← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 75

Sashe 19

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarin ruwa aka sa mata da allurori sannan likitan ya ja shi office, sai da ya gama rubuce-rubuce sannan ya ɗago ya kalle shi ya ce “Haba boss ya da haka? Wannan yarinyar gaskiya ka fi ƙarfinta ya kamata ka barta ta ƙara girma, in kuma ba za ka haƙura sai dai kake bin ta a hankali har ta saba tun da yarinya ce..” Haka ya ci gaba da yi masa faɗa haɗi da nasiha sannan ya ba shi takarda ya ce ya sayo maganin da ya rubuta, godiya ya mishi yana sosa kai ya tashi ya fita..

Sai Washegari ƙarfe 9:pm suka dawo gida inda Aminatou ta musu girkin tarba. Da kanta ta taro su daga bakin mota ta ce a ɓangaren ta za a ci abincin dare. Andizo ta tsaya tana riƙe da hannun Salim, kallon ta Aminatou ta yi zuciyarta na tafasa ta danne ta ce “Haba ƙanwata ɓangaren nawa ne ba ki son zuwa?”
Girgiza kai ta yi ta ce “A a ni na gaji sosai jikina ciwo yake mini kamar an kakkarya ni, ni zanje na kwanta ba ni da lafiya ma..” Ta faɗa tana sakin hannun Salim ta soma tafiya a hankali tana layi kamar mai maye.
Zaro idanu Aminatou ta yi tana kallon Salim a kiɗime ta ce “Salim me ka yi wa ɗiyar mutane?”
Kallon ban gane ba ya mata ya nufi Andizo da ta doshi part ɗin Mamma tana tafiya tana rike bayanta. Tafa hannu ta yi kamar za ta fasa ihu sai kuma ta biyo su da sauri tana faɗin “Ka ga kawo ta nan muje ciki na mata ruwan ɗumi ta yi wanka za ta ji sauƙi.”
Ganin Maigadi na kallon su sai ya miƙa mata ita ta ruƙo ta suka yo part ɗin ta, a kujera ta kwantar da ita ta ce “Khadija ina da ina yake miki ciwo? Meye ya faru da ke haka? Ko wani abin ya miki?”
Kasa cewa komai ta yi sai nuna mata Salim ta yi da hannu, kallon shi kawai Aminatou ke yi tana jin kamar ta cinna musu wuta, ita ta rasa me Salim zai ji a jikin wannan ƙaramar yarinyar da ya ɗauke ta ya je ya yi abin da yake so.

Hawaye ne suka zubo mata da ɗago da kyar ta ce “Mai hankali ka kaini wajen Hajiya babba.”
Saurin kama ta ya yi ya ce “Kinga Aminatou ki bari na kai ta wajen Hajiya Babba sai na dawo, kin san dai halin ta in dai ta san ba ta da lafiya ba a faɗa mata ba yanzu za ta kama faɗa..”
Wani kallo ta watsa mishi ta ce “Ba ta da lafiya ko kuma dai ka jaza mata rashin lafiya? Haba Salim kai fa ka ce mini rainon ta za ka yi har sai ta ƙara girma ka ɗauke ta a matsayin mace, amma me ya sa ka yi haka?.”

Ƙawar da kai ya yi dan zuwa yanzu ransa ya soma sosuwa, gyara tsayuwa ya yi ya ce “To lefi ne dan na yi hakan? Ko akwai in da aka mini katanga da keɓewa da matata? Kinga ba na son irin wannan tambayoyin marar kai, haka kawai daga ganin yarinya a haka sai ki dinga tambayar ta me aka mata? Ba na son irin haka tun da dai ni ba zama na yi da ke ba na ce na miki alƙawarin yin hakan.” Yana gama faɗin haka ya wuce ya bar mata palon...

Baki buɗe Aminatou ke kallon ƙofar palon, kasa zama ta yi sai kuma ta tashi ta nufi ɗaki da sauri, ko minti ɗaya ba ta yi ba ta fito ta shiga kitchen nan ma ta fito ta dawo palo tana nube-dube. Can ta hango abin da take nema wato wayarta, hannu na rawa ta danna wa Sabrin kira amma har ta gama ringing ba a ɗauka ba ta kuma kira, nan ma shuru. Jifa ta yi da wayar ta zauna jagwaf tana huci, kasa daurewa ta yi ta fashe da kuka tana sumbatu, “Wallahi Salim ba ka isa ba ka yi tarayya da wata 'ya mata kai nawa ne ni kaɗai, idan kuma wata ta yi kuskuren haɗa shinfiɗa da kai tabbas sai na ga bayan ta, sai ta gwammace gara mutuwar ta da rayuwa da kai a matsayin miji, na tsane ki Khadija! Na tsane ki! Tun da kuka yi kuskuren barin mijina ya kwana da ke gado ɗaya zan nuna miki iyakarki..” Haka ta dinga sumbatu tana jifa da duk abin da yake kusa da ita, kukan da ta yi har ya fi na ranar da aka kawo Andizo gidan...

Suna isa Hajiya Babba suka samu a palo an yo mata shayi ta miƙe ƙafa tana sha tana kallon sunna tv hannunta riƙe da carbi tana ja..
Kallon su ta yi sai kuma ta kawar da kai tana faɗin “Allah na tuba dama ai sai da na faɗa miki za ku dawo ku same ni ina zaune, to yanzu daga gidan uban wa kuke?” Ta faɗa tana kallon Andizo da duk ilahirin jikinta ya soma rawa, gane hakan ya sa Salim da sauri ya ɗauke ta ya zaunar a kusa da Hajiya Babba yana zama shima. Da dabara Andizo ta zame ta kwato kanta a cinyar Hajiya Babba wasu hawaye masu zafi suka zubo mata, gabaɗaya ko'ina na jikinta ji take kamar ana yankan naman jikinta, kanta da yake mata ciwo ji take kamar an ɗora mata wani gingimeman abu mai nauyi. Aje shayin da ke hannun ta yi ta ɗan gyara zama ta kai hannu ta taɓa wuyanta, da sauri ta kalli Salim ta ce “Subhanallahi! Salimu zazzaɓi ne a jikinta ai, maza kira likita ya zo ya duba ta ina kuka je kuka zauna? Kana ganin yarinyar mutane ta kamu da cuta kaƙi miƙa ta asibiti? Wannan shi ne riƙe amanar da na ba ka? In ba za ka iya riƙewa ba ai sai ka faɗa mini na amshe ta na kula da ita..”

Sunkuyar da kai ya yi yana tsoron ta tona mishi asiri yau ya shiga uku a wajen Hajiya Babba, sosa kai ya yi ya ce “Mun je fa asibitin an ba ta magani har ruwa aka sa mata, shi ne ta ce nan zan kawo ta ba za ta zauna a can ba..”

Dago ta ta yi tana ƙara rungume ta sai sannu take jera mata, mai aikin gidan ta kwallawa kira sai ga ta ta fito da sauri ta durkusa ta ce “Hajiya gani.”

“Je ki haɗa wa jikata ruwan ɗumi a banɗakina, sannan ki ɗaura mata abincin mai ɗan ruwa-ruwa ba ta da lafiya.”
To ta ce ta tashi ta nufi ɗaki da sauri, bayan ta haɗa ta fito ta ce ta haɗa ta ce ta kama Andizo ta kai ta banɗaki ga ta nan zuwa, ta amsa da to ta sunkuya a kusa da ita ta ce “Matar Oga tashi muje ki yi wanka.”
Ba muso ta miƙa mata hannu ta tashe ta suka tafi, Hajiya Babba ta tashi ta ce “To kuma zaman me kake yi? Ba ni maganin sai da safe.”
Miƙa mata ya yi a sanyaye jin ta ce masa sai da safe ya kuma gane yau dai ba za ta kwana kusa da shi ba. Amsa ta yi ta wuce tana mitar wai bai kaita asibiti da wuri ba shi ya sa zazzaɓin ya rufe ta har ta kasa yin magana, shi dai bai ce komai ya yi baya ya lumshe idanuwansa yana jin ba daɗi, anya zai iya barin ta ta kwana a nan tun da yau ma kwanan ta ne? Girgiza kai ya yi ya ci gaba da zama har Mamma ta fito daga ɗaki ta same shi sukuku..

“A'a, Salim lafiya dai ka zo ka zauna kai kaɗai a palo?”
Gaishe ta ya yi sannan ya ce “Khadija ce ba ta da lafiya zazzaɓi mai zafi take, shi ne ta dinga kuka sai na kawo ta wajen Hajiya..”

“Subhanallahi! Ko dai wannan wajen da kuke zuwa wanka ka kaita ta yi wanka har zazzaɓi ya kama ta? Kai fa yanzu ba yaro ba ne Salim bai kamata ba ka kaita can. Dama da kake ce mata za ka kaita ashe da gaske kake? To ni dai babu ruwana kai da Hajiya Babba Allah ya ba ta lafiya.”
Amin ya ce sannan ya zame ya kwanta..

Can ciki Hajiya Babba ta samu Andizo ta shiga ruwan ta zauna har bacci ya ɗauke ta, cike da tausayi ta ce “Allah sarki kinga bacci ma ta yi a ruwan.”
Tashin ta ta yi ta cuɗa ta da kyar take motsa jikinta, ruwan ta canja mata ta sake zuba mata wani ruwan ta ɗarwaye jiki sannan ta miƙa mata towel ta ɗaura suka fito, da kanta ta kwantar da ita ta lulluɓe ta da bargo mai kauri ta fita ta sa aka kawo mata dafa-dukar taliya da ruwan-ruwan ta, sosai ta ji daɗin abincin ta ci mai ɗan yawa sannan ta koma ta kwanta nan da nan wani bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita..

1:am na dare Salim na nan kwance a palo ya kasa tafiya ji yake ba zai iya bacci ba in ba ta kusa da shi. Sai da ya tabbatar Hajiya Babba ta yi bacci ya yi sanɗa ya buɗe ɗakin ya ga Hajiya Babba ita ɗaya a kan gado, daɗi ne ya kama shi ya rufe ƙofar a hankali ya nufi ɗayan ɗakin ya buɗe. A lulluɓe ya same ta tana bacci hasken ɗakin ɗan kaɗan da aka bar mata shi ya ba shi damar kallon fuskarta sai yatsina ta take alamar baccin ba ya mata daɗi..
A hankali ya hayo gadon ya buɗe bargo ya shige, kamar jira take ta matso ya yi saurin janyo ta ya rungume har yanzu zazzaɓin na nan, ƙara ƙanƙame shi ta yi ta saki jiki ta ci gaba da bacci. Shi kuwa duk tausayin ta ya kama shi sai shafa kanta yake yana tofa mata addu'a har bacci ya ɗauke shi...

_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/3, 12:33 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_

26
Chapter 19 · 0% Book details