Sashe 54
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun daga wannan lokacin Ahmad ya daina yi wa Andizo mugun ta sai nuna mata kulawa da soyayya, ita kuma ganin ya daina mata duk wani nau'in cuta sai ta saki jiki da shi suke wasa suna dariya da shi ya kaita makaranta idan sun tashi ya je ya dawo da ita gida, har wani sabon yawo ya tsiro musu da zarar maraice ya yi rana ta yi sanyi zai ɗauke ta su fita sha ice cream ya kai ta wuraren shaƙatawa sai sun kai wajen ƙarfe tara na dare sannan su dawo, su kansu su Hajiya abin ya birge su ganin mafaɗatan sun shirya kansu.
Yau bayan sun taso daga makaranta ita da Amira suna da Sadiya da Arma, tsayawa suka yi dingin wata bishiya suka samu waje suka zauna. Arma da ya gaji ya tashi ya musu sallama ya tafi itama Sadiya ta tafi ya rage saura su biyu, kallon Amira ta yi ta ce “Amira ina so na sanar miki an sa bikinmu nan da wata biyu ni da Yaya Ahmad.”
Da sauri Amira ta zabura tana kallon Andizo ta ce “Ban gane an sa ranar bikinku ke da Ahmad ba Khadija? Da don Allah va na son irin wannan wasan in ma da wasa kike ki fasa please ba na so.”
Da mamaki Andizo take kallon ta ta ce “Wallahi da gaske nake miki yanzu haka ma an yi kwana biyar a cikin wata biyun, da a yi hutu za tafi gida.”
Gyara zama Amira ta yi tana hura hanci kamar za ta kai wa Andizo duka ta ce “Amma dai kin san ba ki yi wa Uncle adalci ba ko? Duk wani motsin shi Khadija ko wani abu ya gani na mata zai ce wannan zai miki kyau ya saya ya aje ya ce in kin zo gidansa zai miki surprise, ashe ke kina can wancan mai ciccin maganin ya hure miki kunne, yanzu da wani ido zan kalle shi na ce masa an sa miki rana? Ki faɗa mini Khadija me kike so na ce masa idan ya tambaye ni mun haɗu da ke a ècole?” Ta faɗa rai ɓace, Andizo ta kafe ta da ido tana mamakin yadda ta fusata a kan ɗan giya, girgiza kai ta yi ta ce “To ke wa ya ce miki dama ina son Uncle ɗin ki? Tun farko dama na faɗa masa ni ba zan auri ɗan shaye-shaye ba manemin mata, amma sai ya mini ƙarya ya ce wai yanzu ya na yin duk wani aikin masha'a kayan mayen ma duk ya rage sha a hankali zai fasa ashe duk ba da gaske ba ne?”
Wai irin kallo Amira ta jefa mata ta ce “Wallahi kin ba ni mamaki Khadija, ba ki san waye Uncle ba ne shi ya sa har kika ƙaryata maganarsa, idan da bai fasa aikata duk waɗannan abubuwan ba Wallahi ko kashe shi za ki ba zai miki ƙarya ba, Uncle mutum ne mai magana ɗaya idan har ya ce eh to haka ne idan kuma ya ce a'a to ba haka ba ne. Tsohuwar magana ce wannan ni kaina shaida ce Uncle ya kimtsu zama na da shi a London da lokacin Sallah ya yi sai ya je ya bi jam'i, ya daina komai duk saboda da ke Khadija. Da farko da ban san ke ba ce na jinjina wa Khadijar da ta yi sanadiyar shiryuwar Uncle ɗina bayan na so na gane ke ce farin cikin da na yi ya fi na baya, ina son na ga ranar aurenku domin ki ƙarasa ladan ki a gaban idona abokansa yan bal in suka zo duba ni a gidansa za su zo da giya amma sai ya ce musu shi Khadija ta hana shi shan komai ta ce cutar da lafiyarsa suke ba zai sake sha ba, su kansu sun sha mamaki matuƙa lokaci ɗaya da ya daina biye musu a kan mace har sukan ce mishi ya kamata ya maza ya auro Khadija ko sun zo sun ga wannan mai sa'ar da ta sace zuciyar Mr J, Idan suka faɗi haka har kyauta yake musu tare da tabbatar musu lalle zai kawo Khadija a matsayin matarsa su ganta su kansu sai sun yaba da zaɓin zuciyarsa, ashe ke kina can ki watsar da shi har an sa miki rana da ƙanen mijin ki. Allah ya sanya alkhairi ya ba ku zaman lafiya amma ki sani ba zan je wajen aurenki ba kar ma ki sa ran za je Uncle ɗina nake tayawa kishi.” Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta wuce fuu. Da sauri Andizo ta tashi har tana haɗawa da gudu ta isko Amira ta janyo hannunta ta yo baya, suna haɗa ido ta fashe da kuka ta faɗa jikinta tare da cewa “Don Allah Amira ki yi haƙuri karki ga lefina a wannan lamarin, Wallahi ko ni kaina zuciyata ta kasa aminta da auren Yaya Ahmad kawai dai na amince ne saboda iyayensa, sun mini halicci kuma suna son su ga auren nan saboda ba sa son na bar gidansu, ni kansu su Maigari tun farkon maganar Maigari ya ce a ɗaura a rabu da ni idan na nutse zan gane gata Salim yake nema mini sai Abba ya ce sam ba zai yi ba a tauye mini haƙƙi a ba ni wanda ba na so, a bari idan har Allah ya sa akwai aure a tsakanin mu za mu fahimci juna gaba, ni kuma ganin yadda kowanni suke son haɗin sai na dangana domin farin cikinsu musamman Maigari..”
Ɗago da ita Amira ta yi ta ce “Yanzu kina nufin ba son Ahmad kike ba kawai dan farin cikin su Maigari za ki yi?”
Gyaɗa mata kai ta yi tana share hawaye ta ce “Kuma ba na son a ce na rayu a inda babu su Nour ba, ina son na riƙe yarana su girma a tare da ni.”
Hararar ta Amira ta yi ta kai mata bugun wasa ta ce “Ke dai ga babban dalili masifar son yaranki da kike ne ya sa kika amince da auren wanda ba kya so.”
Dariya mai haɗi da hawaye ta yi ta ce “Ke dai ki tayani da addu'a Allah ya sa na iya yi masa biyayya.”
“To shi kenan Allah ya ba ki ikon yi masa biyayya, amma dai ni ba zan iya cewa Uncle an sa miki aure ba sai dai ke za ki faɗa mishi idan ya kira ki, dan haka ni kinga tafiya ta sai mun yi waya.”
Da haka suka, yi sallama Andizo na bai wa Amira haƙuri har ta shiga mota ita kuma ta koma gefe tana jiran zuwan Ahmad.
Ba ta jima da tsayuwa ba sai ga shi ya iso, da kallo ta bi motar har ya fito ya iso inda take tsaye ya haɗe hannu biyu yana marairaiwa ya ce “Ina mai ba da haƙuri a kan abin da na yi, nasan na barki kina jira a mini afuwa matata.”
Harara ta banka mishi ta jefa mishi jakar makarantar ta wuce ta shiga mota, murmushi ya yi ya bi ta da sauri ya shiga suka tafi. Tun a hanya ya ga ta yi shuru tana kallon gefen hanya ba magana irin yadda suka saba, jikinsa ne ya yi sanyi ya kai hannu ya shafo fuskarta cikin sassanyar murya ya ce “Khadija ya dai? Ko ba ki da lafiya ne?”
Lumshe ido ta yi ta juyo ta ce “Yaya zazzaɓi nake ji.”
Da sauri ya ce “Subhanallahi tun yaushe ya same ki ba ki kira ni kin sanar da ni ba?”
Ƙasa ta yi da kai ta ce “Ɗazu ne da muka fito fa in naje gida zan sha magani.”
“A'a ba na son wasa da lafiya muje asibiti a duba ki.”
Ƙi ta yi ya yi juyin duniyar nan amma sam ta ce ba za ta je asibiti ba dole ya haƙura ya rabu da ita.
Bayan sun je gida ta yi wanka ta ci abinci ta shige ɗaki ta kulle dan kar ma ya zo ya dame ta da hira ita kuma yau ba ta jin yin magana.
Kwanciya ta yi ta lulluɓa har baccin ta ya fara nisa ta farka a firgice, dafe kanta ta yi tana karanto addu'ar mummunan mafarki cikin wani kalar yanayi irin na masu rashin lafiya
_*“آعوذ با كلمات الله المامات من غضبه و عقابه و شر عباده، و من همزات الشياطين و أن يحضرون*_“
Shuru ta yi bayan ta gama addu'a tana mayar da numfashi, ƙarshe dai ta tashi ta canja kaya dalilin kiran da Ahmad yake mata a waya yana so su fita waje, a harabar gidan ta same shi ya dinga tsokanar ta ita kuma ta yaƙe dan kar ya gane tana cikin damuwa haka dai suka tafi.
Wajen wani sabon cin abinci ya kaita wanda bai fi sati da buɗewa ba, sosai wajen ya ɗebe mata kewa ta ɗan saki jiki suka dinga hira yana nuna mata kalar atamfofi da shaddojin da za a kai mata lefi ta zaɓi kalar da take so, haka dai ta zaɓa wani kuma sai ta ce shi ya zaɓa sai ya nuna ya aje ta. Suna dawowa da gida da kyar ta isa ɗaki ƙafafuwanta sun yi sanyi sosai sai da Ahmad ya ɗauke ta ya kwantar jikinta sai rawa yake. Ganin abin na ƙasuwa hankalinsa ya tashi fita ya kira Hajiya Babba ta zo ta ce su tafi asibiti. Ko da suka je allura kawai suka mata ta maleriya suka dawo gida, da kyar ta samu bacci.