Sashe 5
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lumshe idanuwansa ya yi wanda suke cike da bacci, gabaɗaya daren jiya bai yi bacci ba saboda abin da Mom ta masa na raba shi da matarsa a cewar shi, dafe saitin zuciyarsa ya yana hasko yadda take masa rashin kunya da lokacin da take saka shi dariya. Buɗe ido ya yi jin yana hello Oga, ajiyar zuciya ya sauke yana son yin magana amma ya kasa kawai ya saki wayar ta silalo ƙasa..
“Hello! Hello! Oga are you OK?” Yake faɗa amma ya ji shuru. Mom na cikin mota saboda iskar da ke kaɗawa da ɗan zafi shi ya sa ba ta san me ke faruwa a waje ba.
Kashe kiran ya yi ya sake kiran shi take ya ɗauka, “Oga.”
“Na'am.” Ya amsa yana saita nutsuwar shi, fita ya yi daga wajen motsa jikin ya nufi ɗakinsa yana faɗin “To kai kana ɗan wajen garin ai abin kunya ne ma a ce ba ka san hanya ba.”
“Ba haka ba ne Oga, ni gaskiya ban taɓa zuwa wannan ƙauyen ba duk da a jaharmu yake.”
Jinjina kai ya yi ya ce “Hanyar da ta bi hannun dama ita za ki, amma kafin nan kira Khadija ka ba ta wayar ina son magana da ita.”
To ya ce ya ƙaraso wajen Khadija da ta yi ture ka ga tsiya ya miƙa mata wayar ya ce “Oga ne zai yi magana da ke.”
A wulaƙance ta kalli hannnunsa sai kuma ta tuna ta ji suna cewa Sultan Oga. Da hanzari ta amsa, tsoron ta ɗaya kar ya canja ra'ayi su kuma mayar da ita wannan gidan da take fatan ko a mafarki ba ta son ganin shi.
“Hello wai ka ce a ba ni waya? To gani me zan ba ka? Ni dai don Allah karka sa su kuma sace ni ina jiyo ƙamshin garinmu.” Ta faɗa tana sakin kuka marar sauti, saboda kewar su Hajja da ke addabar ta musamman da ta ji suna cewa sun kusa zuwa garin nasu sai ta ji zuciyarta ta karaya, ta ƙagara ta ga su Hamma da su Saminu abin kaunar ta..
Runtse idanu ya yi yana jin kukan ta har ƙasan zuciyarsa, in tana masa kuka gabaɗaya tayar masa da hankali take ya ji duk wani kuzarinsa na yin ƙasa. Cikin muryar rarrashi ya ce “Haba my wife ki daina kukan nan kin ji, kuma ba zan ƙara sace ki ba Mom ta ce da kanki za ki so zuwa ba sai na sato ki ba. Idan kuka je kar ki ce wa su Maigari komai kawai ki ce Mom ta tsince ki kin ji ki mini alfarmar.”
Shuru ta yi tana jin saukar maganarsa mai haɗe da fitar numfashi a kunnenta har ya gama, har ta soma hura hanci za ta masa diɓar albarka ta tuna gara dai ta lallaɓa kar ya ƙara sace ta, cikin sanyin muryar da ita kanta ba ta san tana da ita ba ta ce “To ba zan ce komai ba, amma don Allah ni dai ba na son na sake ganin ka.” Ta faɗa tana murguɗa baki kamar tana gaban shi.
Saurin janye wayar ya yi yana jin zuciyarsa na bugawa, sake mayarwa ya yi ya ce “Khadija ni kike cewa ba ki son ki sake gani na? Ni ne fa.”
Hararar wayar ta yi sai kuma ta rufe baki tana kallon Mom da ke danna waya daga cikin mota, a hankali ta matsa daga inda take ta koma jikin bishiya ta duƙa. Murya ƙasa-ƙasa ta ce “Kai wai meye ma my wife ɗin nan da kake faɗa mini? Sannan ni ba suna na Beauty ba Khadija nake ko ka ce Andizo jikar Hajja ko ka ce Dijan mai hankali shirin Allah, kai ko uwar masu gari ka ce daidai ne saura na kuma ji ka ce mini Beauty kamar wata ƴar tagwaye.”
Murmushi ne ya suɓce mishi har tana jiyo sautin shi, wani sanyi ya ji na ratsa shi zafin da ke addabar zuciyarsa na sauka, jin ta soma halin nata ya yi saurin faɗin “Ni dai ki mini alƙawari ko kin je babu ke babu wani saurayi, dama ina so na faɗa miki zan tafi Germany za mu buga wasa a can nan da sati ɗaya, daga can ma za mu yi gaba ina so ki tsare mini kanki karki bari kowa ya ce yana sonki, da zarar na dawo kawai bikinmu za a yi kinga ke mata ta ce. Na so na ɗauke ki mu tafi to Mom ta mini katanga da ke, ina sonki Khadija..” Ya faɗa cikin wani kalar yanayi mai narkar da zuciyar wanda aka furtawa.
Da yake ita ba ta shi take ba tsaki ta ja ta ce “To sai me dan za ka tafi Germany? Ni fa na faɗa maka ba na son ma sake haɗuwa da kai, ka ce darajar ƙanwarka Farrah ita ƙawata ce in ba dan haka ba alƙur'an da sai na ɗan iskan duka kafin mu taho, ko kuma na sa Hammana ya buge mini kai da laggyar.”
Ɗaiɗai ya yi a kan gado yana sauraron ta har ta dasa aya, buɗe idanuwansa ya yi ya janyo pilow ya rungume ya ce “Khadija ni kike cewa za ki a a buge ni?”
A fusace ta ce “Yo kai ɗin a kayan miya mene ne?”
Lura da in suka tsaya dare zai musu ya ce ta ba shi wayar ta miƙa masa tana kumbura baki, kallon ta Farrah ta yi ta ce “Waye kike magana da shi.”
Kama hannunta ta yi suka nufi mota ba ta ce mata komai ba. Mom ta kalli Andizo ta ce “Khadija lafiya na ga kin ɓata rai?”
“To ba shi ba ne yake mini daɗin baki, so yake ya sake sace ni.”
Girgiza kai Mom ta yi suka ci gaba da tafiya..
Sai bayan La'asar suka iso garin lokacin Andizo na bacci ita da Farrah, da tambaya suka nufi gidan Maigari duk da Sultan ya musu bayanin koma amma ya ce su tambaya in sun shigo gari.
Su Maigari suna zaune suka ga mota ta paka duk suka kalli motar, juyowa Mom ta yi ta tashi Andizo, buɗe ido ta yi ta kalli waje ai kuwa ta ga Maigari a zaune wani irin zabura ta yi tana dariya ta tashi Farrah ta ce “Tashi ƙawata ki ga garinmu kinga ga Babana can waiyo daɗi ku buɗe mini na fito.”
Ganin yadda take murna sai ta ba wa Mom tausayi, buɗe wa Mom aka yi ta fito sannan suma ya zagaya ya buɗe musu, da mugun sauri ta fito ta kwasa a guje har tana faduwa ta nufi su Maigari sai kiran shi take da ƙarfi, “Maigari!Maigari!”
Tashi tsaye Maigari ya yi yana kallon yarinyar da take tunkaro shi, sai da ta zo kusa ya ga Andizo ce ya saki baki yana kallon ta har ta iso ta rungume shi ta fashe da kuka..
Kowa na wajen sai hamdala yake, Maigari ya zauna ya janyo Andizo yana shafa jikinta kamar ya yi kuka ya ce “Uwata ina kika shiga mun yi neman ki har mun gaji mun zuba wa sarautar Allah ido.”
Share hawaye ta yi ta ɗago ta kalli Mom da suka tsaya a ɗan naisa da su suna kallon su, har za ta faɗi inda aka kaita sai ta tuna da maganar Sultan ta yi saurin faɗin “Maigari waccan mata ta cece ni ta kawo ni gida ita da ɗiyarta.”
Tashi Maigari ya yi ya kama hannun Andizo suka yo wajen su Mom, sannu da zuwa ya musu sannan ya musu jagora suka nufi ciki.. Suna isa bakin ƙofar gida Andizo ta kwace hannunta daga cikin na Maigari ta nufi gidan da gudu tana kiran su ɗaya bayan ɗaya..
Da sauri Hajja da Inna suka fito jin muryarta, tana dariya ta ƙaraso ta haɗa su ta rungume.
Hamdala suka dinga yi Hajja ta ce “Uwar masu gari Allah ya kwace ki daga hannun azzalumai.”
Dariya ta yi ta sake su ta ce “Wallahi fa Hajja kin ga da su Mom muke tare ga su nan a baya, amma ina su Hammana suke?”
Sannu da zuwa Inna ke yi wa Mom ta ɗauko tabarma ta shinfida musu.
Nan da nan gari ya ɗauka Andizo ta dawo ai kuwa yara suka dinga rige-rigen zuwa ganin ta, duk wanda ya zo sai ya ce ai Andizo ta zama mai kyau, ita kuwa sai murna take tana ba su hannu suna tafawa wasu har shafa jikinta suke wai jikinta ya yi laushi.. Ita dai Mom sai kallon Andizo take sai yanzu ta ji hankalinta ya kwanta da ta dawo da ita ga ahalinta..
Hayaniyarsu ce ta fito da su Giɗaɗo, yana isowa ya hango ta a tsakiyar yara tana ta murna, cike da wani kalar zallar farin ciki ya ce “Surbajon Hamma.”
Juyowa ta yi suka haɗa ido ta nufo shi tana faɗin “Hammana gani na dawo gida na yi kewar ka sosai.”
Ɗaukar ta ya yi yana juyi da ita sai dariya take shima ya yi, sai da Hajja ta musu magana sannan ya sauke ta ta nufo Umar duk ta rungume su suna ta farin cikin ganin ta..
Sai da aka dama wa Mom fura da nono aka kawo mata ruwa mai sanyi a cikin kofin sulba ta ɗan sha, ita kuwa Farrah sai ta ta ji ta ƙoshi sannan ta bari tana faɗin “Mom furar nan akwai daɗi.”
Dariya Andizo ta yi ta ce “Yarinya haka muke yin ta.”
Maigari ya ce “Gaskiya mun yi matuƙar farin ciki da kika ceci rayuwar yarinyar nan, Allah ya saka da alkhairi ba mu da abin da za mu biya ki sai dai mu yi miki addu'a. Uwar masu gari wai su waye suka sace ki?”
Miƙe ƙafa ta yi ta ce “Nima ban san ko su waye ba kawai sai ji na yi an shaƙa mini wani abu daga nan ban sake sanin komai ba sai ganina na yi a wani gida ina tambayar mai aikin kawo mini abinci ta ce wai a Abuja Nigeria nake, to ina nan a tsare kawai sai ga Allah ya kawo Mom ta zo ta ceci rayuwata, shi ne ta dawo da ni gida..”