Sashe 3
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tashi ya yi ya zauna a kasan carpet ya kalle ta, murmushi ya sakar mata tare da miƙa mata hannu ya ce “come here my wife.”
Kallon shi kawai take sai kuma ta sauko ta tsaya a naisa da shi ta ce “To alƙur'an in ka kuskura ka zage ni tsaf zan rama kar ka ga dan ina ƙarƙashin ka.”
Lumshe idanu ya yi yana jin muryarta kamar ana masa busar sarewa, ta kurame ya dinga mata alamar ta zo ga abinci ya samu ta zo ta zauna.
Ruwa ya zuba mata a cikin wata ƙaramar roba da aka tanada dan wanke hannu ta wanke, abincin ya buɗe dambun kuskus ne ya sha kayan ƙamshi ya sa cokali ya ɗiba ya nufi bakinta da shi, da sauri ta ja da baya tana ɓata rai ta ce “An faɗa maka ni jaririya ce da zan tsaya ƙato kamar kai kana ba ni abinci a baki?”
Tashi ya yi ya ɗauko wani ɗan ƙaramin kwali ya dawo ya zauna, “My wife ki tsaya in ciyar da ke abincin nan za ki fi ci da yawa.” Ya faɗa yana ƙara kai mata baki ta kauce tana murguda masa baki..
“Kai ni fa ba ƙaramin aikina ba ne in maka ɓalle-ɓalle a mazaunai da reza sabuwa fil.”
Dariya ta ba shi amma ya gyumtse ya shammace ta ya kamo hananyenta duka biyun, da hanzari ya fito da gam din da ya ɗauko ya manne mata hannayen da shi da kyau , ta juya ta kasa raba hannun ai kuwa ta fasa ihu ta fashe da kuka tana faɗin “Allah ya t..”
Next Fage
_Maman Nusaiba ce_
[5/23, 7:39 PM] Ummu Amjad: *Arewabooks@saratalkasum88*
_LITTAFIN ANDIZO NA KUƊI NE N300 KU TURO KUƊIN KU TA WANNAN ACCOUNT ƊIN._
_Account number 0003187186_
_Name account, khadija Salisu_
_Name Bank, Ja'iz Bank_
_Sai a yi screen shot a turo ta wannan number_
_🥏+966577675904_
Shafi 17
Kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon abincin da ya zuba mata a baki, furzar da dambun ta yi har da haɗawa da kakarin amai ai kuwa ya wuce mata ta kwaru. Tari ta dinga yi ga shi ba damar ta tashi, shi ko yana zaune yana kallon ta ko motsi bai yi bare ya taimaka mata, idanuwan Andizo suka yi jajur tana nishi kamar kadangaruwa ta ce “Ru. Ruwa zan sha.”
Murmushin mugunta ya yi ya ɗauki ruwan a riƙe, kallon shi ta yi a galabaice ta yi abin tausayi, gyara zama ya yi ya ce “In dai har kina son shan ruwan nan sai kin amince da abin da na zo miki da shi.”
Ba tare da tunanin komai ba ta ce “Na amince in dai za ka ba ni ruwan.”
Gyaɗa kai ya yi ya miƙa mata ruwan sai kuma ya janye yana dariya, ganin da gaske makasar ta yake nema ta yi kukan kura ta yi facali da farantin abincin ta kurma ihu ta yo kanshi, da ƙafa ya dinga kai masa duka tana faɗin “Dama ai so kake ka kashe ni shi ya sa ka rabo ni da dangina, to alƙur'an kafin ka kashe ni sai na gajiyar da kai ko mu mutu tare.”
Ko motsi bai yi ba yana jin ta ta gama dukan shi iya son ranta ta nufi hanyar banɗaki fuu, da sauri ta shigi banɗaki ta yi dabara da kyar ta kunna kan fomfo. Sai da sha ta ƙoshi sannan ta ɗago tana mayar da numfashi, kallon ko'ina take tana mamakin wai a ce duk kyan wajen nan banɗaki ne, jikin bangon ta shafa ganin yadda yake da sulɓi abin ya birge ta, bakin bahon wanka ta ƙaraso ta tsaya.
“Shi wannan ɗin ko me ake yi a cikin shi? Inda bari na taɓa naji ko yana da kyan jikin bango.” Ta faɗa tana durkusawa ta taɓa a hankali ta ji shima sulɓi gareshi, ai kuwa ta sa ƙafarta a ciki sai ta kusa aje wa sai ta cire ta yi dariya ta ce “Kut na je na saka a lula mini da ƙafata..” Sai da ta yi haka ya fi sau biyar sannan ta saka ƙafar ciki, jin babu komai ta kuma saka ɗayar ai kuwa ta kama murna tana juyi a ciki. Kan fomfo ta kalla da ya yi sama ya lankwaso ƙasa, baki ta riƙe ta ce “Tab ji kamar maciji.”
Haƙori ta sa ta dinga cirar gam ɗin da ya ɗaure mata hannu har ta cira shi, kallon hannun ta yi ta ce “Wallahi sai na ɗauki fansa ko min daren daɗewa, duk abin da ka mini bashi kake ɗauka da ni kake zancan..”
Wani waje ta matsa ai kuwa sai ji ta yi shaa ruwa ya shiga yi mata feshi, ƙara ta fasa ta yi sufa sai ga ta bakin banɗakin tana zare ido, ruwan ya ci gaba da zuba tana tsaye tana kallo. Ganin dai ruwan ba zai daina zuba ba ta matso cikin sanɗa kamar mai son kama wani abu, riƙe ƙugu ta yi da hannu ɗaya dayan hannun ta miƙa ta taro ruwa ai kuwa ta ji ya fi na farko sanyi, dariya ta yi ta miƙa duka hannun ta dinga tarar ruwan tana wanke fuska cike da nishaɗi..
Sai da ta jiƙa kayanta har suna ɗigar ruwa tukun ta janye hannu tana son ta kulle amma ba ta san wajen ba, ganin ba zai tsaya ba ta nufi kofar fita ta kama za ta buɗe ta ji kam ta kulle..
Tsoro ne ya kama ta ta ci gaba da girgiza ƙofar tana faɗin “Kai dan giya zo ka buɗe ni mana.”
Duk abin da take yi yana kallon ta cctv da ke cikin banɗakin, ganin ta fara kuka sai ya tashi ya zo ya buɗe mata. Da gudu ta fito sai ji ta yi ta afka kan mutum. Da sauri ta yunƙura za ta tashi ya yi saurin riko ta ta koma, kawar kai ta yi tana hura hanci ta ce “Malam dallah can ni sake ni na tashi.”
Ƙin sakin ta ya yi sai ma juyawa da ya yi ya kwantar da ita suna fuskantar juna, jin ya matse ta sai ta daina mutsu-mutsu ta yi shuru tare da ƙura wa beauty face ɗin sa ido, shima kallon ta yake yana sakar mata kyakkyawan murmushi. Sosai ta shagala ta kallon shi tana yaba kyan shi a zuciyarta har ba ta san ba san da ta ce “Ashe 'yan iska ma suna da kyau kamar mai hankali?”
Kunnenta ya ja ta fasa ihu tana ɗora hannunta a kan nasa, raurau ta yi da idanu ta sa ɗayan hannun ta riƙe hunnunsa wanda ya riƙe kunnen ta ce “Don Allah karka cire mini kunne.”
Sakar mata ya yi ta yi saurin tashi tsaye tana shafa kunnen, kallon ɗan ƙaramin bakinta yake yadda take murguɗa shi, wato ita ko me za a mata ba za ta daina rashin kunya ba. Ajiyar zuciya ya sauke ya miƙe tsaye jin ƙaran ringing wayarsa ya nufi ɗaki, sum-sum ta bi bayan shi tana ƙara ƙare masa kallo, yadda yake tafiyar sai abin ya birge ta ga shi tsayayyen namiji mai jini a jika, gashin kansa da ya daure da rubam ta kalla tana gyaɗa kai, gabaɗaya sai ya mata kama da mata..
“Alƙur'an ya yi kama da Allu Arjun ɗan India.” Ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi.
Juyowa ya yi ya ga shi take kallo ya yi murmushi ya ɗauki wayar, yana ɗagawa ta ji ya ce “No no Mom karki shigo gani nan zan fito.” Ya faɗa da sauri. Kafin ya sauke wayar ya gano ta ɗaga caméra tana tunkaro ɗakin, da hanzari ya buɗe wardrobe ya ɗauko wata riga da wando jins baƙi rigar ja ya nufi ta. Ja da baya ta yi tana faɗin “Meye haka?”
Bai kula ta ba ya kamo ta tana zillewa ya shiga ƙoƙarin cire mata doguwar rigar da ke jikinta, kunce suka shiga yi ta dage ba zai cire mata kaya ba shi kuma ganin tana ɓata masa lokaci ya saka ta tsakanin kafafuwansa ya matse ta ya ɗaga hannayenta sama ya cire rigar, a ruɗe ta kwalla ihu tana faɗin “Waiyo zai mini tsirara na shiga uku!” Ta faɗa tana zamewa a ƙoƙarin ta na son zama a ƙasa ganin daga pant sai wata ƴar karamar farar riga a jikinta. Shi dariya ma ta ba shi sai wani rufe jiki take, a ransa yana cewa _'Ka ji wannan kwailar yarinyar yo me zan gani a jikinki?'_
Ƙararrawa aka dinga dannowa amma ya yi kunnen uwar shegu ya ƙi buɗewa, sai da ya sa mata kayan ya kamo gashin kanta ya ƙara daure mata shi. Ita kuwa sai zagin shi take tana jero masa Allah ya isa, ta kuma ce sai ta rama duk abin da ya mata ya ce ya ji ta rama ɗin. Jinkin madubi ya kawo ta ya ce “Beauty kalli ki ga yadda kika yi kyau.”
Har ta ɗago za ta masa rashin mutumci ta kalli yadda kayan ya mata kyau, shafa fuskarta ta yi ta juyo ta kalle shi ya sakar mata murmushi..
Ƙofar ɗakin ya nufa ya buɗe sai ga wata ƴar karamar yarinya mai shekaru 8 kyakkyawa mai kama da shi ta shigo da gudu tana faɗin “Daddy I miss you?” Ta faɗa jikinsa. Rungume ta ya yi yana shafa bayan ta ya ce “Miss you too my darling.”
Andizo ta saki baki tana kallon yarinya kyakkyawa, har za ta yi magana ta ga wannan matar ta shigo waya kare a kunnenta karaf idanuwanta ya sauka a kanta. Sauke wayar ta yi ta shigo daret ta iso har gaban Andizo cike da mamakin ganin ta, kallon Sultan ta yi ta ce “Son wannan black beauty fa? Wa ya kawo ta?”
Tashi ya yi tsaye ya ruƙo hannun yarsa ya samu waje ya zauna, sai da Mom ta sake tambayar shi ya daure fuska ya ce “Ita ce na aura.”
“What? Ka yi me ka ce? Son kana cikin hankalinka kuwa? Wannan ɗin ƴar ƙaramar yarinyar kusan sa'ar ƴarka ce ka aura? Waye ya aura maka ita?”