Sashe 60
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da dare bayan sun ci abinci ana hira Ahmad ya dubi Hajiya ya ce “Ina so zan faɗa muku wata magana ban san da mai za ku ɗauke ta ba, amma duk abin da kuka ji da gaske nake kuma na yi shi ne dan sadaukarwa.”
Duka palon suka kalle shi Hajiya ta ce “To kai kuwa Ahmadu mene ne shi haka wadda kake tunanin za mu kalle ta ta wata fuskar?”
Gyara zama ta yi ya yi ƙasa da kai ya ce “Daga yanzu na janye aure na da Khadija.”
Hajiya ta matso kusa da shi da sauri tana tafa hannu ta ce “Wannan ɗin wacce irin magana ce Ahmadu? Anya ba ka fara shaye-shaye ba?”
“Babu abin da nake sha Hajiya ina cikin hankalina, nima ba da son raina zan yi hakan ba sai dan na yi saukarwa ga abokina Mr J.”
Shuru suka yi suna kallon shi, Hassana ta nisa ta ce “Wallahi Yaya dama ni na jima da ganin soyayyar Mr J a idanun Khadija, musamman lokacin da ya kaita asibit, na tabbata ta fi son shi sama da kai a zuciyarta kawai dai faɗa ne ba za ta yi ba.”
Hussaina ta amshe maganar da cewa “Tabbas haka ne domin na taɓa jin ta wata rana tana waya tana kuka tana sanar da Anty Aminatou, auren ka da za ta yi kawai dan farin cikin su Maigari da su Hajiya za ta ba dan tana jin ka a zuciyarta ba, amma ita Sultan take so kawai dai dan ba shi da hali mai kyau shi ya sa ta dangana ta zaɓi ta faranta muku rai ita ta ba wa zuciyarta haƙuri, da aka ce zuciyarta ta fara kumbura na karo na biyu na so na sanar da ku abin da naji tana faɗa sai kuma na yi gum da bakina, amma dama can Sultan take so ba kai ba Yaya kuma naji daɗi da ka haƙura ta auri wanda take so, Allah dai ya ba ta lafiya.” Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da suka zubo mata.
Shuru palon ya yi Abba ya girgiza kai yana nazarin maganar ya rasa ta ina zai fara sanar da Maigari Ahmad ya janye auren Khadija, Mamma ta janye tagumin da ta yi ta ce “Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gareka, kuma ka kyauta da ka yi hakan.”
Murmushin yaƙe Ahmad ya yi ya ce “Dan ma, ba ku ga halin da yake ciki ba da sai kun miahi kuka. Nan ya kwashe komai ya sanar su har vidéo da ya gani da bayanin Amira, gabaɗayan su jikinsu ya yi sanyi da jin labarin Sultan suka mishi addu'ar samun lafiya.
“Gobe ni zan je na fara fahimtar da Maigari komai ba sai ka je ba Abba.” Ya faɗa yana tashi ya wuce..
Washegari ya shirya ya nufi gidan su Amira da ta miahi kwatance, yana isa suka fito ita da Mama ya fito ya buɗe musu mota suka kama hanya..
Kamar yadda aljani Najibu ya yi alƙawari da su Malam suka dawo ya dawo shima ya kuma kawo abokan aikinsa, sai da aka yi dambarwa da su sosai sannan wani daga cikin su ya ce “Mu za mu tone sihirin da muka binne, amma ba fa iya wannan ba ne sihirin da ke jikinta akwai baƙin sihiri da aka yi mata, shi ne wanda bakinta yake cika da ƙuraje a zare mata kuzari ta kasa tashi, idan ta kwanta a danne mata ƙirji ta kasa tashi sai lokacin da suka ga dama su rabu da ita, kowanne daban-daban ne.”
Malam ya yi tasnima yana kallon Khadija ta aka birkice ta ƙafafuwanta a lauye bakinta ya karkace, jinjina kai ya yi ya ce “To su ina suke?”
Dariya aka yi sannan ya ce “Ku nemo su kamar yadda kuka nemo mu.”
Malam ya kalli liman ya ce “Lalle yarinyar nan ko su waye suka mata wannan ɗanyan aikin sun cika azzalumai na ƙarshe. To shi kenan ku tone ku lalata shi idan kuma kuka, mini ƙarya dukkan ku sai na ƙona ku daga ku har waɗanda suka buya.”
“Haba Malam ai mun yi maka alƙawarin hakan yanzu haka ma ɗaya daga cikin mu ya tone ga shi can yana lalatawa, idan muka fita a jikinta za ta yi amai baƙi hakan shi ke nuna ta amayar da cutar da ke cikinta saura ɗayan.” Suna faɗin haka sai gani suka yi ta maƙure a waje ɗaya ta dinga jero attishawa, sai da ta yi bakwai sannan ta soma tari sai amai ya biyo baya mai wani, sai da ta gaba tas Umar ya ɗauko ruwa ya zuba mata a bakin ya ce ta kuskura bakinta ta zubar, sai ta wanke har fuskarta sannan ta ɗago kai tana kallon su.
Liman ya kiran sunanta ta amsa tana bin su da kallon mamaki, gefe Umar ya janye ta Maigari ya ce su canja wajen zama su koma can gefe a gyara wajen, ita dai kamar raƙumi da akala haka take bin su tana jikin Umar sai sannu yake jera mata. Bayan, sun zauna Malam ya ƙara gyara zama ya fara karatu yana yi yana fes mata ruwan addu'ar da ke gefen shi.
Sai da aka ɗauki lokaci mai tsayi sannan aka samu nasarar samun su, ɗaya daga cikin su ya ce “Malam ka yi haƙuri karka ƙona mu za mu faɗa.”
Gyara zama Malam ya yi ya ce “To ina jin ku me ya sa kuke cutar da baiwar Allah?”
“Ka yi haƙuri Malam muma saka mu ne aka yi amma za mu rabu da ita, duk sihirin da muka mata za mu warware.”
Sai da Malam ya jigatar da su sosai sannan ya umarce su da su warware komai kuma su fita daga jikinta, cikin ladabi suka bai wa Malam haƙuri sannan suka ce sun warware komai tukun ya ba su izinin fita, haka ta dinga jero attishawa har sai da Umar ya riƙe ta saboda ƙarfin attishawar sai da ta yi kamar za ta kifa. Hamdala suka yi suna yin kabbara tare da yi wa Allah kirari da ƙarfin ikonsa an yi nasara yau sun fita gabaɗaya.
Ruwan addu'ar Malam ya ba da ya ce ya dinga shafe mata jiki da shi in za ta kwanta, godiya sosai suka mishi Maigari ya rasa da me zai saka wa wannan baƙin malaman masu ɗinbin tarin albarka da suka zama sanadin warakar jikarsa mafi soyuwa a zuciyarsa, shi ya sa ake cewa baƙo raɓa ne kuma rahama ne..
Ƙarfe 1:20pm suka iso garin in da aka musu jagora har cikin gidan. Sai da suka gaisa sannan Ahmad ya gabatar musu da Amira da mamanta sun zo ganin Khadija, sosai Hajja ta ji daɗi ta musu jagora zuwa ɗakin da Andizo ke kwance tana baccin wahala, shi kuma Ahmad ya nufi wajen Maigari domin faɗa masa abin da ya kawo shi ko sun koma a kan lokaci.
Suna shiga ɗakin a zaune suka same ta tana murza ido, da sauri Amira ta isa in da take ta ce “Alhamdu Lillah Khadija.”
Saurin buɗe ido ta yi sai ganin Mama da Amira ta yi a gaban ta, sake murza ido ta yi ta ɗauka ko gizo ne suke mata sai da ta ji Amira ta rungume ta ta fashe da kuka, itama kukan take sai suka ba wa Mama tausayi ta same waje ta zauna tana kallon su....
_Maman Nusaiba ce_
[7/9, 12:06 AM] Ummu Amjad: ADZ
46
Sai da suka gama kukan ganin juna sannan Amira ta fara ɗago da Andizo daga jikinta tana ƙare mata kallo, wani irin tausayin ta take ƙara ji na shigar ta ganin yadda ta koma kamar ba ita ba, itama kallon ta take tana tuna maganar su ta ƙarshe da ita.
Sai da Mama ta gaji da abin nasu ta ce “Khadija sannu ya jikin naki?”
Dogon numfashi ta sauke ta juyo ga Mama tana gaishe ta har tana tambayar baban Amira Mama ta ce yana lafiya. Bayan sun huta sun ci abinci Hajja ta zo ta fita da Andizo Amira har za ta bi su Mama ta riƙe ta tana dakatar da ita, “Ki tsaya su dawo mana kika sani ko magani ne za a ba ta?”
Turo baki ta yi ta zauna tana faɗin “Ni ba na so ta haɗu da yaya Ahmad har sai na sanar da ita komai, kinga ko da ya yi mata maganar za ta fi fahimtar shi.”