Sashe 44
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Saboda ni ne zan aure ki dole kuma ki bi duk wani umarni da zan ba ki matuƙar kina son ki ji daɗin zama da ni.”
Kallon ba ka da hankali ta mishi tana hura hanci te ce “Allah ya sauwaƙe na aure ka Wallahi, ai ko da kuɗi aka haɗa mini da kujerar Makkah ba zan yarda na haɗa alakar aure da kai ba, da alama sai na dawo maka Andizo ɗin da ka sani tun a Ƙauye kafin mu daidaita da kai, kai a su wa da har kake wani tsaƙewa? To ka fita
sabga ta ban sayo da kai ba daddyn Farrah kuma dole ne na kula shi tun da baban ƙawata ne.”
Tashi ya yi tsaye a fusace ya ce “Haka kika ce?”
Itama a zafafe ta ce “E haka na faɗa.”
Kwafa ya yi zai fita suka ji ana buga ƙofar duk suka kalli wajen. Muryar Hussaina suka jiyo tana faɗin “Anty Khadija Daddyn Farrah ya ce ki zo zai ba ki saƙon da Farrah ta ba shi ya kawo miki.”
Dan ta ba wa Ahmad haushi ta saka mayafi ta nufi ƙofar tana faɗin “Gani nan zan, fita yanzu.” Ta buɗe ta fita suka, wuce da Hussaina.
Har gaban shi ta kai ta ta ce “Yawwa ga ta na kawo ta.”
Godiya ya mata sannan ta juya ta koma, sunkuyar da kai ta yi tana mamakin kiran da ya mata, leda ya miƙa mata yana sa ɗayan hannunsa a aljihu ya ce “Ga shi wannan ce kyauta ta a gareki ta farko Khadija.”
Kallon ƴar ƙaramar akwatin ta yi ja an ɗore jar flower a kai Mai ƙamshi, ɗago kai ta yi tana kallon shi baki sake za ta yi magana ya yi saurin faɗin “Kar ki ce komai please my wife ba a mayar da hannun kyauta baya.”
Karaf maganar a kunnen Ahmad da yake can gefe yana kallon su, ya yi kwafa yana jiran Sultan ya tafi ya bi ta har ɗaki ya ga abin da ya ba ta.
Ganin yadda yake mata magiya dai ta amsa har ta ɗan juyo sai ta ga Ahmad ta yi kuyo tana murmushi ta ce “Na gode da wannan kyautar da ka mini, gaskiya naji daɗi flower na da ƙamshi irin na turaren jikinka.”
Ta faɗa tana kallon Ahmad da wutsiyar ido.
Ƙayataccan murmushi ya sakar mata sannan ya ɗago ya kalli Ahmad ya masa alama da ya zo, fuska daure ya iso yana bin akwatin da kallo hakan ya sa Sultan ya ce “ Ya dai ko ta birge ka ne na sayo maka ka kai wa budurwarka.”
Murmushi ya yi ya ce “Gaskiya ta yi kyau sosai, muje na kaika gida tun da na ga direban naka bai riga da ya zo ba.”
Kallon Andizo ya yi ya ce “Khadija please ki ɗauki Kiran Amira ta dame ni tun jiya har kuka ta yi ta ce na haɗa ta faɗa da ke kina fushi da ita, sannan ki zo gidan su Amira sai na nuna wa Mama ke.”
Duk da ba ta son zuwa amma ganin Ahmad ya sa ta ce “Ai kuwa zan zo sai dai ba ni da waya bare na kira Amira na ce mata zan zo, amma ba komai zan ari ta Hassana sai na sa numéro ta na kira..”
Har zai shiga mota ya fasa jin abin da ta faɗa, “Haba Khadija kamar ke a ce ba ki da waya a hannunki kina babbar yarinya? Gaskiya abin kunya ne dole ki yi waya an jima zan turo Amira ta kawo miki.”
To kawai ta ce ta mishi sallama ta juya ta wuce..
Suna tafiya a hanya Sultan ya ce “Ashe dai nine zan auri Khadija Shi ya sa ta ƙi amincewa da kai.”
Kallon shi kawai Ahmad ya yi yana saƙa da warwara, murmushi ya yi yana gyaɗa kai ya danna wayarsa ya shiga gallery ɗin wayar, photon su Nour ya taɓo ya nuna mishi. “Wannan su ne yaran Khadija jiya aka yaye su.”
Amsa ya yi yana kallon yaran, sosai suka birge shi yana faɗin “wow so beautiful.”
Haka ya dinga kallon su yana yaba kyaun yaran, sai da ya shiga whatsapp ya tura photon yaran ya fi ashirin a kan number shi sannan ya a je masa wayarsa. Shi dai Ahmad bai sake cewa komai ba sai murmushi da yake yana gyaɗa kai.
Ɗakin Aminatou ta shiga ta same ta tana haɗa kaya, da mamaki ta zauna a bakin gado ta ce “Adda ina zuwa haka?”
“Zan koma gida ne zaman ai ya isa haka a gidan surukai, su ba sa so mu bar gidan nan suna so su haɗa mu da wannan ɗan rainin hankalin ni kuma ba zan taɓa yarda na zauna da Ahmad a matsayin miji ba, tun farko ba ma ga maciji da shi dan haka ni gidanmu zan tafi can zan fi sakewa dama ai dan yaransu ne suka hana mu bar gidan, to an ɗauke su in sun dawo a kai mini Khadija gidanmu, idan kuma sun ce su za su riƙe ta zan haƙura na bar musu ita tun da gari ne zan ke zuwa ina ganin ta akai-akai..”
Jinjina kai Andizo ta yi ta ce “Wallahi Adda kamar kin shiga raina, na zauna na yi tunani na ga zaman da muke a gidan nan ba shi da amfani, shekara da wata biyu ai gara mu koma gaban iyayenmu.”
Sai da ta gama haɗa kayan sannan ta zauna a kusa da Andizo ta ruƙo hannunta ta ce “Ko da mun bar gidan nan Khadija kar mu yanke zumunci, sannan muke ziyartar yaranmu.”
“In sha Allahu, nima nan da kwana uku zan, tafi ƙauyenmu sa..”
Kasa ƙarasa maganar ta yi jin kamar ta yi fitsari, da sauri ta miƙe tana riƙe ciki cikin tsananin ciwo ta ce “Waiyo Adda zan mutu cikina da ƙuguna.”
Saurin ruƙo ta Aminatou ta yi tana jero mata sannu, kan gadon ta kalla sai ta kalle ta da sauri ta ce “Khadija dama haka kike fama idan ƙarshen wata ya yi?”
Lumshe ido ta yi ta ce “A a Adda ni ban taɓa yin irin wannan ciwon ba.”
Da mamaki take kallon ta, kama hannunta ta yi ta nufi banɗaki da ita. Ruwa mai ɗumi ta haɗa ta ce “Shiga ki gyara jikinki zan miƙo kaya ki sa.”
Hijabin ta ja ta cire sai ta ga jini a jiki, a rude ta kalli Aminatou Kamar za ta sa kuka ya ce “Kin gani fa wani ciwon ne ya same ni?”
Dariya ta yi ta amshe hijabin ta ce “Wallahi ban taɓa ganin macen da ta haihu ba ta taɓa yin al'ada ba sai ke Khadija, ina jin labarin irin ki na ɗauka ƙarya ce ashe da gaske akwai irin ku? To gyara jikin ba wani ciwo ba ne sai yanzu kika girma.” Ta faɗa tana fita.
Sai lokacin ta ji kunya ta rufe ta ta zauna, ita ta manta da wai mace tana jini duk ƙarshen wata, ajiyar zuciya ta sauke ta tashi tsaye ta gyara jikinta ta fito ta tsaya tana jiran ta kawo mata kayan.
Tana kawo mata kayan ta sa ta fito kanta a ƙasa da sauri ta gudu ta bar ɗakin, dariya Aminatou ta yi tana faɗin “Ki dawo na ba ki abin amfani karki zauna a haka.” Amma taƙi juyowa ta fita..
Sai da ta gama shiryawa ta ɗauki pant ta kai mata har ɗaki suka rungume juna har da kuka, haka ta lallaɓa suka fito tare Mamma na faɗin “Yanzu yaran nan duk tafiya za ku ba za ku zauna ba har ku yi wani auren? To ba komai hakan ma mun gode.”
Sunkuyar da kai Aminatou ta yi ta musu sallama ta ce in an kawo su Khadija a sanar da ita za ta zo ta dauke ta, Mamma ta ce ba matsala za a sanar mata. Har bakin mota suka raka ta suna ɗaga hannu, Andizo ta dawo ta bar su a harabar gidan dan ta gyara jikinta kamar yadda Aminatou ta nuna mata.
A bakin ɗakinta suka ci karo ta matsa gefe ta buɗe ƙofar ta shiga za ta rufe y yi karaf ya shigo kallon shi ta yi a fusace ta ce “Fitar mini a ɗaki Malam ba na son kawo ciwon kai ta kaina nake.”
“Ki fito da wannan ƴar akwatin da Mr J ya ba ki na ga wacce tsiyar ce a ciki.”
Kallon banza ta watsa mishi ta ce “Idan kuma aka ƙi fa?”
“OK bari ki gani.” Ya faɗa yana yo wa kanta gadan-gadan, da sauri ta matsa gefe tana hararar shi, ganin zai taɓa ta ta hankaɗa shi ya faɗa kan gado ta nufi banɗaki da gudu ta datse kofa...
_Maman Nusaiba ce🤙🏻_
[6/25, 8:57 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
39