← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 75

Sashe 4

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maƙale kafaɗa ya yi irin ko a jikin shi kai tsaye ya ce “Kawai ni naje aka ɗaura mana aure, na ga kin takura mini tun da Hibbat ta mutu ba ku da magana sai ta in yi aure, to ni kuma ban samu wadda nake so ba sai yanzu kuma ita ce wannan wadda nake matuƙar so.” Ya faɗa yana kallon Mom..

Sake da baki Mom ke kallon Sultan, duk da halin shi na rashin kirki amma ba ta yi tsammanin zai iya zuwa wani waje a ɗaura masa aure ba tare da sun sani ba, kuma auren ma da ƙaramar yarinya wadda ko ciwon kanta ba ta sani ba bare ta san me ake nufi da auren kanshi. Salati ta dinga tana dafe ƙirji in ta kalli Sultan sai ta juyo ta kalli Andizo da take kifkifta idanu, zama ta yi a bakin gado ta kalli Andizo ta ce “Come here.”
Alamar da ta mata da hannu ne ya sa Andizo ta gane cewa kiran ta take, a hankali ta tako ta iso gaban Mom ta tsaya, sai da Mom ta ƙare mata kallo sannan ta ce “Ya sunanki?”
A sanyaye ta ce “Suna na Khadija na malami amma a ƙauyenmu ana ce mini Andizo, shin ke ɗin babarsa ce?”
Murmushin yaƙe Mom ta yi ta ce “Yes ni Mom ɗin sa ce.”

“To don Allah ki faɗa masa ya mayar da ni garinmu in da ya sa aka sato ni, yanzu haka nasan an manta da ni ma sai su ɗauka ko mutuwa na yi namun daji sun cinye namana.” Ta faɗa tana matso ƙwalla.
Ƙara tafa hannu Mom ke yi tana kallon Sultan da yake daddana waya, kwafa ta yi ta ce “Ina ne garin naku? Ƙauyen Kano ko na Katsina ko Kaduna ko Jigawa a wani state kike?”

“Ki ma daina ɓata bakinki Khadija ba 'yar Nigeria ba ce.” Ya faɗa yana kallon Mom.

“Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Sultan mu kake son tozartawa a idanun duniya? Yanzu har za ka iya tsallake wata ƙasa ka sato yarinya ƙarama da sunan kana son ta wai ma har an ɗaura muku aure? Ina ne ƙasarsu?”

“Inna ni 'yar Niger ce garinmu yana wajen Niamey, don Allah karki barni a wajen nan mugu ne yanzu fa sai da ya cire mini riga ya sa mini wannan kayan na 'yan iska, to amma dai duk da haka na yi kyau. Ni dai so nake in ganni a gida.” Andizo ta faɗa tana shafa kayan jikinta..
Tashi tsaye Mom ta yi cikin tsananin fushi ta ce “Maza tashi mu je ka kaini wajen malamin da ya ɗaura muku aure, kai na ma fasa tashi maza ka ciro mini ticket guda biyu yanzun nan na mayar da ita ga ahalinta, ban da kai shashasha ne kawai dan kana son ta sai ka sato ta haka ka auri Muhibbat da ka fara son ta? Ba gidansu muka je aka nema maka auren ta ba? To ka tashi kafin raina ya ƙara ɓaci na la'ance ka tun da abin da ka fi so kenan..”
Da sauri ya ɗago ya kalle ta jin abin da ta faɗa, fuskar tausayi ya yi ya matso kusa da su ya kalli Andizo da itama shi take kallo ya ce “Beauty ai kina so na za ki zauna da ni ko? Kinga ga Farrah nan sai kuke zuwa makaranta.” Ya faɗa yana haɗa hannunayensu..
Farrah ta kalli Andizo ta ce “Za ki zama friend ɗina?”

Kallon yarinyar Andizo ta yi ta kama kumatunta tana murmushi ta ce “ 'Yar yarinya mai kumatu irin na ƴar lukuta, mene ne friend?”
Dariya Farrah ta yi itama ta kama kumatun Andizo ta ce “Aboki ko ƙawa.”

“To na gane, amma ni garinmu nake so a kaini sai dai in za ki dinga zuwa Niamey a can za a mini aure da mai hankali shirin Allah, za ki zo wajen bikina ai ko?”
Murna Farrah ta hau yi tana dariya ta ce “E ina so zan je tare za mu tafi na ga gidanku.”

Ganin surutun nasu ba na ƙarewa ba ne Mom ta kama hanayensu ta ce “Mu je waje maza ina nan zuwa, Khadija riƙe hannun Farrah ku zauna a palo ku jira ni..”

Bayan sun fita Mom ta tsatsara Sultan ta ce “Lokacin da aka ɗaura muku aure waye waliyin ka waye kuma waliyin ta? Sannan su waye shedun an ɗaura auren?”
Hannu ya sa a aljihu yana murmushi tare da shafa kwantaccan sajensa ya ce “Mom Nazee ne fa ya ɗaura mana auren, kawai kuɗi na ba shi na ce ya ɗaura mana aure, sai ya ce sai an sayo halawa da goro kuma ya ji ana karanta fahita in za a ɗaura aure..”
Ajiyar zuciya Mom ta sauke jin ba cikakken ɗaurin aure aka yi ba, kuma daɗin daɗawa ma Allah ya rufi asiri bai haƙe wa yarinyar mutane ba, kallon shi ta yi ta ce “wato saboda tsabar jahilci babu abin da ka sani game da addini sai Fatiha ko? Ka kyauta shi uban naka da ya ɗaura ka a kan wannan muguwar hanyar daga kai har shi sai kun yi kuka matuƙar ba ku canja hali ba banza kawai shashasha fi ce mu je ka sa a cire mana ticket ɗin, sannan ka haɗa mu da waɗanda suka sato maka ita su kai mu har garin su..”

Baki ya buɗe zai yi magana ta daka mishi tsawa “Ba na son ka ce komai kawai ka yi abin da na ce maka!”
Ba dan ya so ba ya hadiye maganar da yake son yi ya yi gaba ta bi shia baya..

Suna fitowa Mom ta kama hannunsu suka fito, a harabar gidan ta tsaya ta kalle su fuska daure ta ce “Kabir cikin ku su waye suka kawo yarinyar nan?”
Sai da ya kalli Sultan Mom ta daka musu tsawa ya ce “Hajiya mu ai a airport muka amso ta a wajen wasu da suka kawo ta.”
Tsaki ta ja ta sa su Andizo a mota itama ta shiga, direba na shirin shigowa ta dakatar da shi ta ce Sultan ya zo ya yi draving da kanshi, haka ya shiga jikinsa a sayayye..

Kafin su isa gidan Mom Sultan ya sa aka tanadar musu da ticket uku saboda Farrah ta kafe ta ce sai ta ga garin su Andizo tun da ta zama ƙawarta.

Washe gari jirgin su Andizo ya ɗaga zuwa ƙasar Niamey, saboda murnar da take har rungume Mom ta yi tana mata godiya na fito da ita da ta yi daga wannan baƙin gidan za ta kai ta ahalinta...

Ƙarfe 10:50am jirgin su ya sauka a Niamey, sosai ta dinga kalle-kalle har suka shiga mota, direban da ya dauke su can ya kaisu wata unguwa in da ya haɗa Mom da wasu matasa uku ya sanar da su Oga Sultan ne ya ce su mayar da yarinyar har cikin garinsu. Babu muso suka amsa da To..

Kasancewar sun gaji wani gida suka kai su suka huta suka ci abinci, Farrah sai cewa take “Khady ina gidanku yake wai.”
Ita kuwa tana dariya ta ce “Ba nan ba ne mun kusa.”

Sai da aka yi Sallar Azuhar sannan suka fito daga gidan, buɗe musu mota suka yi suka shiga suka wuce..

Da sauri ya fito daga motar yana kallon Ahmad ya ce “Ahmad Wallahi naji a jikina a cikin motar can akwai Khadijata, don Allah zo mu bi bayan su mu gani.”

Girgiza kai Ahmad ya yi ya ce “Anya ba ka samu taɓin hankali ba Yaya Salim? Ta ya kawai daga ganin mota sai ka ce da Khadija a ciki? Ka ga shiga mu je gida..”
Ba dan ransa ya so ba ya shiga motar Ahmad ya ce ya koma gefe shi zai ja su kar ya je ya kifar da su....

Next Fage.

_Maman Nusaiba ce_
[5/24, 5:07 PM] Ummu Amjad: *_Arewabooks @saratalkasum88_*

Littafin ANDIZO na kuɗi ne N300 ne, za ku turo kuɗinku ta wannan account ɗin.
Account number 0003187186
Name account, khadija Salisu
Name Bank, Ja'iz Bank.
Sai a yi screen shot a turo ta wannan number.
🥏+966577675904.

18

Sai da suka tsaya suka sha mai sannan suka ci gaba da tafiya, Andizo da Farrah sai surutu suke Mom dai na kallon su, ita Andizo tana faɗa mata yadda suke yi a garinsu ita kuma Farrah na faɗa mata irin wajen shaƙatawa da Sultan kai ta da kuma sunan school ɗin da aka saka ta..
Sun yi nisa sosai da tafiya hanyar sai ta rabe musu gida biyu suka rasa wacce ce suka bi farkon zuwan su, ganin sun tsaya Mom ta kalli direban ta ce “Ya dai na ga kun tsaya?”
Ɗaya daga cikin su ne ya ba ta amsa, “Mama hanyar ce ta rabe mana gida biyu mun rasa wacce ce muka bi a farkon zuwan mu..”

Shuru Mom ta yi ta kalli Andizo da ko a kanta sai hira suke, kiran sunan ta yi ta ɗago kai ta kalli Mom tana sakar mata murmushi, ruƙo hannunta ta yi cikin nuna kulawa ta ce “Khadija shin ko za ki gane daga nan wacce hanya za ta kaimu cikin ƙauyenku?”
Kallon gefe ta yi amma duhun glass ɗin motar ya hana ta ganin abin da yake waje ta ce “Mom to sai dai in ku buɗe mini na fita na gani ko zan iya ganewa.”
Umarni Mom ta ba su suka buɗe motar, sai da Mom ta fita ta buɗe mata daga bayan ta fito Farrah na biye da ita. Kallon wajen ta dinga yi ko za ta gane sai dai ta ga wajen ba ta taɓa zuwa ba, a sanyaye ta kalli Mom ta ce “Mom gaskiya ni ban san ba wannan wajen, dama ban taɓa zuwa Niamey ba ina dai jin sunan ta.”
Ganin lokaci na ƙure musu ɗaya daga cikin su ya danna wa Sultan kira.

Lokacin Sultan na wajen motsa jiki ya yi shakaf da zuba, yana shirin fita ya ji wayarsa na ringing ya juyo ya ɗauka, ganin mai kiran ya yi saurin ɗagawa ya kara a kunne bai ce komai ba.

“Hello Oga mun fa kasa gane kan hanyar ta rabe mana guda biyu, wacce za mu bi?”
Chapter 4 · 0% Book details