← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 75

Sashe 25

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe takwas ta shirya ta saka Unform ɗin da ya kawo mata, sosai kayan suka mata kyau ta ɗaura ɗankwali ta saka hijabin tana murna sosai, kallon ta ya yi ya kamo hannunta ya juya ta irin na 'yan India yana faɗin “A a matar tawa chass abinki, kinga kuwa yadda kika yi kyau kamar ba ke ba? Wai meye sirrin na ga sai wani ƙara zama lukuta kike kin yi fes kin barni?”
Dariya ta yi ta yi tsalle ta dire ta yi juyi a gaban shi ya riƙe kwankwaso yana kallon ta suna dariya, shoki ta ɗauko ta dire sannan ta ce “Alƙur'an mai hankali ina sonka sosai, kaima fa ka haɗu kamar ba kai ba.”
Ta faɗa tana gyara hannun hijabi.
Ɗaukan ta ya yi ya ɗauki jakarta ya fito da ita har bakin mota, hakan ya yi daidai da fitowar Aminatou tan gansu a haka ta yi saurin dafe ƙirji kamar za ta faɗi, nan da nan kishi ya motsa mata ganin yadda suke ta wasa a bakin motar taƙi ya saka ta shi kuma yana mata magiya. Tuno maganar Umminta ta yi ta yi saurin faɗin “A'uzu billahi minan sheɗani rajim. Ya Allah ka sassauta mini wannan baƙin kishin nawa kar ya rinjaye ni wataran na cutar da wannan yarinyar, Wallahi ba na son ganin ki da mijina kawai dan babu yadda zan yi ke matarsa ce Allah ya halatta masa ya yi fiye da biyu ma, kuma na shaida mijina kana da adalci ba ka tauye hakkina..” Da sauri ta goge hawayen da suka zubo mata ta gyara zaman hijabinta ta dinga karanto lahaula wala ƙuwata ta doshe su tana mai ƙaƙalo murmushin yake..

Tsayawa Andizo ta yi ta ce “La ka ga Adda za ta fita itama, ai sai mu tafi tare ko?” Ta faɗa tana kallon Aminatou.
Juyowa ya yi yana ƙare mata kallo, hannu ya miƙa mata suka yi musabaha yana murmushi ya ce “Gaskiya kin yi kyau matuƙa, yanzu wannan wankan ba ni za barwa na kalla na more ba gidan Ummi za a kai?”

Murmushi mai sauti ta yi ko ba komai ya sanyaya mata zuciya da ruhi, juyawa ta yi ta ce “A a ku tafi abin ku na yafe ba na so na ɓata muku lokaci.”

“Gaskiya ki zo mu tafi sai a fara kaini tukun ke sai ya wuce inda zai je.” Andizo ta faɗa tana turo baki. Dariya ta yi ta ce “To 'yar ɓaci naji zan shiga mu je to..”
Yawwa Andizo ta ce ta je da sauri ta shige baya tana dariya ta ce “Dan in walala na yi kwanciyata kafin mu je.”

Ita dai Aminatou wani lokacin in Andizo ta yi wani abin mamaki take kamar babbar mace, shiga ta yi ya ja suka bar gidan..

Tun da suka tafi hira suke yi ita da Andizo shi dai Salim yana sauraron su, Andizo ta miƙo kanta tsakanin kujerunsu ta ce “Adda idan kika haihu ki sa wa baby sunana, kinga sai in samu takwara.”
Saurin kallon ta Aminatou ta yi, a sanyaye ta ce “To Khadija in sha Allah zan miki takwara, amma ki mini addu'a Allah ya kawo cikin ko a wannan satin ko a cikin watan nan sai na haifa miki takwara, kema ai watarana za ki haihu sai ki wa 'yar taki suna na.”

Dafe ƙirji Andizo ta yi ta kalli Salim ta ce “Wai da gaske watarana zan samu ciki irin na haihuwa? Kai to ma ya kiyaye ni ai ba zan iya ba.” Ta faɗa tana taɓe baki, tun da ta taɓa ganin yadda ake naƙuda a ƙauyensu ta ce ita kuwa ba za ta yarda ta yi ciki ba tun da wahala ake sha..
Dariya Salim da Aminatou suka yi, Aminatou ta ce “To fa! Ji wata magana a wajen Khadija, to tun da ba ki so ai shi kenan za mu gani nan da wani lokacin.”
Turo baki ta yi ta koma ta harɗe hannayenta a ƙirji ta ce “Haka kawai yo ina zan iya wannan abin da ake ai sai in mutu l..”

Aminatou ta ce ai kuwa za ta haihu ta ce ta ji amma ai sai ta zama babba ta yi girma sannan ta haihu, Aminatou ta ce to shi kenan sannan ta daina mita tana Allah ya tsare ta da haihuwa.

Suna tsayawa sai da Salim ya shiga ciki ya kaita wajen malamar ya ce ta kula mishi da ita da kyau ta amsa da ba, matsala sannan ya dawo..

Daret gidan su Aminatou ya nufa suna tafiya suna hira har suka isa, ko shiga bai yi ba ya ce kawai ta gaishe da Ummi sauri yake in ya dawo ɗaukan ta zai shigo, to ta ce masa suka yi sallama ta shige ciki shi kuma ya juya ya koma..

Tun da ta shiga ajin ba ta cewa kowa komai ba ta takure a waje ɗaya, sai da wata matahiyar mata da ke kusa da ita ta ɗan taɓa ta ta ce “Baiwar Allah ya sunanki?”
Murmushi ta sakar mata mata ta ce “Sunana Khadija, ke fa?”

“Ni suna na Aishatou, amma dai yau kika fara zuwa ko? Dan na ga kamar dai yau na fara ganin ki.”

“E yau ya kawo ni.”

“Ma sha Allah, to Allah ya, bamu ilimi mai amfani ga al'umma da da kawunanmu.”
Amin Andizo ta ce suka ci gaba da amsar darasi, sai ƙarfe ɗaya aka tashe su..

Haka ta kasance ba ta hutu kullum tana makaranta, sosai take gane karatu yayin da Aishatou ta dinga koya mata wasu abubuwan tun da ta ce mata ita matar aure ce, da farko ba ta yarda ba sai da Salim ya zo ɗaukan ta ta janyo ta suka zo har wajen ta tambaye shi, murmushi ya yi ya ce tana aure shi ne ma mijinta, abin ya ba ta al'ajabi ta kuma, birgewa ganin yadda yake nuna mata tsantsar kulawa kamar zai mayar da ita ciki.

Andizo ta manta da batun wayarta sai da watarana ta yi wanka za ta ɗauko kaya taki wani abu, da mamaki ta ƙara lalumawa ta zaro sai ta wayar ce, dafe kai ta yi ta ce “Ni har na manta da wayar nan Wallahi, ga shi kuma inanson mu yi magana da Farrah.”
Kunna wayar ta yi ta samu waje ta zauna, kamar jira ake ta buɗe wayar sai ga kiran Mom ya shigo wayarta, ta washe baki tana faɗin “Allah sarki Mom ai dama yanzu nake shirin kira.”
Ɗaga kiran ta yi tare da yin sallama Farrah ta amsa.

“Haba Khadija ina ta kira sai a ce wayarki a kashe take ko lalacewa ta yi?”

“Gyara zama ta yi ta ce “Ki bari kawai karatu ne ya ɓoye ni, to kuma ranar da muka yi hirar nan wayar ta lalace sai da aka gyara ta..”

“Ayya to Allah ya kiyaye gaba, so nake na miki surprise ne..”

“Da gaske?” Ta faɗa tana yin dariya..

“Sosai ma an jima za mu tafi Niamey tare da Antyna wajen Yayar Mom mu mata weekend..”

“Ka amma ko da naji daɗi za ki zo gidana ai ko?”

“Dama ai dan na zo gidanki zan biyo ta ba wai dan na ga wannan matar mai faɗan tsiya ba..” Ta faɗa tana haɗe fuska.

Daɗi sosai Andizo ta ji suka ci gaba da labaransu na makaranta..

Yau da yamma sai ga Sabrin ta zo gidan Aminatou, ba yabo ba fallasa ta tarbe ta, ta kawo mata ruwa ta zauna ta ɗauki waya ta kira Andizo ta ce ta zo su ɗaura girki.

Kallon ta Sabrin ta yi tana wani taunar cingam ta ce “Ƙawata wai wata Khadijar naji kina kira ta zo ku yi girki?”

Daure fuska ta yi ta ce “Abokiyar zamana ko da wani abin dan na kira ta mu yi girki?”

Cike da mamaki ta ce “Oh ni! Yaushe kika zama mai ƙwaƙwalwar kifi ban sani ba? Kishiyar taki ce kike yi wa haka? Anya ba ki fara shan kodin ba?”

“A a uwar abin da ya fi kodin nake sha, dama neman ki nake dan na faɗa miki daga yau babu ni babu ke karki sake zuwa gidana, ke ko a hanya muka haɗu kika nuna kin sanni sai na miki rashin mutumci tun da na ga alama so kike ki ruguza mini rayuwar aurena, kina ɗora ni a kan keken ɓera ki kaini ki baro na koma ina zaman gida kamar ke, to daga yau na yanke alaƙar da ke tsakani na da ke. Saboda tsabar shisshigi da ya miki yawa kamar ke Salim yake aure kika sa ake bibiyar rayuwar yarinya duk dan ki tozarta ni ita kuma ki cusa mata baƙin ciki, ke Salim yake aure ko ni? Tambayar ki nake ko kun hada dangi da shi?”

Tashi Sabrin ta yi rai ɓace ya kalli Aminatou ta ce “Yau ni kike faɗa wa wannan baƙaƙen maganganun? To kin yi da shegiya za ki gani, duk taimakon da na miki ina raka ki wajen malamai da bokaye duk dan ki samu fada a wajen mijinki shi ne yau za ki saka mini da haka? Daɗin ta ma daga ke har mijin naki dukkan ku juya ne ba haihuwa kuke ba bare ki yi gadara da shi, da ke ce mai matsalar waccan shashashar ai da yanzu ta samu ciki. Kin yi da ƴar halak Wallahi na rantse sai na rama wannan wulaƙanci, sai na tona duk wani ƙulli da muka yi ni da ke tun daga farko har ƙarshe mijinki sai ya san ke wace ce mai fuska biyu, tun da har kika yi kuskuren shiga gonata za ki ga abin da zan yi, kuma ni duk abin da nake yi ba dan ke nake ba ina da tagger ɗina daban, ke na ma fasa faɗa za ki gani a aikace.” Tana gama faɗin haka ta fita fuu.

A hanya suka haɗu da Andizo za ta bangaje ta ta yi saurin matsawa ta ce “A'uzu billahi minan sheɗani rajim!”
A kufule Sabrin ta kalli Andizo ta ɗaga hannu za ta mare ta sai kuma ta fasa ta wuce.
Chapter 25 · 0% Book details