Sashe 21
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Nana Khadija Maigari dai za ka ce.” Ta faɗa tana gyara zama.
Kanta ya shafa ya ce “Kinga nan dai ba gida ba ne karki sake cewa komai in ba cewa aka yi ki yi magana ba, Maigari ai sunan shugabanci ne asalin sunanshi shi ne Umar, ba ki ga hammanki Umar magajin shi ba ne aka yi masa?”
Baki ta saki tana kallon shi ita sai yau ma ta taɓa jin asalin sunan Maigari, saboda ita a can ƙauye da Khadija Maigari ake kiran ta a makaranta, shuru ta yi saboda ba ta son ɓata masa rai..
Sai da ya gama mata komai sannan aka yi mata tambayoyi ta dinga amsawa, sosai shugaban makarantar ya ji daɗi yadda take ba shi hamsa, hakan ya sa aka kai ta 6ème A (aji ɗaya secondary) har cikin classé ya raka ta, ganin da maza sai ya fito da ita waje ya sunkuya ya ce “Kina ji Khadija, kinga yanzu zan tafi na barki a nan inda baki san ba kowa, ban da neman faɗa ko wani namiji ya miki magana ki kula shi, karki kula kowa musamman maza ke matar aure ce haramun ne ki yi magana da namiji in ba ta kama dole ba, dolen ma sai malaminku idan kina buƙatar wani abu ki je wajen mutumin da na kaiki ya miki tambayoyi zai kira ni sai mu yi waya kin ji, ki dage ki yi karatu sosai zan sayo miki duk abin da kike so..”
Jikinta ne ya yi sanyi ta ɗago da kai idanuwanta sun cika taf da kwalla, girgiza mata kai ya yi ta yi saurin faɗawa jikinsa ta sa kuka, shima rungume ta ya yi ya dinga rarrashin ta har ya samu ta daina kukan sannan ya ɗago da ita ya share mata hawayen yana lallaba ta har sai da ya ga ta yi dariya, babban Monsieur ya tarar da su a haka ya yi murmushi ya ce “Abin da za a yi ranka ya daɗe zan haɗa ta da ƙanwata su zauna a waje ɗaya, duk abin da ba ta gane ba zan sa take nuna mata..”
Sosai Salim ya ji daɗi ya masa godiya sannan ya ciro kuɗi ya miƙa mata ya ce in an fito da su shan iska ta sayi abinci kar ta zauna da yunwa, to ta ce tana ɗaga mishi hannu har ya bar wajen sannan ta bi bayan Monsieur suka shiga ciki.
Gabaɗaya ɗalibai suka tashi suka gaishe shi ya amsa, table na farko ya kalli wata yarinya ya ce “Ke tashi ki koma baya Khadija ta zauna a gaba saboda kin fi ta tsayo..”
Kallon Andizo yarinyar ta yi fuska a damke ta tashi ta koma baya ita kuma ya ce ta zauna, zama ta yi ta kalli ɗayar ta mata murmushi itama ta mayar mata, matsowa kusa da su ya yi ya ce “Amira ga ƙawa na kawo miki, ki riƙe ta da kyau karki bari kowa ya takura mata saboda tana da kima a wajena. Ina dai ba ki manta Salim soja ba ko?”
Gyaɗa masa kai Amira ta yi tana murmushi, ya ce “To matarsa ce ki kula karki kuskura wani namiji ya mata magana.”
Zaro ido ta yi tana kallon Andizo sosai mamaki ya kama ta wai wannan yarinyar ce aka yi wa aure? Dafa ta Amira ta yi ta ce “Khadija daga yanzu ni ƙawarki ce za mu ke yin komai tare kin ji.”
Kai ta gyaɗa mata tana wasa da kudin da Salim ya ba ta, kallon kuɗin Amira ta yi ta ce “To ki sa kuɗin a jakarki mana karki yada.”
To ta ce ta sa kuɗin sannan duk suka mayar da hankali a kan darasi da aak fara musu...
Bayan an tashe su shan iska suka fito a tare 'yan ajinsu sai kallon ta suke, ita kuwa duk jin ta take a takure duk yadda take da sakin jiki da wuri in ta je baƙon guri yau dai ta kasa sai ɗari-ɗari take da kowa, abincin Amira ta saya musu suka zauna amma ta kasa cin na kirki, saboda ta saba Salim ya ɓata ta ba ya bari ta ci abinci da kanta shi yake ba ta a baki har ta ƙoshi. Wasu zafafan hawaye suka zubo mata ta yi saurin gogewa tana kawar da kai da kar Amira ta gani, amma ina tuni ta gani ta dafa kafaɗarta ta ce “Khadija ki daina kuka kin ji, kinga Yayana ya ce na kula da ke kar na bari ki yi kuka, ki faɗa mini me kike so zan miki?..”
Da kyar ta danne kukan da ya zo mata ta haɗiye yawu sannan ta samu damar yin magana, “Ban saba cin abinci ni kaɗai ba, shi yake cinyar da ni ga shi yanzu ba ya tare da ni.” Ta faɗa tana sakin kuka..
Dariya ce ta kama Amira amma ta daure ta ce “Ke Wallahi Khadija lamarin ki ba sauƙi, yanzu saboda haka ne kike kuka? Anya za ki iya zuwa wani garin ki yi sati ba tare da Yaya Salim ba? To bari ni na wakilce shi gyara zama na ciyar da ke kar ya zo ɗaukan ki ya ce an bar masa mata da yunwa..”
Girgiza kai ta yi ta ce “A'a zan ci da kaina ai.”
Amira ta janye abincin gaban ta ta ce “Ban yarda ba da wannan maganar, ki tsaya na ba ki kar a koma..”
Dariya abin ya ba ta sai ta gyara zama Amira ta dinga diba da cokali tana ba ta tana ci, sai da ta ƙoshi sannan ta ce ta ƙoshi Amira ta yi hamdala ta miƙa mata ruwa ta sha ta wanke baki sannan suka koma ciki..
Ana tashi aka zo ɗaukan Amira ita kuma Andizo Salim bai zo ba, kallon ta yi ta ce “To yanzu ya za a yi Khadija? Ko za ki bini mu tafi gidanmu ne idan mun je sai Yaya ya kira shi ya zo ya ɗauke ki?”
Shuru ta yi tana kallon gefe ta gaji sosai saboda yau darasin ya mata tsauri dayawa, sai da Amira ta sake yin magana sannan ta sauke jakarta ta ce “Da dai shi direban naku zai kaini gida sai in shiga.”
Ɓata rai Amira ta yi ta ce “Kenan gidan namu ne ba za ki je?”
Saurin girgiza kai ta yi ta ce “Ba haka ba ne bacci nake ji duk na gaji.”
Za ta sake magana sai ganin mota suka yi ta paka a gaban su, da kallo suka bi motar har ya buɗe ya fito. Da sauri ta tashi tana murmushi ta ce “Amira ga Yaya Ahmad ma ya zo ɗauka na ba sai na bi ki ba.”
Kallon shi Amira take tana yaba kyau da zubin halittar shi, ga shi ya ɗau wanka sai ƙamshi yake tashi a jikinsa. Yana isowa ya musu sallama suka amsa ya kalli Andizo ya ce “Matar yaya na zo ɗaukan ki, aiki ma nake aka ce sai na zo na ɗauke ki yanzu haka kina nan kina kuka ba a zo an, ɗauke ki ba.”
Dariya ta yi ta miƙa masa jakar makarantar ta ce “Da ba ka zo yanzu ba da ƙawata Amira zan bi mu tafi gidansu.”
“Ayya ya kike Amira?”
Ya faɗa yana kallon ta.”
Sunkuyar da kai ta yi ta ce “Alhamdu Lillah ya aiki?”
Lafiya lau ya ce suka mata sallama suka tafi itama ta shiga mota suka direba ya ja suka tafi..
Ko da ta zo gidan sai ta ga wata mota da ba ta saba gani a gidan ba, kallon Ahmad ta yi ta ce “Yaya Ahmad ko baƙi aka yi a gidan?”
Sai da ya fito daga motar sannan ya ce “Mamar Aminatou ce da 'yan'uwanta suka zo..”
To kawai ta ce sannan ta wuce ɓangaren ta, tana isa ta kai jakar ɗaki ta aje ta fito palo, sosai ta yi mamakin ganin yadda aka hargitsa mata palon kamar yau ba ta gyara shi ba, cike da gajiya ta dinga gyara palon tana yi tana hutawa har ta gama, banɗakin palon ta shiga nan ma ta samu duk an yi fitsari a ƙasa sabulun wanke hannu a zubar da shi gabaɗaya a ƙasa, towel ɗin da suke goge fuska in sun wanke suma duka an yado su cikin fitsarin, mamaki sosai ya kama Andizo sai tambayar kanta take yaushe aka shigo mata palo har aka mata wannan ta'asar? Facemark ta ɗauko ta sa ta saka safar hannu ta shiga wanke banɗakin tana yi tana kakarin amai saboda tsamin kashin da banɗaki yake yi, bayan ta gama ta zuba abin ƙamshi mai yawa ta kwara a ƙasa ta zuba a ko'ina ta janye ruwan sannan ta ji banɗakin ya dawo yadda yake.
A matuƙar gajiye ta fito duk ta haɗa zufa, duk son ta da kallo yau ji ta yi ya ishe ta ta nufi ɗaki, har za ta kifta kamar an ce ta kalli ɗakin baƙi ta ga an kunna hasken ɗakin, da mamaki ta nufi ɗakin tana karanto addu'a. Zaro ido ta yi ganin kujerunta gabaɗaya an hargiza su har carpet ɗin duk an yuye shi, rasa abin da za ta yi ta yi kawai ta fashe da kuka tana kallon ɗakin, sai da ta yi mai isar ta sannan ta shiga ta dinga gyara kujerun tana nishi saboda sun mata nauyi, da kyar ta gyara ta fito lokacin har an kira sallar la'asar, ɗakinta ta nufa ta wuce ta shige wanka. Bayan ta fito ta yi Sallah sannan ta shiga ta kunna gawayi, sosai yau take jin haushin yadda ta samu gidan nata a hargitse bayan sai da ta gyara ta yi masa turaren wuta sannan ta tafi makaranta. Turaren wuta ta kunna ta ɗauko 'ya'yan habbatussauta da Hajiya Babba ta ce da ta ga marece ya yi take turare gidan da shi saboda lafiyarta, har gyara gida sai da ta koya mata ita da Mamma domin sun ce mata in ba ta iya gyara gida da girki ba Salim zai daina sonta, hakan ya sa ta dage ta koyi komai ƙarfi da yaji har girki Mamma ta fara koya mata amma dai ba ta iya ba dafa indomie kaɗai ta iya..