← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 75

Sashe 50

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“E haka za ki ce mana dama tun da har wani ƙato ya ɗauko ki ya kawo ki asibiti. Zan yi maganin ku daga ke har shi.”
Banza ta mishi ba ta ce komai ba har Hajiya ta, shigo da likita aka cire mata allurar ƙarin ruwa ta sauko da ita daga kan gadon, a hankali take takawa sosai ta ji daɗin ƙafar ganin kumburin ya huce zafin ma ba sosai ba take ji.
A harabar asibitin suka isko Sultan ya tari Hajiya ya ce “Hajiya zo mu je ku shiga motata wannan motar ta muku kaɗan.”
Fuska a sake ta ce “To Sultan ai da ka bari ma mun tafi a haka ɗawainiyar ta yi yawa, amma to ina su mamar taka?”
Shafa sajansa ya yi ya ce “Ai sun tafi gida wata motar ta zo ta ɗauke su suka tafi.”
Motar ya buɗe musu suka shiga su kuma su Mamma suka shiga ta Ahmad suka bar asibitin.

Sun fara tafiya Andizo ta ɗago kai ta ce “Hajiya ba ki sanar da ni ba wannan maganar, kinga nan wancan mugun ba ya nan ki ba ni labarin kafin mu je gida.”

“Haba Khadija ke da kike fama da rashin lafiya ina ke ina son jin labari?”
“Ni kam dai ina so ki faɗa mini.”
Sultan ma ya kasa kunne yana jin wani labari ne ta kafe sai an ba ta shi daga tasowar ta daga gadon asibiti?

“Kamar yadda na fara faɗa miki Alyasa'a babban ɗa a wajen Musalle, da kuma ɗan autana Ziya'ulhaƙ da mahaifin Zulai da ƙanenta. Sun kasance dukkan su sojoji ne mahaifin Zulai shi ne general a wajen aikin su Alyasa'a kuma mataimakinsa, Ziya'ulhaƙ da ƙanen Zulai su ne kasa da su, sun kasance sojoji ƙasa da ƙasa ne. A wannan rana ta asabar aka tura su can jahar Tahoua cikin wani daji da 'yan ta'adda suka addabi wajen, haka muka yi sallama da su suka tafi muna ta musu addu'a, kamar Alyasa'a yana ganin wani abu sai sun shiga mota sai ya dawo ya rungume ni ya rungume uwarsa Zulai ya ce zai yi kewar mu, sai da ya yi haka ya fi sau biyar sannan na ɗaka mishi duka na ce ya tafi jiran shi fa suke sannan ya shiga mota. Haka muak dinga ɗaga musu hannu muka dawo ciki, a wannan lokacin Salim yana makaranta sai da ya kira aka ce mishi su tafi kamar yaro ƙarami ya yi ta kuka sai da na rarrashe shi ya yi shuru..
Bayan sun sauka muka yi waya da su wadda ita ce ta farko kuma ta ƙarshe..”

_Maman Nusaiba ce_
[6/27, 11:38 PM] Ummu Amjad: ADZ

41

Saurin kallon ta Andizo ta yi Sultan kuma ya ja birki a ƙofar wani babba shopping mall mai kyau, Hajiya ta dago hawayen da suka zubo mata ta dubi Sultan ta ce “Ya kuma ka tsaya?”
Juyowa ya yi yana murmushi sannan ya ce “Hajiya ki zauna za mu shiga na sayo mata ɗan kayan marmari irin na marassa lafiya ko ta warware da wuri, kinga kuma likita ya ce ake kula da ita kar a bari ta shiga damuwa, to nasan tana son irin kayan wajen nan shi ya sa na tsaya.”
Turo baki gaba ta yi tana yin fuskar tausayi jin abin da ya faɗa, ita sam ba ta son jerawa da shi amma ganin Hajiya na kallon ta ya sa ta buɗe motar ta fita. Hannunta zai kama ta maƙale kafaɗa ta ce “Don Allah ka bari ni ba na son kake kama hannuna tun da ni ba muharramarka ba ce.”
Murmushi ya yi kamar bai ji mai ta faɗa ba sai da ya kai hannu ya ja kuncinta sannan suka jera suka nufi ciki. Suna shiga wasu daga cikin masu sayayya suka dinga kallon su suna magana ƙasa-ƙasa, ƙara ɗaure fuska ta yi domin ita ta tsani kallo ya yi yawa duk sai ta daburce. Wajen kayan marmari ya ja ta suka ya dinga ɗiba mata su apple ayaba da sauransu, ta yi tsaye tana kallon ikon Allah ganin yadda yake kwasar kayan kamar ba kuɗi zai ba da ba, gaba ya yi ta bi bayan shi suka iso wajen su chocolate ya kalle ta, saurin sunkuyar da kai ta yi dan kar ya ga abin da take kallo ya ɗauko mata, murmushi ya sakar mata ya ɗauko mata duk abin da ya san tana so sannan suka wuce wajen biyan kuɗi. Yana biya suka sa mishi a leda aka dauka ya nuna musu motar da za su saka, ɗago kai ta yi za ta mishi magana sai ga wata matashiyar budurwa ta iso wajen su, farin cikin ne ya bayyana kan fuskar budurwar ta dafe ƙirji ta ce “Mr J! Kai nake gani ko dai mafarki nake?”
Annurin fuskarsa ta ga ya ɗauke suka haɗa ido sai ya saki fuska ya kalli budurwar yana murmushi ya ce “E ni ne dai.”
Kamar za ta faɗa jikinsa ta matso kusa da shi sosai ta ce “Don Allah ka ba ni number ka ni ɗin nan da kake gani babbar masoyiyarka ce ta haƙiƙa, in ba damuwa ka ba ni number ka sai mu yi magana ka taimaka.”
Ta faɗa kamar za ta yi kuka, kallon Andizo ya yi ya ga tana kallon budurwar da wani irin yanayi, murmushi ta yi yana jinjina kai ya ce “Kawo wayar na sa miki number.”
Miƙa mishi ta yi zai karɓa ta yi saurin amsa ta daddana ta sa mata number ta miƙa mata, da kallo budurwar ta bi Andizo sai kuma ta amsa tana faɗin “Merci beaucoup, amma ke ƴarsa ce ko?”
Ko kallon ta ba ta yi ba dan mugun haushin budurwar ta ji, Sultan ya ji daɗi ya rufe shi ganin Andizo ta nuna kishi a kanshi, gyaran murya ya yi ganin budurwar ba ta tafi ba ya ce “To sai an jima mu za mu wuce..”
“Don Allah Mr J ƴarka ce Ko ƙanwarka?” Budurwar ta faɗa domin ita tuni ta tabbatar wa kanta tsuntsunta ya kama tarko tun da har ta samu number Sultan cikin ruwan sanyi, abin da ta ɗauki sama da shekara biyu tana neman wanda zai haɗa ta da shi amma aka yi ta damfarar ta ƙarshe dai ta haƙura, sai yau kamar daga sama ta ganshi.
“A a ba 'yata ba ce she is my favourite wife.”
Zaro ido ta yi sai kuma ta wayance ta ce “Ayya yi haƙuri madam ai ban sani ba mu fans ɗin mijinki ne, ni suna na Halisa ɗiyar gwamnan Niamey.”
Kallon ta ya yi ya jinjina kai ya ce “Wow ashe ku ke riƙe da garin? To na gode sosai da ƙauna sai an jima mun wuce.”
Har sun juya ta kira sunansa ya juyo ta ƙaraso ta ce “Please one minute zan ba ka wani abu kar ka ce ba ka so.” Ta faɗa tana ciro wani babban turare na maza mai shegen ƙamshi sabon fitowa, miƙa mishi ta yi tana murmushi ta ce “Ga kyauta ta a matsayina na fans Allah ya sa ban ɓata ran madam ba.”
Amsa ya yi ya mata godiya Andizo ta kalle ta ce “Mun gode Halisa sai an jima.”
Tafiya suka yi suka bar ta a nan tsaye tana sakin murmushi kamar wata sakarya. Wasu 'yanmata biyu ne suka iso wajen da take tsaye, ɗayar ta ce “Wai ke ina kika shiga muke ta duba ki?”
Lumshe ido ta yi ta ce “Yau dai na ga abin ƙauna ta.”
Kallon mahaukaciya suka mata ɗaya ta ce “Haba dai Halisa ai ba abu ba ne mai sauƙi ki ga Mr J a nan garin, da a Nigeria ne ba zan miki gardama ba in ya zo hutu za ki iya ganin shi a wani wajen.”
“Wallahi da gaske nake Bishira ku yarda da magana ta kunga har number shi na amsa, sannan wannan turaren da na saya dama dan shi na saya idan Allah ya haɗa ni da shi na ba shi sai ga shi kamar daga sama na haɗu da su a nan.”
Hararar ta Bishira ta yi ta ce “To in dai da gaske ne mu fita ki nuna mana shi.”
Da hanzari ta ce “Ku yo sauri ga motarsu can ana sa musu kaya.”
Suna fita suka ganshi tsaye shi da Andizo ana sa kayan da suka saya, kallon juna suka yi Bishira ta ce “Kan uba! Alƙur'an shi ne bari mu je mu gaisa.” Ta faɗa tana shirin tafiya Halisa ta damƙo hannunta ta ce “Kar ki je tare fa suke da waccan yarinyar wai ya ce mini matarsa ce.”
Kallon Andizo Bishira take tana tafa hannu, sai kuma ta ce “Ke Wallahi faɗi ne yake ba matarsa ba ce ko kin manta a binciken da muka sa aka mana an ce ba shi da aure amma yana da matashiyar budurwa? Ko kin manta uwar ɗiyarsa rasuwa ta yi?”
Dafa ƙirji Halisa ta yi ta ce “Wash Wallahi sai yanzu naji zuciyata ta yi sanyi, yanzu haka ji nake kamar na faɗi saboda ganin waccan ƙaramar yarinyar a zaman matar masoyina.” dariya suka yi suna tafawa har motar su Andizo ta bar wajen sannan suma suka tafi..

Bayan sun kama hanya Andizo ta sauke ajiyar zuciya ta ce “Hajiya ki ci gaba da ba ni labarin dama ban bi shi ba sai zafi nake ji na haɗa zufa..” Ta faɗa tana murguda baki, shi kuwa yana kallon ta ta madubi ya yi murmushi.
Chapter 50 · 0% Book details