Sashe 58
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Can ɓangaren Sultan tun da suka shiga da shi emargercy ba su fito ba har sai da suka shafe awa biyu suna faman ceton rayuwarsa, bayan sun fito suka buƙaci yun magana da Mom ta bi bayan babban doctor ita da Amira da Farrah zuwa office ɗin sa, bayan sun zauna gama duba sakamakon da suka samu na rashin lafiyar Sultan ya aje a gefe ya fuskance su, Mom ta tattaro 'yar sauran nutsuwar da ta rage mata ta fuskanci doctor domin ya ji wani halin ɗan nata yake ciki.
“Hajiya gaskiya yallaɓai yana cikin mawuyacin hali ƙodarsa na gab da kamuwa da ciki, zuciyarsa dama tun zuwan ku farko na sanar da ku ya kamu da ciwon zuciya, ya kamata ku nemo mishi abin da yake buƙata tun kafin abin nasa ya ƙara girmama, daga ya farfaɗo sunan wata yake kira ni ban ma riƙe sunan ba amma dai koma meye wannan mai sunan ita yake son gani a kusa da shi..”
Hawayen da suka zubo mata ta sa hannu ta goge tana girgiza kai ta ce “Ba zai taɓa samun wannan mai sunan ba domin an riga da an aura wa wani ita, kuma ita ɗin ma yanzu haka ta ma fi shi jin jiki ba ta da lafiya.”
Shuru Doctor ya yi yana kallon su Amira ta ce “Gaskiya ba a yi wannan auren ba Mom, ni zan je na sanar Yaya Ahmad komai har garin nasu zan nema na tafi domin na ga halin da yake ciki kuma na sanar da su abin da suke son aikatawa za su kashe rai biyu ne, na tabbatar Mom Khadija tana son Uncle kawai dan babu yadda za ta yi ne ya karɓi auren Ahmad, ko an ɗaura auren nan nasu zan roki alfarma su warware.” Ta faɗa tana gunjin kuka.
Dafa ta Mom ta yi ta ce “Kin tabbatar ba a ɗaura auren nan ba?”
“E Mom ba a ɗaura ba ai da sauran kwanaki, kuma ma tana cikin wannan yanayin taya za su ɗaura mata aure?”
Kallon su Doctor ya yi ya ce “To ku dai yi ƙoƙarin kawo masa wannan yarinya yana farkawa ya ganta kar aikin da muka masa ya sake dawo da mu baya.”
Godiya suka mishi suka fita a office ɗin, ɗaukan handbag ɗin ta ta yi ta rataya ta ce “Mom ki sa a nema mini ticket ko na dare ne ba na son na kwana a garin nan zan wuce.”
Kallon ta Mom ta yi ta ce “Yanzu ke ba za ki zauna ba sai kin tafi? Ki bari ya samu sauƙi sai mu tafi har da ni zan je har ƙauyen nasu na nemi alfarma.”
Girgiza kai ta yi ta ce “Ba za ki gane ba Mom Khadija ta sanar da ni Maigari yana son wannan haɗin mai Hajja tun farkon abin, to kinga kuwa da Ahmad ne kawai za mu fara idan har ya janye to komai ya zo da sauƙi, shi ya sa na ce miki shi zan fara tunkara da maganar, idan kuma Mama ta dawo sai mu je tare har gidansu mu sanar da su komai.”
Ba yadda Mom ta iya ta kira ɗaya daga cikin yaran Sultan ta sanar da shi ticket take so na zuwa Niger na mutum ɗaya, an gama ya ce sannan ta kashe. Gida ta sa aka kaita ta ce da direban in ya je ya isa airport ya ɗauko Farrah ta kusa sauka ya amsa da to..
_NIGER_
Bayan kwana biyu da kai Andizo ƙauye Maigari ya sa duk malaman ƙauye su dukufa da yi mata addu'a, Liman ya ce za su gwada yi mata ruƙiya su gani ko za ya dace, bai musa ba yau da rana ta yi Liman da wasu baƙin malamai biyu da suka zo suka shigo gidan tana kwance jikin Inna ana ba ta kunu, ganin su ya sa ta kankame Inna tana ɓoye fuskarta. Zama suka yi suka gaisa suna tambayar me jiki suka ce da sauƙi, bayani Maigari ya musu ga abin da za a yi wa Andizo sai suka ba su waje aka bar Umar da Giɗaɗo suka riƙe ta.
Karatu malaman suka fara yi mata suna tofawa har kusan minti ashirin amma shuru, ɗaya daga cikin baƙin malaman ya kalli Liman ya ce “Gaskiya da akwai babbar matsala Liman, aljannun jikin yarinyar nan mugaye ne ba sa ma yin magana amma bari ka ga zan sa su yi magana dolen su.”
Shi dai Liman yana gefe yana kallon su yana tofa tashi addu'ar, ruwa ya sa Umar ya ɗauko ya tofa addu'oi shima ɗayan ya amsa ya tofa sannan suka aje a gefe suka ci gaba da karatu, sai da suka ɗauki lokaci sannan malam ya ɗauki ruwan addu'ar ya zuba mata a fuska. Wata irin zabura ta yi tana ƙoƙarin kwacewa daga hannun su Umar malam ya ce su riƙe ta da kyau suka ƙara riƙe ta, sake ɗaukan ruwan ya yi ya zuba mata ta sa ƙara tana buɗe idanu malam ya yi murmushi ya ce “To daga kuma wa ya turo ku.”
Kuka ta hau yi har da rufe fuska Maigari ya kalli Malam ya ce “Akarramakallah ya kuma take kuka?”
Hannu malam ya ɗaga wa Maigari ya ce “Kar wanda ya sake kuma, ina jin ku me ya sa kuke cutar da baiwar Allah.”
Tsayar da kuka ta yi ta haɗe rai tana kallon Malam kamar ba ita ba ce take kuka yanzu, fuskar tausayi ta yi ta ce “Malam ka daina ƙona ni nifa babu ruwana ba ni nake cutar da ita ni iyaka ta kawai mai tsaro ne.”
Jinjina kai Malam ya yi ya ce “To idan ba kai kake cutar da ita ba me ya sa sai kai muka samu? Ka faɗa mana gaskiya tun kafin na ƙona ka.”
Kara murtuke fuska ta yi aljanin ya ce “To idan har ka yi gangancin ƙona ni to tabbas wannan yarinyar ba za ta taɓa samun lafiya ba har abada za ta zauna a haka.”
Ganin abin na shi da wasa da hankali malam ya kuka fesa mata ruwan ta sa ihu tana ƙoƙarin kwacewa suka ƙara riƙe ta gam, Malam ya kuma cewa “Za ka faɗi ko kuma sai na ƙona ka maƙaryaci?”
“Zan faɗa Malam ni ina tsaron inda aka binne sihirin ne, waɗanda suke shan jininta suna cutar da ita suna nan guduwa suka yi.”
“To maza ka kira su su dawo yau sai kun faɗa mana wanda ya sa ku aikata wa baiwar Allah wannan ɗanyan aikin.” Ɗayan malamin ya faɗa a fusace.
A galabaice aljanin ya ce “Sun gudu ni kaina tsoron su nake ji amma zan sanar da ku komai, wata mata ce ta je har ƙasar India aka mata wannan aikin a kan Khadija, da farko cewa ta yi kashe ta bokan ya ce ba zai yiyu ba shi ne ta ce a sa mata ciwon da kowa zai tsane ta, ƙarshe ta dinga ɗoyi tana wari koya ya gudu ya bar ta har 'yan'uwanta kowa ya tsane ta ta ruɓe ƙarshe ta mutu. To yanzu maganar da nake maka sun gama sa mata dukkan cutar da matar da nema daga gobe wasu ƙuraje za su fito mata a cikinta masu wari wanda zai dinga fitar da koran ruwa mai tsami har' yan hanjinta su fatattake su ruɓe, idan an gama wannan kuma an hana ta gane kowa a makantar da ita ta yadda babu wanda za ta gani kuma ba bakin magana ballantana in tana da buƙatar wani abu ta iya magana. Kun taki sa'a da kuka fara nema mata maganin cutar ta yau, da kin bari sai gobe to ba zan ce ba za ta warke ba amma da wahala, kai ko yanzu illar da suka mata ta wuce misali dan haka ku bari su zo sai ku sa su warware..”
Shuru su Malam suka yi sai kuma ya ce “To yanzu kai ka nuna mana in da aka binne sihirin mana.”
Girgiza kai ya yi cike da tsaro ya ce “Idan na nuna muku za su kashe ni, yanzu haka ni kaina ban san takaimaiman in da maganin nan yake ba domin jiya sun canja mishi waje, a nan inda nake a tsaye yake amma ban san ta wani ɓangare yake ba, da za au binne aikina aka yi wajen wani boka na kai saƙo kafin na dawo sun binne sun sanar da ni a nan yake amma ba za gani ba sun mishi muguwar ajiya..”
Malam ya gyara zama ya ce “To kai ya sunanka?”
Dariya ya yi sannan ya ce “Ni ne Najibu.”
Da mamaki malam ya ce “Amma kuma sai naji sunan musulmai gareka, kai kuwa kana musulmi me ya sa kake cutar da ɗan'uwanka musulmi.”
“Ni ba musulmi ba ne malam kawai na zaɓi sunan ne dan ina so.”
“To shi kenan yanzu kai Najibu ba za ka ji tausayin wannan baiwar Allah ba ka tone wannan sihirin?”
“Gaskiya ba zan iya ba, amma taimako ɗaya zan muku.”
Malam ya ce “To muma jinka wani taimako ne?”
“Idan kuma son samun su ku zo da dare. Ko da yamma kusan magariba.”
Malam ya haɗe rai ya ce “Ka tabbatar da gaske kake? Idan fa muka kasa samun su zan ƙona ka da ayar Allah kuma ka san dai ai zan iya ko?”
“Na yarda Malam.” Yana faɗin haka sai gani suka yi ta yi atishawa mai ƙarfi ya koma jikin Umar ta kwanta.
Maigari ya kalle eu ya ce “Amma Malam za su dawo kuwa? An ce fa aljannu mugun wayo né da su ga ƙarya.”
Girgiza kai Malam ya yi ya ce “In sha Allah dai sun dawo, idan ma kuka ƙi dawowa da ƙarfin ikon Allah zan sa su dawo kuma su tone sihirin da suka binne.”
Godiya suka mishi ya miƙa musu sauran ruwan ya ce su shafe mata jikin ta da shi za ta samu sassaucin ciwon da take ji a jikinta, godiya sosai Maigari ya musu sannan suka fita.