Sashe 49
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“To amma me ya sa ba ki ba ni amsa ba?”
Hararar shi ta yi tana tsuke ɗan ƙaramin bakinta da ya sha man lips sai sheƙi yake, lumshe ido ya yi yana ciza lip ɗin sa na ƙasa, gabaɗaya yarinyar tana rikitar da tunaninsa ya ƙagara ta ba shi amsa ko zai samu Mom da magana a yi auren nan ko hankalinsa ya kwanta ya samu nutsuwa.
Ba ta ko kalle shi ba sai marmatsa ƙafa da take saboda zafin takalmi da zafin ciwo sun haɗe mata, ganin tana yatsina fuska sai ya kalli ƙasa ya ga yadda take yi da kafar, cike da kulawa ya kalle ta ya ce “My wife ko ciwo ƙafar take miki ne?”
Girgiza kai ta yi tana kumbura baki ba ta yi magana ba, ganin hakan ya sa ya ɗago ƙafar ya cire takalmin ai kuwa ya ga yadda ƙafar ta ɗauki kumburi, a ruɗe ya ƙara ɗagowa ta dora ta a kan cinyarsa yana kallon ta da kyau. Runtse ido ta yi da ya dan danna ƙafar ta yarfa hannu ta ce “Please ka bari akwai zafi.”
Bakinsa ya kai kan ƙafar ya dinga hura mata isa, shuru ta yi tana jin saukar iskar bakinsa sai ta ji zafin ya ragu hakan ya sa ta saki jiki ta jingina kanta da jikin kofar motar tana kallon shi.
“Sannu my wife ya aka yi kika ji ciwo har ƙafar ta fara kumbura ba ki je asibiti an duba miki ba?”
A shagwaɓe ta kalle shi idanuwanta sun cika taf da ruwa, gira ɗaya ya dage mata yana mata wani irin kallo mai wiyar fassarawa, yana tsaka da hura mata suka iso makaranrar ta soma ƙoƙarin janye ƙafarta amma ya riƙe ya hana ta motsi.
“Kinga mu je asibiti a duba miki ƙafar nan kar ciwon ya miki yawa.”
Maƙale kafaɗa ta yi ta ce “Zai daina ai sake mini ƙafa kar in makara irin na jiya da ka hana ni fita.”
Ba dan ya so ba ya sake mata ƙafar ta buɗe motar za ta fita ta juyo a hankali cikin Sanyin murya ta ce “Thank you.”
Jinjina mata kai ya yi yana bin ta da kallo kamar kar ya bar ta ta fita, tana fitowa Amira ta iso suka nufi ciki inda suka samu Arma da Sadiya suna jiran su.
Gaisawa suka yi Arma ya ce “Wallahi yau wani Monsieur ne mai zafi aka kawo shi zai fara shiga classé ɗin mu, dan haka ku zo mu shiga daga ciki.”
Tashi suka yi suka shige ciki suka ci gaba da tattaunawa a kan darasin da zai musu har ya zo.
Suna gaf da tashi ƙafar Andizo ta ƙara kumbura take zazzaɓi ya rufe ta, da kyar ta lallaɓa suka fito Amira na riƙe da ita suka samu waje suka zauna. Number Sultan ta kira ringing ɗaya a na biyu ya ɗauka, ko hello bai ƙarasa faɗa ba Amira ta taru numfashinsa ta ce “Uncle akwai matsala fa don Allah ka yi maza ka zo jikin Khadija ya rikice zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta.”
Daga can ɓangaren Sultan da yake yin Sallama da Mama zai wuce airport zai koma Nigeria ya yi saurin faɗin “Subhanallahi! Gani nan zuwa yanzu karki kuskura ku shiga motar haya.”
To Amira ta ce sannan ya kashe Mama ta dube shi ta ce “Lafiya dai yaron?”
Cikin damuwa ya ce “Wai Khadijata ce zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta suna can a makaranta da Amira, na fasa tafiya zan je na kai ta asibiti zuwa gobe in na ga jikin da sauƙi sai na tafi.”
“A to in kuwa haka ne bari mu tafi tare.”
Mota ya buɗe mata yaransa biyu da ya zo da su suka iso za su shiga ya ɗaga musu hannu ya ce “Ba sai kun biyo mu ba idan ina buƙatar ku zan kira ku.”
To suka ce suna matsawa daga kusan motar ya shiga mazaunin direba ya ja suka bar gidan..
Andizo sai rawar sanyi take Amira ta cire hijabinta ta rufa mata ita kuma ta warware ɗankwalin kanta ta yafa sai sannu take jera mata, suna nan zaune sai ga su Sultan sun iso, yana gana packing ya fito da sauri ya kamo ta zai ɗauke ta Mama ta ce “Ka bari mu shigar da ita ni da Amira.”
Ba dan ya so ba ya sakar musu ita suka kama ta yana biye da su har bakin mota, buɗe musu ya yi suka saka ta a baya suka shiga sai asibiti..
Kasancewar Sultan na da aboki babban likita hakan ya sa ya kira shi, yana ɗauka ya ce ga shi nan zai zo da mara lafiya ya amsa da to. Suna isa aka amshe ta suka yi ciki da ita, tsaye ya yi yana kallon kofar sai da Mama ta mishi magana sannan ya iya zama.
Amira ta kira Hassana ta sanar mata Andizo ba lafiya sun asibiti, a ruɗe Hassana ta ce “Inna lillahi! Gamu nan a wani asibiti kuke?”
Kwatance ta yi mata sannan ta kashe kiran.
Suna zaune sai ga su Mamma sun iso asibitin hankali tashe, tambayar Amira Hassana ke yi meye ya samu Andizo ta ce zazzaɓi ne mai ƙarfi..
Ƙofar aka buɗe likitan ya iso gaban su, saurin tashi Sultan ya yi ya ce “Friend me ke damun ta ne bayan zazzaɓin?”
Murmushi ya yi ya ce “Ka, ga ka kwantar da hankalinka iya zazzaɓi ne sai kuma da alama tana yawan yin tunani zuciyarta ta fara kumbura, ya kamata ku kula kar ciwon zuciya ya kama ta. Yanzu mu je na rubuta maka maganin da za take sha amma dai kar ake barin ta tana zurfafa tunani.”
Salati suka ɗauka Ahmad ya yi shuru yana jin maganar likita wani iri, “Zuciyarta ta fara kumbura?” Ya nanata maganar yana bin bayan Sultan, a hanya suka haɗu zai wuce amsar magani da aka rubuta, hannu ya miƙa mishi ya ce “Ba ni takardar ni zan sayo maganin da kuɗi na mun gode ma da ɗawainiyar kawo ta asibiti da kuka yi Allah y bar zumunci.” Ya faɗa yana haɗe rai.
Kallon ban gane ba Sultan ya mishi sai kuma ya ja tsaki ya ce “Kema fa Ahmad mugun ɗan rainin hankali ne, ya ina son na kyautata wa masoyiyata kana ƙoƙarin hana ni matsa ka ba ni guri naje na sayo maganin.” Ya faɗa yana raɓawa gefen shi zai wuce Ahmad ya yi saurin janyo shi ya dawo baya, a kausashe ya ce “Ka ga wasa a idanuna? Yarinyar nan ɗiyar ruƙo ce a wajen mu amana aka ba mu shi ne har kake nema ka faɗa mini maganar banza? Babu wanda ya kamata ya kula da ita fa ce ni da nake a matsayin yayanta na kusa.”
Wani irin kallo Sultan ya mini ya buge hannun Ahmad da ke kan kafadarsa ya wuce fuu, kwafa ya yi ya juya shima ya wuce.
Bayan ya sayo maganin ya koma office ɗin doctor ya miƙa mishi ya amsa suka fito tare, suna isowa ya shige ciki ya ce kar su biyo shi ba su gama ba. Allah-Allah Ahmad yake a ba su damar ganin Andizo ya shiga ya nuna wa Sultan ƙarfin ikon da yake da shi a kan ta, sai ciza lip yake yana jinjina kai gabaɗaya kishi ya rufe mishi ido har ya fara ganin lefin Andizo da ta yarda su Sultan suka kawo ta asibiti, “Wa ya sani ba ko shi ya ɗauko ta a jikinsa da za su saka ta a mota tun da Amira ta ce kasa tafiya ta yi?” Ya faɗa can ƙasan maƙoshi yana jin wani irin ɗaci ya mamaye masa maƙoshi.
Duk abin da yake Sultan na ankare da shi, murmushi ya yi bin shi da kallo.
Bayan ya fito aka ba su damar ganin ta duk suka shiga b kamar Ahmad ma shi ne a gaba-gaba ya ƙwaryar sallah, a zaune suka same ta a rufe ido kamar mai bacci duk suka jeru suna mata sannu. A hankali ta buɗe ido ta ga Ahmad a daf da ita yana mata sannu, kawar da kai ta yi tana amsawa ta juyo ɗayan gefen suka kalli juna ita da Sultan murmushi ta mishi tana kallon Amira da ke kusa da shi tana mata sannu, a hankali ta ce “Na gode sosai ƙawata Allah ya saka da alheri, na gode daddyn Farrah.”
Zama ya yi a kujerar da ke wajen ya ce “Ni fa godiyar nan taki ta fa isheni Khadija, ke ba dama a miki abu sai kin yi ta godiya? Ai in na taimake ki kamar kaina na taimaka tun ke ɗin tawace ni kaɗai.”
Shuru ta yi ba ta ce mishi komai saboda kalaman nasa sun sa ta ji kunya ga kuma su Mamma a wajen duk da tasan ba ji mai ya faɗa ba, Ahmad na jin su ya cika ya yi fam yana jan numfashi da kyar, a fusace ya fita suka bi shi da kallo. Tare suka dawo da likita ya miƙa wa Sultan takarda ya ce “Idan ruwan da aka sa mata ya ƙare za ku iya tafiya gida ga takardar sallama nan.” Ya juya zai tafi Sultan ya miƙe ya ce “To friend my je mu tattauna kafin mu tafi.” Fita suka yi a tare Amira da Mama suka musu sallama suka tafi Hajiya na ta musu godiya, sai da su Mamma suka fito waje ya ga daga shi sai ita ya hayo kan gadon ya zauna a can gefe ya tsare ta da idanu, kawar da kai ta yi ta ce “Kai mutum ba shi da lafiya ma sai ka nuna mishi halin naka?”