar ƙaramin yaro ya ce “Please kiss me one.”
Kallon banza ta watsa mishi ta ce “Kai ni fa ba ƴar iska ba ce da har kake ƙoƙarin nuna mini iskanci, ba za, a yi kiss ɗin ba.”
Kwantar da kansa ya yi a jikin kujera kuma ya ƙi sakin ta, ɗayan hannun ya sa ya ce “Idan ba ki yi mini ba a baki ba za ki tafi ba sai ki zaɓa na wuce da ke hotel mu wuni a can ko kuma ki mini one kiss mai sugar.”
Dafe kai ta yi kamar ta sa kuka ta ce “Don Allah Daddy Farrah ka rabu da ni na makara ni ba na son iskancin nan naka.”
“Ai kuwa sai kin so ko ki mini ko mu wuce.”
Banza ta mishi ga Amira a tsaye a gefen motar tana jira ta fito, danne dariyarsa ta yi ya ce “Oya to yi mini a kumatu.”
Gabaɗaya tsoro ya rufe ta gani take kamar zai sake sace ta a karo na biyu, ba dan ta so ba ta miƙa fuskarta ya yi saurin ruƙo ta, runtse ido ta yi za ta mishi kamar ya faɗa a kunci amma sai ta ji saɓanin hakan sakamakon ɗumi da ta ji ya ratsa mata baki, kwalalo ido waje ta yi tana ƙoƙarin kwacewa amma ya riƙe ta kam kamar zai ƙarya ta, inna lillahi kawai take faɗa a zuciyarta ganin ya ƙi sakin ta, sai da ta daddage ta minti ne a hammata ya sake ta ta dinga mayar da numfashi, buɗe motar ya yi ya fito ya za gaya itama ya buɗe mata da kyar ta fito tana sunkuyar da kai gani take kamar Amira ta gane abin da Uncle ɗin nata ya mata.
“Haba Khadija kuma shi kenan sai ku zauna kuna ta hira alhalin kin san mun makara.” Ta kalli Sultan ta ce “Duk lefin ka ne Uncle nan fa makaranta ce muka zo ga shi ƙila ba za mu samu haiga ba sai malamin da ya shiga ya gama ya fito za mu samu shiga.”
Murmushi ya yi yana shafa gemunsa da yake sheƙi ya kalli Andizo ya ce “Ƙawar taki ce ta cika neman rigima, wai so take na kai ta wajen Farrah ni kuma na ce ta bari sai kun yi hutu lokacin za mu yi aure sai mu koma can da zama.”
“Kai!” Ta faɗa tana kallon shi jin sharrin da ya mata, kwafa ta yi ta kama hannun Amira ta ce “Muje kinga ba na son doguwar magana.”
Kuɗi ya zaro a aljihunsa ya kamo hannunta ya damƙa mata ya ce “Wannan tukuici ne da aka kula da ni yau.”
Ƙin amsa ta yi sai da Amira ta yi magana sannan ta amsa ta mishi godiya suka yi gaba, sai da suka ɓace wa ganinsa sannan ya juya ya koma cikin motar suka tafi..