← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 75

Sashe 68

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Lokacin da su Mama suka samu labarin kin ce Ahmad kike so sai ran Amira ya ɓaci amma a lokacin ba ta nuna miki ba da za su tafo, bayan sun dawo da yan kwanaki na dami Amira yaushe za ta kawo mini ke ta sanar da ni abin da ya faru, to a lokacin ne na zabura na faɗo daga kan gadon asibiti na faɗo a kan glass cup ɗin da Mom ta zuba mini juice, na zubar da jini sosai domin cup ɗin ya fashe har ya shiga jikina sai da aka cire mini, shi ne taɓo da kika gani a ƙirjina.” Ya faɗa yana buɗe mata towel ɗin, wani irin tausayin shi ta ji ta sunkuyar da kai shi kuma ya ci gaba da ba ta labarin ɗaya bayan ɗaya.
“Mom ta ce a ranar sai da aka mini allurar bacci saboda sumbatun da nake yi ina kiran sunanki, kwana biyu tsakani na farfaɗo na sa Rahama ta kira mini Ahmad, yana ɗauka na ce mishi yanzu Ahmad kaine za ka aure mini abin da na fi Ƙauna? Anya akwai amana ?”
A nan ne yake sanar da ni na kwantar da hankalina ai Khadija tawa ce domin ya riga da sadaukar mini, sun shirya komai ta yadda ba ki gane ba Ahmad ba ne Angon, hakan da ya yi Amira ta ce ita kuma za ta maye mishi gurbinki a zuciyarsa a sa bikin kamar yadda aka sa bikin, sosai naji daɗi matuƙa sai naji na samu lafiya duk da an ce in na gama shan magani za a yi mini aiki ƙodata ɗaya ta lalace, haka na dinga shan magani har bikin ya matso nasa Mama ta sayo kayan lefe da duk abin da ake buƙata, idan kuma na ɓangaren abokai ne zan tura wa Ahmad komai ya sayi duk abin da ake buƙata har angon bikin na ce mishi ya ɗinka wa abokansa ko sun kai ashirin, domin naji daɗin yadda ya mini sadaukarwa. Ana saura kwana biyu biki Mom suka yi nasu bikin a nan duk da ba ta gaiyaci kowa ba iya family ne suka zo, ranar ɗaurin aure har ƙauyenku muka je na sa Ahmad ya ba ni turaren da kika san shi da shi nasa na kuma saka facemark na rufe fuskata, ina zaune aka ɗaura mana aure mutane suka dinga ba ni hannu ina amsawa ni da Ahmad domin sun kasa gane ba Ahmad ba ne Angon kasancewar sunanmu ɗaya da shi, kuma su Abba su suka amsa mini aurenki. Bayan mun ta so na kasa nutsuwa sai da na sa Ɗahare ki muka gaisa ba ki gane ni ba saboda kanki a ƙasa yake kin kasa kallon mu, ni kuwa a lokacin kallo ɗaya na miki na gane kika cikin damuwa, sai a lokacin na ƙara tabbatar wa kaina kina masifar sona kawai kin danne ne kika zaɓi Ahmad dan ki faranta ran iyayenki.
A tare aka kawo ku ke da Amira aka yi sama da ita ke kuma aka barki a ƙasa, na so naje amma Ahmad ya hana ni dole na haƙura sai washegari muka je, a nan ma dai ba ki kalli kowa ba har aka gama komai muka fito. Bayan mun fito sai da muka raka abokanmu har mota sannan na koma ɗakin da na sauka na canja kaya na sa turaren da kika sanni da shi na zo gareki. Ahmad da Amira su suka yi komai, ba dan Ahmad ya haƙura ba da yanzu ina kwance ko a mace ko a raye. Amma fa Ahmad sai da ya kwanta rashin lafiya har na kwana uku tukun ya warware, ganin shi a wannan hali ne Amira ta ce da shi in dai har zai iya ta amince su yi aure, Wannan shi ne abin da ya faru.”
Tun da ya fara maganar ta yi lamo a jikinsa tana jinsahar ya sada aya, tashi ta yi ta ce “Gaskiya mun gode wa Ahmad har da Amira, ni ai lokacin an kuma biki ta kira ni ta mini tas ta ce kai za ta aura ta share maka hawaye, ƴar rainin hankali ashe ƙarya take, na jima ina dakon soyayyarka a gangar jiki da ruhina kawai ina dannewa ne domin ba na son ɗora wa kai son wanda ya fi karfina ta kowanni ɓangare.”
Kunnenta ya ja ta sa ƙara tana yarfa hannu ta ce “Akwai ciwo fa Daddyn Farrah.”
“Sai na murɗe wannan bakin da yake kirana da daddy, ke ba irin ki kira ni da sunan masoya sai wani Daddyn Farrah kamar wata suruka ta?”
Kwafa ta yi ta ce “Zan rama ai.”

“Sai dai ki rame yarinya oya zo mu kwanta.”
Kyale shi ta yi suka kwanta nan da na bacci ya ɗauke su...

Washegari da yamma ƙarfe 4:10pm su Rahama suka shirya musu dinner a harabar gidan, kowacce ta gaiyato ƙawayenta da abokan aikinta gidan ya cika taf kamar a lokacin ne ake bikin. Wani tsadaddiyar atamfa Andizo ta saka shi kuma ya sha ƙanana kaya sai ƙamshi suke zubawa, haka aka dinga musu liken kuɗi wasu daga cikin masu zuwan sai mamaki suke ganin matar da Sultan ya auro yarinya ce sosai, wasu kuma suka birge su sai ɗaukan su suke a waya ana musu tafi.
Karfe shida da rabi aka tashi kowa ya tafi gida.
Wannan satin da suka yi ba su samu damar yin baccin kirki ba saboda zuwan da ake yi ana taya Mom murnar auren Sultan, sai ana gobe za su tafi London suka kwanta da wuri..

Washegari suka shirya tafiya zuwa London, tun da ta tashi ta yi sanyi domin ta ji labarin yadda ake yin aikin cire ƙoda sai ta ji sam ba ta son tafiya, amma ta danne zuciyarta su Mom suka raka su har airport, sai da suka ga jirginsu ya tashi sannan suka dawo gida....

_Maman Nusaiba ce_
[7/17, 1:18 PM] Ummu Amjad: ADZ

49

Cikin takunsa na ƙasaita ya fara saukowa daga cikin jirgin hannunsa cikin nata, ya manna baƙin glass sai wani shan ƙamshi yake, Khadija ta yi lakwas a gefen shi tafiya ma ƙarfin hali take saboda da yadda ta ga irin motocin da suka zo ɗaukar mijin nata, ashe ba ta ga komai ba a Nigeria da motoci shida suka zo tarbar su, domin nan iya wanda ta gani a jere su goma duka baƙaƙe kala ɗaya, ta jinjina kai tana yi wa Allah tasbihi wai ita ce aka zo ɗauka a irin waɗannan motocin da a film kawai take gani. A hankali ta ɗago kai ta kalle tsayinsa iya haƙarƙari ta zo mishi ga ta ƙarama ita ba wani jikin a zo a gani ba, amma ba za ka kira ta da sirriya ba, murmushi ya sakar mata tare da tsayawa ya duƙa ya ce “My wife ya kika ga London?”
Ajiyar zuciya ta sauke ta rasa me za ta faɗa masa sai juya kalaman bakinta take tana taunasu gudun ta faɗi ba daidai ba, ƙara matso da ita ya yi jikinsa ga mutane sun soma taruwa suna ɗaukan su a waya, wasu kuma suna faɗin “super star Mr J.”
Lumshe idanu ta yi a hankali ta ce “Je t'aime mon amour.”
Cak ya ɗaga ta sama ya mata ɗaukan jarirai ya nufi wajen mota, kafin ya ƙaraso da sauri ɗaya daga cikin bodyguard ɗin ta buɗe masa mota tare da yi masa welcome back, murmushi kawai ya sakar mishi ya shige mota. Motocin na tafiya sai ga Jennifer ta shigo Airport ɗin cikin motarta, packing ta yi ta fito da sauri ta nufi wata matashiyar budurwa da ke zaune kan kujera, tana isowa ta ce “Ruby ina suke?”
Tashi tsaye Ruby ta yi tana yatsina fuska ta ce “Ai kin makara ɗazu suka wuce, ba ki ga yarinyar da ya zo da ita ba kyakkyawa ce sosai kuma ƙarama dan kin yi biyun ta a girma, yadda yake mata magana da nuna mata tsananin kulawa ya sa na fahimci tabbas akwai wani abu a tsakanin s..”
Ɗaga mata hannu Jennifer ta yi tana dafe ƙirji cikin tashin hankali da firgici ta fara magana irin ta wanda ya fita daga haiyacinsa.
“Ruby ina jin zuciyata Kamar ta fashe zan mutu, ina mai tabbatar miki in dai yarinyar da kike ba ni labari girlfriend ɗinsa ce sai na kashe ta, duk macen da ta raɓi my start sai ta yi nadama.” Ta ƙarashe maganar da ɗaga muryar hakan ya janyo hankulan mutanen da ke wajen, ganin za ta tara musu mutane Ruby ta kama ta sai sumbatu take ta saka ta a mota suka wuce..

Tun da suka shiga mota ba ta ce komai ba domin ta matuƙar gaji sai lumshe ido take tana buɗewa, shi kuwa Oga waya kawai yake amsawa ta abokinsa yana sanar da su alƙawarin da ya musu gobe zai cika domin ya kawo Khadijarsa da yake faɗa shekaru da dama. Tana jinsa ta yi kamar ba ta ji ba sai yanzu ta tuna maganar Amira lokacin da ta sanar da ita an sa mata rana da Ahmad, murmushi ta yi tana ƙara jin son ƙawartata.
A ƙofar wani gold ɗin get suka hon maigadi ya buɗe musu suka shiga, ba ta ɗago ba har ya fita ya zagayo ya buɗe set ɗin da take ya sa hannu ya fito da ita, wari idanu ta yi ganin girman gidan ya fi na Mom ga kyau ga shukoki kala-kala a harabar gidan, ganin ta tsaya kallo ya kama hannunta suka nufi wata ƙofa. Duk in da suka bi masu aikin gidan sai sun rusuna suna mishi welcome back sir shi Kuma ya tsaya su gaisa sannan su yi gaba, sosai ta ji daɗin ganin yadda yake kula da masu yi masa hidima, idan suka gaishe ta murmushi take ta ce thank you tana ganin abin take kamar almara, wai yau ita ce turawa ke gaishe ta cikin girmamawa suna kiran da ta ma'am?
Chapter 68 · 0% Book details