← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 75

Sashe 15

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsura masa idanu ta yi tana kallon yadda yake fitar da numfashi yana zuƙa, a hankali ta kai hannu ta taɓa kwantacciyar girar idonsa. Tun da ta farka shima ya tashi amma ya yi shuru kamar bai tashi ba, tana ɗauke hannunta ya buɗe ido suka kalli juna ai kuwa ta juya fuska da sauri tana cewa “Kawai dai birge ni ne ta yi shi ya sa na taɓa.”
Janyo ta ya yi ya mata kiss a goshi, cuno baki ta yi ta soma tirje-tirje ta ce “To ni dai ka daina mini wannan ab..” Ba Ta ƙarasa ba sakamakon bakinta da ta ji cikin nasa, ta zaro ido tana ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa dole ta saki jiki kamar wadda aka zare wa lakka ta yi ɗaiɗai a jikinsa. Haka ya yi ta juya ta son ransa jin yana neman wuce gona da iri ta mirgino daga jikinta ta koma gefe ya biyo ta, da kyar ya iya controle kansa ya sake ta yana mayar da numfashi. Hannu ta sa ta rufe idanu tana shafa bakinta ta hankali ta ce “Ni dai alƙur'an karka cinye mini bakina, wannan ai maita ce mai lasisi.” Ta faɗa tana tashi zaune.
Hannu ya sa ya janyo ta jikinsa ya tsura mata idanu, kumatunta ya shafa ya ce “Khadija wannan ai ba maita ba ce, komai naki nawa ne kar kike bijire mini kin ji.”

“Yo to ni da ba maiya ba ta ya zan yarda da wannan abin, ai ƙazanta ce ma wannan kai ko kunya ba ka ji ma kake tsotse mini baki?”
Dariya ya yi ya tashi da ita a jikinta ya saɓa ta a kafaɗa ya sauko ya nufi banɗaki. Har banɗaki ya kai ta ya ce shi zai tafi masallaci ta yi Sallah ta amsa da to sannan ya fita..

Bayan ta fito ta sa hijabi ta yi raka'atainun fajur, tana zaune tana lazimi ta ji an tayar da iƙama ta miƙe ta gabatar da Sallah.
Bayan ta gama ta yi addu'oi ta shafa ta tashi ta cire hijabin ta faɗa gado saboda barci ba isar ta ya yi ba.

Sai ƙarfe 7:am ya shigo ɗakin ya same ta ta yi ɗaiɗai tana sharar bacci, jallabiyarsa ya cire shima ya kwanta suka ci gaba da barci..

Ba su tashi ba sai ƙarfe goma ya ce su je ya mata wanka ai kuwa ta dinga dariya tana kallon shi, kama hannunta ya yi ya ce “To muje na miki wanka mana rana ta yi.”
Maƙale kafaɗa ta yi ta ce “Tab haka kawai sai na yarda ka mini wanka da girma na da komai? To ni dai alƙur'an ba zan yarda da wannan abin ba sai ka ce wata ƴar is...” Shuru ta yi ta koma ta zauna tana murguda masa baki.

Zama ya yi a gefen ta ya ce “To ai ba haramun ba ne dan na miki wanka, malaminku ba ki ji yana cewa tsakanin mace da miji babu kunya ba? Kuma ba lefe dan sun ga jikin juna?”
Kai ta ɗaga sama alamar tunani, can ta kalle shi sai ta tashi ta ce “To muje.”
Gaba ta yi ya bi bayan ta har banɗakin, da kyar da lallami ta yarda ta cire kayan ya mata wanka fes ya naɗo ta a towel ya kawo ta ya aje ya koma shima ya yi.
Mai ta shafa tana ƙoƙarin yin kwalliyar da ta saba ya hana ta, da kanshi ya dauko fauda ya shafa mata kaɗan ya ce ta sa kwalli, amsa ta yi ta sa ta yi ɗigo ɗaya a goshinta ya ce ya isa haka..
Palo suka fito inda suka samu an kawo musu abinci daga gidan Mamma, janta ya yi suka zauna a ƙasa sai ya tuna kazar jiya ya tashi ya shiga ya ɗauko ya sa a freeze. Yana buɗe kular ya ga soyayyiyar doya ce da kwai sai kayan shayi, ɗayar kular kuma farfesu ne yana tururi. Andizo da son cin nama ta ce ita shi take so, plate ya ɗauko ya zuba mata ya haɗa shayi ya aje a gaban ta ya yi bismillah ya soma ba ta a baki ba muso ta dinga amsa..

Bayan sun gama ya ɗauke kwanukan ta taya shi ɗauke wa suka wanke wanda suka ɓata, kallon juna suka yi ya sakar mata murmushi itama ta mayar masa..
Suna zama ta ce ya kunna mata tv tana son yin kallo, ya kunna ya kawo mata arewa24 suna kan yin shirye-shiryen su ai kuwa ta gyara zama..

Sai da Andizo ta yi kwana huɗu ko nan da ƙofar gida bai barta ta fita ba, ba ta komai sai dai ta sha bacci in ta tashi ya mata wanka ya shirya ta su dawo palo ya kunna mata kallo, idan kuma yan rigimar sun tashi sai ta ce sai ya goya ta ba yadda ya iya haka yake goya ta ya yi ta zagaya palon da ita tana dariya..

Yau suna zaune aka kira shi wajen aiki kiran gaggawa, ganin tana kallo sai ya ce “Baby ki zauna zan je na dawo an kira ni wajen aiki, idan kuma na kaiki wajen Aminatou to tashi na kaiki ko wajen su Mamma.”
Girgiza kai ta yi ta ce “A a sai ka dawo ni ban gama kallo na ba.”
Ficewa ya yi ganin hankalinta gabaɗaya yana kan tv...

“Hello sir na binciko maka gaskiyar magana game da girlfriend ɗin ka, da gaske ne an yi mata aure tana cikin garin nan, amma ba mu san a wani waje take ba sai dai in mun bincika..”

Sultan da ba su jima da tashi daga buga kwallo ba ya yi sharkaf da zufa yana cire safar kafarsa jin maganar ya yi kamar saukar aradu, miƙewa ya yi tsaye ya ce “ What? Anya kuwa ka yi bincike da kyau, ni fa ban kama maganar Farrah ba ka ga ita yarinya ce duk da ta je ta yi kwana biyu a can.”

Girgiza kai Bansh ya yi ya tashi tsaye ya ce “Ba ƙarya ta faɗa maka ba tabbas wajen auren aka kaita.”

“Bansh ina so ka binciko mini ko ɗan gidan waye shi wanda ya aure ta, da auren nawa a kanta za ta bari a aura mata wani auren saboda Mom tana son ganin mutuwa ta? Wallahi in na ga wanda ya aure ta sai na binne shi a ransa, maza ina jiran ka, sati na ba ka ka gama binciko mini duk wani abu da shafe shi.” Ya gama faɗin haka aje wayar sai kaiwa da komowa yake yana ciza yatsa. Sam shi bai ɗauka da gaske Farrah take ba domin har labarin kyau da tsaruwar gidan Andizo take faɗa masa amma ya yi banza da ita, kallon shi Jamil ya yi ya ce “Man what happing?”
Iska mai zafi ya fesar a yadda yake ji ba zai iya tsayawa yin doguwar magana ba, hakan ya sa ya wuce ɗaki duk taku tsaya ji yake ana zage masa lakkar jiki da kyar ya isa ɗaki yana dafe ƙirji. Freezer ya buɗe ya ɗauko kwalbar giya ta yi sanyi sosai ya buɗe ya ɗaga ta sama ya dinga kwankwaɗa, sai da ya kusa shanyewa sannan ya janye yana huci, a hankali ya miƙe yana tangaɗi ya faɗa kan gado sai bacci..

Sanye take da riga da wando ta yi fresh da ita, tana zaune a palo ba ta jima da dawowa daga sashen Mamma saboda can ta wuni kasancewar Salim ya koma bakin aiki. Kwankwasa ƙofar aka yi ta tashi da sauri tana cewa “Da aka jima ba ka zo ba da wajen hajiya babba zan koma.” Ta faɗa tana buɗewa. Ganin waɗanda suke tsaye sai ta matsa gefe tana cewa “Adda kune? To ku shigo.”
Murmushi Aminatou ta sakar mata suka shiga ciki, zama suka yi ta tashi ta kawo musu ruwa da lemo ta zuba musu sannan ta koma ta zauna, Aminatou ta ɗauka ta kurba itama Sabrin ta sha, kallon ko'ina suke na palon can suka ga babban photon Andizo da Salim na ranar dinner su, Sosai suka shagala da kallon shi har sai da Andizo ta soma gaishe da su suka kawar da kai. Sabrin na yatsina fuska ta tashi ta ce “Bari mu je mu ga ɗakin kwanan amarya.” Amiantou ta yi dariya tana gyara zama, ita kuma ta wuce ba ta bari an yi mata izini ba ta nufi ɗakin. Da sauri Andizo ta sha gaban ta tana haɗe fuska ta ce “Ke kuma a su wa da kike son shigar mini ɗakina? Ai sai ki bari ma na miki izini ba ki yi gaban kanki ba kamar gidanki?”

Baki Sabrin ta riƙe ta ce “Kan bala'i! Ke ni kike yi wa gorin gida? Banza ƴar ƙauye kucaka, in ban da ma namiji ga mata a gari nan na faɗi ya je ƙauye ya kwaso wannan jaririyar.”
Andizo ta ji haushi ce mata kucaka da ta yi ta ce “Wallahi ke ce kucaka ba ni ba, na rantse dan kin ci darajar Adda Aminatou da ba dan haka da tuni na haɗa miki jini da majina, ki koma ba za ki shigar mini ɗaki ba..” Ta faɗa tana tura ta baya..
Zaburowa ta yi cike da haushin abin da ta mata ta ɗaga hannu za ta kifa mata mari ta ji an ce “Kika kuskura kika mare ta sai na ga uban da ya daure miki gindin shigowa har gida ki ce za ki ɗaki matar gidan..”

Next fage

_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[5/31, 12:14 AM] 577675904: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_

24
Chapter 15 · 0% Book details