← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 75

Sashe 65

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kiran Sallar assatu ne ya tayar da shi ya buɗe ido yana ƙaranto addu'ar tashi daga bacci, a hankali ya zame ta daga jikinsa ya sauka a gadon ya dauro alwala. Bayan ya fito ya jima a kanta a tsaye yana son tashin ta amma ya ga baccin ya mata daɗi, sai da ya ji ana tayar da iƙama sannan ya soma tashin ta. A hankali ta buɗe ido ya kai hannu ya bubbuga kumatunta Sanyin ruwa ya sa ta wartsake ta tashi zaune.
“My wife tashi ki je ki yo Sallah ni na wuce masallaci.” Ya faɗa yana wucewa.
Sauka ta yi ta dauro alwala ta soma gabatar da Sallah..

Sai ƙarfe bakwai ya dawo ya tarar da ita tana bacci ta jingina kanta da jikin gado, sanin jirgin ƙarfe shaɗaya za su bi ya sa shi ɗaukan ta ya cire mata hijabin ya kwantar da ita, shima cire rigarsa ya yi ya hayo gadon ya, kwanta yana shinshinar gashin kanta da ya sha gyara sai wani sihirtaccan ƙamshi yake fitarwa har bacci ya ɗauke su.

Ba su farka ba sai karfe 10:20am ya sauko ya ɗauke ta ya yayo mata wanka idanuwanta cike da bacci ta saki jiki kamar marar lakka a jiki, shi kuwa daɗi yake ji saboda zai ɗauke ta su wuce salin alin kafin ta tayar da fitina. Bayan ya shirya ta shima ya shirya ya kama hannunta suka fito zuwa palo, daret kan dinner table suka nufa ya haɗa mata tea ya ba ta tana sha tana mishi mitar wai bai iya haɗa tea ba, dariya ya yi ya ce ya ji ta dai sha. Kular da ke gaban su ya buɗe ya ga soyayyar doya ce wadda aka haɗa da kwai ya juyo ya kalli Andizo ya ce “My wife za ki ci wannan abincin?”
Kallon abincin ta yi ta ystsina fuska ta kawar da kai gefe, ganin haka sai ya rufe ya tashi ya wuce ɗaki ya janyo akwati ƴar madaidaiciya ya aje a Palo, ɗakin ya sake komawa tana nan zaune jim kaɗan ta ga ya fito cikin wata dakakkiyar shadda kalar kayan jikinta pink colour, dinkin Kamar a jikinsa aka zana ya masa kyau sosai duk da ya rame. Kasa ɗauke ido ta yi a kansa har ya ƙaraso gaban ta sai jin iska ta yi a idanuwanta, saurin rufe ido ta yi ya kama ta ya miƙar ya ce “Mu je kar jirgi ya zo ba mu isa ba.”
Har ta yi taku ɗaya sai kuma ta tsaya cak ya juyo ya kalle ta, “Ya kuma kika tsaya?”
Kamar za ta sa mishi kuka ta ce “To ba sun ce za su dawo da safe ba me ya sa har yanzu ba su zo ba?”
Fuskantar ta ya yi ya ce “Am sorry kina bacci Ahmad ya kira ni ya ce su bacci suke Amira ba ta jin daɗi gajiyar zirga-zirgar ce da ta sha.”
Baki ta turo ya harde hannayensa a ƙirji yana kallon ta da wani irin yanayi, in tana mishi shagwaɓa sai ya ji kamar tana tafiya da numfashinsa ne, gaba ta yi ta zauna a kan kujera ta kafe ta ce sai ya kira su sun zo, ya yi ta rarrashin amma taƙi yarda su tafi ita lalle sai an zo an sanar da ita yadda aka yi wannan badaƙalar. Sai da ya kira Amira ta sharara mata ƙaryar suma za su je Nigeria nan da kwana biyu sannan ta yarda suka tafi.

Sun isa filin jirgin aka sauke su suka nufo inda za su zauna su yi jira na minti goma, wasu kattai ta gani su shida suna nufo su masu kama da bodyguard ai da sauri ta maƙale a bayan Sultan, dariya ya yi ya janyo ta ta dawo gefen shi ya ce “Ki nutsu my wife yarana ne fa.”
Ajiyar zuciya ta sauke tana dafe ƙirji ya sa hannu yana ruƙo ta har suka iso.
Hannu suka dunƙule aka yi gaisuwar yan gayu ta kalle su tana mamaki ganin yadda suke wasa da dariya, bayan shi ta koma komawa har sai da suka gama tattaunawa suka bar wajen sannan ta fito, dariya ya yi ta mata tana hura hanci sai ga jirgin da za su hau ya sauka..
Bayan sun shiga suka miƙa can gaba in da sai manyan mutane suke zama wato special kujera, sun kusa isa sai ga ɗaya daga cikin ma'aikatan jirgin ta fito, ganin Sultan ya sa ta faɗaɗa fara'arta tare da cewa “Welcome Mr J.” Ta ƙarashe maganar tana miƙa mishi hannu alamar su gaisa. Saurin shiga tsakanin su ta yi ta fuskanci Sultan idanuwanta cike da ruwa ta saɓa baki, gab take da fashewa da kuka ya kamo hannayenta ya ce “Mene ne faɗa mini naji?” Ya yi maganar cike da tsananin kulawa irin ta masoyan da suke ƙaunar junansu kamar ba gobe.
Hannu ta ɗaga mishi murya na rawa ta ce “Ni ka ɗauke ni ƙafafuwana ciwo ba zan iya tafiya ba.”
Murmushi ya yi ya ɗauke ta cak ya mata rungumar jarirai ya ce “Abu mai sauƙi hakan ya miki?”
Gyaɗa kai ta yi tana kwantar da kanta a ƙirjinta ta kalli wannan mata ta gefen ido. Sultan ya gyara tsayuwa ya ce ta ba su waje, har sun wuce sai ta kasa haƙuri ta bi su har kujerar da suka zauna, takaici ne ya rufe Andizo amma ba ta ce komai ba tana son ta ga iya gudun ruwan matar.
“Mr J wannan yaronka ne?” Ta yi maganar da Hausar ta wadda ba ta gama shiga bakinta ba.
Girgiza kai ya yi ya ce “Amaryata ce.”. Ya ba ta amsa.
Zaro ido ta yi cike da mamaki tana tunani, kenan zuwan da ya ce mata zai yi Niger aure ne ya yi? Jinjina kai ta yi ta ce “Congratulation.”
Kai kawai ya gyaɗa mata dan ya matsu ta ba shi guri da matarsa su huta, jiki ba ƙwari ta bar wajen ta fice da sashen ta koma baya. Kwafa Andizo ta yi can ƙasa ta ce “Shegiya futsararriya wai har da wani miƙa mishi hannu, Wallahi duk sai na ci muku uwa ɗaya bayan ɗaya sai na raba ku da shi ko a hanya kuka ganshi sai kun canja wata.”
Gum Sultan ya yi da bakinsa ko motsi bai yi ba dan kar ya nuna alamun ya ji maganar da ta yi, zuciyarsa ta ƙara narkewa a login ƙaunar ta ya sa mata bel ya yi baya ya lumshe idanu yana shafa kanta...

*Ina matuƙar godiya da addu'oinku Allah ya saka muku da alkhairi*

_Maman Nusaiba ce_
[7/14, 10:49 PM] Ummu Amjad: ADZ

48

Tana jin yadda yake taɓo mata gashi ta yi luf a jikinsa kamar mage, sai da suka kusa zuwa Nigeria sai ga wannan matar ta iso fuska ba yabo ba fallasa, ɗago kai ya yi ya kalle ta ta aje musu cake da ruwa da duk abin buƙata wanda in ka shiga jirgi musamman manyan mutane ake kawo musu, murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, kallon Andizo ya yi ya ga ta yi kicin-kicin da fuska tana kallon abincin, ɗago da ita ya yi ya ce “My wife Ko akwai abin da kike buƙata a kawo miki?”
Turo baki gaba ta yi tana dora hannunta ɗaya a ƙirjinsa, sai da ta ɗago ta ga tana nan a tsaye ta kawar da kai gefe ta ce “Ruwa kawai zan sha.”
“To nima dai ruwa kawai nake so tun da ba za ki ci komai ba.”
Kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, kayan abincin ya ce ta mayar ruwa suke buƙata, sororo take kallon shi cike da takaicin canja mata da ya yi daga jiya zuwa yau, idanuwanta ne suka ciko da hawaye ta yi saurin ɗauke kayan ta fita. Da kallo ya bi ta yana jin ba daɗi ganin hawaye a fuskarta, ita kuwa Andizo tana ganin ta tafi ta sauke ajiyar zuciya a ɓoye ta koma jikinsa ta kwanta babu jima bacci ya yi gaba da ita..
Chapter 65 · 0% Book details