Sashe 39
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murmushi Ahmad ya yi ya ce “Allah sarki aboki wai ni ko sai yaushe za ka yi aure ne? Zan fa zuga Mama ta taso ka a gaba ko kuma na samo maka wata a nan garinmu, yanzu dai a ƙalla ka kai kusan 40 years kana zaune ka zama tuzuru ƙarfi da yaji, kai duk matan duniyar nan ka kasa samun mace ɗaya da ka ji kana so a zuciyarka? Kuma nasan ba wai masu sonka ba ne ka rasa kaine dai kaƙi yarda ka aura.”
Tsaki Mr J ya yi ya ce “Kai fa ɗan iska ne wani lokacin Ahmad, so kake ka ɓallo mini ruwa kenan? To ka kwantar da hankalinka in sha Allah ba zan sake yin shekara cikakkiya ba zan yi aure, ba na taɓa ba ka lamarin wata kyakkyawar budurwata ba?”
“Kwarai kuwa an yi haka.” Cewar Ahmad.
“To ita ce take ba ni ciwon kai, ka bari sauran labarin sai na zo zan maka bayanin komai.”
“To Allah ya nuna mana lokacin aboki, ni kaina yau na shiga wata matsananciyar damuwa mai girma, amma ka bari in ka iso sai mu tattauna ko za mu samu mafita daga ni har kai.”
Sallama suka yi Ahmad ta girgiza kai ya tashi ya shige banɗaki..
BAYAN SHEKARA ƊAYA
Su Nour sun yi wayo suna gudun su ko'ina Mamma ta ce za ta yaye su amma Andizo ta hana, ta ce sai sun kai lokacin da kowanni yaro yake kaiwa kafin a yaye shi dole ta rabu da ita.
Sanye take da riga da sket na atamfa kayan sun zauna a jikinta, idan ka ganta ba za ka taɓa cewa ta san meye rayuwar aure ballantana a kai ga haihuwa, ta ƙara tsayi da jiki ga wani kyau na musamman da ta yi fatarta sai sheƙi take, duk wata cikar halitta da ake nema a jikin mace Andizo ta same ta ma sha Allah, ita kanta ta san yanzu take cikakkaiyar mace saɓanin baya da take kwaila. Aiman ne a kafaɗarta sai jijjiga shi take saboda rigimar da yake mata, ganin Aminatou a zaune sai ta iso ta saka mata shi tana kumbura baki ta ce “Wallahi Adda wannan ɗan naki ya cika rigima, tin safe nake fama da shi kamar na sabga mishi mari nake ji, ga Nour can ta yi luf abin ta amma shi ban da saka ni zarya babu abin da yake.”
Dariya Aminatou ta yi ta saɓa shi a kafaɗa ta soma jijjiga shi ai kuwa ya yi shuru yana sauka ajiyar zuciya, kallon juna suka yi ta riƙe baki ta ce “Ka ji yaro ɗan nema.”
“Ki ba shi abincinsa kafin ki tafi, ni da kin yarda ma sai a samo mai raino take bin ki ècole ɗin idan sun kuka sai ki fito ki kula da su, dama kuma Aiman ne ya fi kowa rigima a cikin su.”
Zama ta yi tana turo baki ta amshe shi tana faɗin “Kai Wallahi ba zan tafi da su ba, haka kawai su addabe ni su hana ni karatu musamman shi wannan mai kama da wancan ɗan wiwi ɗin.”
Ta faɗa tana dungure kan Aiman ai kuwa ya sa kuka.
“Kai Khadija wannan dai cuta ce ya za kike masa rankwashi a ka kamar wani babba? Ki ba shi ya sha zan goya shi.”
Bayan ta gama ta tashi tana gyara rigarta ta saka mayafin da ta fito da shi, kallon ta Aminatou ta yi ta ce “To a dawo lafiya nima na kusa komawa ai.”
Amin ya ce ta goya jakarta ta sa kai ta wuce, a bakin ƙofar fita suka ci karo da shi ya zo shigowa, riƙe kai ta yi ta ce “Kai kai kai!”
Saurin kallon ta ya yi ya ce “Yi haƙuri dama ke na zo kira ai, mu je na kaiki kar na makara wajen aiki.”
Harara ta banka mishi ta wuce gaba fuu tana turo baki, gani take duk dan a takura wa rayuwarta ne Mamma ta ce shi zai ke kaita makaranta, tsaki ta ja ta tsaya tana jiran ya iso ya buɗe mata ƙofa.
Kallon ta ya yi ya girgiza kai, ya san haka take yi wa Salim dole shi ne zai buɗe mata mota in dai za su fita, a hankali ya buɗe ya ce “Bismillah matar yaya.”
Baya ta kama ta buɗe za ta shiga ya yi saurin rufewa ya ce “Na rantse da Allah in kika shiga baya sai dai yau ki fasa zuwa ècole ɗin, dan kin raina mini hankali direbanki kika ɗauke ni da za ki shiga baya?”
Baki ta murguda tana hura hanci ta ce “To ai dama ban ce ka kaini ba malam, ai kasan ina da direban da mijina ya ɗauka mini yake kaini, idan kuma ba ya komai shi yake ɗauko ni ko ka taɓa ɗauko ni daga makarantar in ba sau ɗaya ba? Ni ba na son wannan baƙin halin naka..”
Ran Ahmad ne ya ɓaci amma ya danne saboda da kashedin da Hajiya Babba ta mishi, da hannu ya nuna mata gaba ta ja tsaki ta buɗe baya ta shiga. Zagayawa ya yi ya shiga ransa a matuƙar ɓace ji yake kamar ya yi ta zabga mata mari saboda sabon rainin da ya shiga tsakaninsu.
Yana kaita ya ciro 1000F (dala ɗari) ya miƙa mata yana wani shan ƙamshi ya ce “Mamma ta ce a ba ki saboda sayan abinci kafin ku taso.”
Da har ta kalle shi a wulaƙance jin Mamma ce ta ba da ba ta sai ta amsa ta wuce da sauri ya bi bayanta da kallo.
Tana shiga suka gaisa da 'yan ajinsu, sai da ta jima a zaune tana tunanin rashin zuwan ƙawarta Amira.
Dafa ta ta ji an yi ta yi sauri juyowa suka haɗa ido da wata matashiyar budurwa, murmushi ta sakar mata ta ce “Yane Sadiya da dama?”
Tashi ta yi ta dawo kusa da ita ta zauna ta kalle ta sannan ta ce “Lahiya lau Wallahi ya gida? Ina su Aiman ?”
Kwafa ta yi ta ce “Cewa za ki yi ina sarkin rigima, ai yana can ya gama kuka na samu ya yi bacci sannan na fito.”
Dariya ta yi ta ce “Khadija ina jinjina miki matuƙa Allah ya ba ki ƙoƙari da juriya, kalle ki fa yarinya ƙarama amma kina da yara biyu ga ɗiyar abokiyar zaman ki ta uku, Allah dai ya raya miki su.”
Itama dariyar ta yi ta ce “Amin Sadiya na gode da addu'ar da kika yi wa yarana, amma ban da abin ki wa yake ja da ikon Allah? Ai ko ke aka yi wa aure a shekaruna za ki iya duk abin nake wanda kike ganin kamar na yi ƙarama na yi su.”
“Tab! Alƙur'an ba za iya rainon yara biyu ba, ke ni fa ko ɗaya ne sai na samo mai raino tana tayani.” Cewar Sadiya tana ƙifƙifta idanu.
Dariya Andizo ta yi ta gyara zama hango malaminsu ya nufi aji, hakan ya sa itama Sadiya ta gyara zama..
Bayan sun taso suka fito a tare suna tafiya sai ga wannan saurayin mai suna Arma da yake damun ta ya tare su, kallon shi ta yi cike da mamaki ganin yadda ya ƙara girma ko dan ta jima ba ta ganshi ba ta ga ya yi saurin girma.
Murmushi ya yi ya ce “Nana Khadija Maman Aiman da Nour barka da dawowa, ya kuma haƙuri Allah ya jiƙan mijinki ya raya ɗiyanku, lokacin da aka yi rashin mun je har sau biyu amma ba mu samu damar ganin ki ba.”
Sunkuyar da kai ta yi ta ce “Amin ya Rabbi na gode sosai.”
Gyara tsayuwa ya yi ya ce “Ba komai dama na zo ne in ba ki haƙuri a kan abin da na miki a baya na bibiyar ki da nake, Wallahi ban ɗauka da gaske ke matar ba ce sai da Monsieur ya sanar da mu Allah ya yi wa mijinki rasuwa, ashe ma nasan mijin naki sosai. Amma don Allah yanzu zan iya zama ami ɗinki sai muke karatu tare har Sadiya da Amira?” Ya faɗa yana haɗe hannu biyu alamar roƙo.
Kallon Sadiya Andizo ta yi ta gyada mata kai, juyowa ta yi ta ce “To ba matsala amma wai ina Amira ta shiga ne? Tun da na dawo ban taɓa gani ta zo ècole ba ko lafiya? Kuma ina kiran layinta sai a ce mini a kashe, ga shi ba ni da spécial numéro ɗin ta ta so ta ba ni lokacin da na yi zuwan ƙarshe ècole, to sai aka zo ɗauka n doek na haƙura na tafi.”
“Amira ba ta jin daɗi ne rashin lafiya ta yi, ai ta jima rabon ta da ècole yanzu haka ni zuwa gobe nake so naje har gidansu na duba ta in kina son zuwa ki zo mu je.”
Fuskar tausayi ta yi ta ce “Ayya Allah sarki ƙawata, to shi kenan goben sai mu tafi ko kana da sabuwar numéro ɗin ta?”
“To Allah ya kaimu ki ba ni number ki idan isa gida zan tura miki whatsapp, goben in shan Allah in na fito sai na kira ki mu haɗu kin san ni yanzu na bar ajinku.”
Numéro ta ba shi ya mata godiya sannan ya wuce..
Tun da suka tsaya Ahmad ya iso yana kallon su cike da takaici, kallon saurayin ya yi har ya shige mota yana yin kwafa. Sallama kawai ta mishi ta shiga ya amsa ciki-ciki ya ha motar suka tafi..
Washegari bayan sun taso daga makaranta ta fito bakin get tana jiran shi ya fito, har ta gaji ta samu waje ta zauna tana jira sai ga jira ya shigo wayarta ta duba ta ga sabuwar number ce, ɗauka ta yi tare da yin sallama ya amsa sannan ya ce “Ina mai baki haƙuri Khadija gani nan zuwa yau mun sha karatu ne ba sauƙi.”