Sashe 40
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 5 min read
“Ayya Allah sarki to sai ka zo.”
To ya ce mata sannan ya kashe kiran.
Tashi ta yi ta isa wajen Ahmad ganin ya iso, kankwasa glass ɗin ta yi ya zuge, wani daddaɗan ƙamshi ne ya ziyarce ta har sai da ta lumshe ido ta buɗe su a kanshi, kallon ta ya yi sannan ya ce “Shiga mu tafi sauri nake karki ɓata mini lokaci, ina da abin yi karki ce za ki mini wannan rashin kunyar taki.”
Wani irin kallon raini ta mishi ta ɗora hannunta a bakin ƙofar ta ce “Dama zuwa na yi na ce maka ka tafi gida yanzu ina da wajen zuwa, ina so zan je gidan su ƙawata Amira ba ta jin daɗi zan duba ta da jiki.”
“OK to shi kenan sai kin dawo.”
To ta ce mishi sannan ta juya cikin nutsuwa ta wuce ya bi bayanta da kallo yana jinjina kai..
Yana zuwa ya yi packing a motarsa ya buɗe ya fito yana faɗin “Afuwan fa Khadija kina ta jira ko?”..
“Ba komai ina Sadiyar take?”
Nuna mata mota ya yi sai ta zagaya za ta shiga baya ya ce “Ki shiga gaba mana Khadija.”
Murmushi ta yi ta shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga suka bar wajen duk a kan idanun Ahmad, kwafa ya ja ya ja motarsa ya wuce, yana jinjina rainin da Khadija ta mishi yaro ƙarami wanda bai kashi ba ta shiga gaban mota shi, da shi sai ta masa ɗibar albarka kuma taƙi shiga. Iskar bakinsa ya fesar yana kallon hanya, a fusace ya ce “Yarinyar nan sai na koya miki hankali tukun za ki daina mini rashin kunya, ni za ki mayar kamar ƙanenki? Wallahi da na ce na fasa aurenki saboda tausayinki da nake ji amma yanzu na daina dole ma na aure ki na ladaftar da ke yadda ko suna na kika ji sai kin rusuna, sai na nuna miki ni Ahmad sanin da kika mini a farkon haɗuwarmu haka nake babu abin da ya rage sai ma ƙaruwa ya yi..”
Suna isa gidan su Amira ya yi hon aka buɗe mishi get ya sa kai ciki, a tare duk suka fito ya tsaya tare da sa hannu a aljihunsa ya fito da waya, kiran Amira ya yi ya ce mata sun zo ta ce ga ta nan zuwa. Suna nan tsaye sai ga ta ta fito, tana hango Andizo ta haɗa da gudu ta iso suka rungumi juna suna murna, ɗago ta Andizo ta yi ta ce “Ƙawata ashe ba ki da lafiya?”
“Hmm ki bari kawai muje ciki tukun.”
Ɗakin baƙi ta kaisu ta fita ta kawo musu abinci da ruwa da duk abin buƙata, zama ta yi tana faɗin “Arma 'yan ècole gaskiya naji daɗi da ka zo mini da ƙawata, da ina cewa sai na ƙara jin sauƙi zan je na gano yarana.”
Murmushi Arma ya yi ya ce “Itama ba ta san ba ki da lafiya ba sai jiya nake sanar da ita da zuwan da zan yi, shi ne ta ce to za mu zo tare.” Ya faɗa yana kallon ta.
Dafa Andizo ta yi ta ce “Nasan ni mai laifi ce a wajen ki ƙawata ina ba da haƙuri, an yi mutuwa ban je ba an kuma samu ƙaruwa nan ma ban je duk ina kwance ba lafiya, ƙarshe da abin ya fi ƙarfin nan sai da aka fitar da ni waje fa.”
Zaro ido Andizo ta yi tana kallon Amira, tagumi ta yi ta ce “Allah sarki Wallahi ban sani ba dukkan mu kowa yana cikin yanayi, ashe har waje aka fitar da ke Allah ya ƙara lafiya ya su Mama.”
“Wallahi wani yayana da ya kira waya aka ce masa ba ni da lafiya gani a kwance ko motsi ba ne yi, shi ne ya mana kuɗin jirgi da komai aka kaini ƙasar da yake, yana da kirki sosai ba ki ga yadda yake kula da ni ba kamar 'yar da ya haifa. Da za mu dawo ya ce zai biyo mu ya kawo ziyara wa Mama saboda ba mu je tare da ita ba da Yaya muka je da wata likita da aka haɗa mu da ita tun daga nan. Mama kuma tana nan lafiya lau idan mun gama ta ce ku shiga a gaisa, ya karatu Sadiya?”
“Alhamdu Lillahi Amira ya ƙarfin jiki? To Allah ya ƙara lafiya.”
Jinjina kai Andizo ta yi ta ce “Kai gaskiya ya cika mutumin kirki, Allah ya saka mishi da alkhairi yadda ya taimake ki Allah ya ba shi duk abin da yake nema duniya da lahira.”
Cikin jin daɗi Amira ta amsa da amin sannan suka ci gaba da hira.
Su Arma da suka jima suka ce su za su wuce Amira ta hana Andizo ta tafi ta ce za ta sa a kaita kar ta bi su Arma tun da ba hanya suke ba, ba dan ta so ba ta zauna tana faɗin “Haba Amira yo ai da sai in hau motar haya babu komai.”
Hararar ta Amira ta yi ta kama hannunta ta kaita ɗakinta ta zaunar a bakin gado, hira suka fara amma duk hankalinta yana kan su Nour kar su fara kuka, kallon ta yi cike da damuwa ta ce “Ke Amira gaskiya ki sa a kaini gida yaranki lokacin tashin su ya yi, gabaɗaya ba na jin nutsuwa gida zan tafi.”
Tashi Amira ta yi ta ce “To shi kenan ina zuwa bari naje na sanar da direban ga shi can yana ba wa flower ruwa.”
To ya ce mata ta wuce, ko minti ɗaya Amira ba ta yi da tafiya ba aka kwankwaso kofar, miƙewa Andizo ta yi ta isa bakin kofar ta ce “Amira ba ta nan ta fita.” Ta faɗa tana buɗe ƙofar.
Tun daga kan kyakkyawan ƙafafuwanta ta soma kallon shi har zuwa kan fiskarsa wadda ƙasunba ta cika ta, kallo ɗaya za ka mishi ka gane yana cikin damuwa.
Zaro ido ya yi ya juya gefe da gefe ya ga ba kowa, kallon shi kawai take tana tunanin a ina ta taɓa ganin mai kama da wannan fuskar, ba ta ankara ba ta ji ya kama hannunta ya tura ta cikin ɗakin ya kulle. Zaro ido ta yi ta soma ja da baya gabaɗaya jikinsa rawa yake so yake ya kira sunanta amma ya kasa sai nuna ta yake da hannu, zamewa ta yi ƙasa ta kankame jikinta tunaninta ya ba wannan mutumin mai larurar ƙwaƙwalwa ne ba a cikin haiyacinsa yake ba...
_Maman Nusaiba ce_
[6/22, 1:34 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_
37