Sashe 53
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Misalin ƙarfe 11:00am Ahmad ya sauka a ƙauyen su Andizo, ya samu kyakyawar tarba daga wajen Maigari da sauran jama'a, hatta ɗaliban da ya koyawa karatu sai da suka yi comba guda suka zo gaishe shi har da masu kawo mishi girki, hakan ya faranta mishi rai matuƙa ganin yadda yaran ke ƙaunar shi wasu ma daga cikin 'yan matan har an musu aure har da masu haihuwa, mamaki sosai ya sha ganin su Salame an musu aure har da yaronta jariri ɗan wata biyu, yana kallon ta ya miƙa hannu ya amshi yaron tsaf-tsaf da yaron sai ƙamshin mai jarirai yake. Addu'a ya yi wa yaron yana murmushi ya ce “Allah mai girma su Salma an zama Mama.”
Dariya Salame ta yi tana rufe fuska ta ce “Monsieur ai har yanzu ban fasa makaranta ba ina yi, yanzu ma hutu muka samu na kwana goma shi ne na zo gida ziyara.”
“A haba dai? To shi mijin naki yana ina?” Ya faɗa da mamaki kan fuskarsa.
Nuna mishi ta yi ta ce “Shima karatun yake ai tare muke a can Niamey, akwai danginsu a can shi ne muke zaune da su, na so a ce na san gidanku da sai na kai muku ziyara to ban sani ba, har numéro ɗin Andizo na nema ban samu ba amma tun da ka zo don Allah ka taimaka ka ba ni numéro ta ina so na kai mata ziyara mu ga juna.”
Jinjina kai Ahmad ya yi sosai Salame da mijinta suka birge shi, numéro Andizo ya ba ta sannan ya miƙa mata yaro ya sa hannu a aljihu ya ciro 'yan jika biyar guda huɗu ya miƙa mata ya ce “Ga shi a saya wa bèbè(Baby) madara.”
A kunyace ta amsa ganin kuɗi mai ƴar dama ta mishi godiya ita da mijinta sannan suka tafi. Bayan kowa ya watse Ahmad ya huta ya ci abinci sannan ya nufi su Maigari domin gabatar da abin da ya kawo shi, sai da ya gama tsara duk maganar da zai fara tukun ya shiga cikin ɗakin Maigari. Murmushi Maigari ya yi yana nuna mishi wajen zama, zama ya yi ya gaishe da Maigari ya amsa yana faɗin “Ya su Musan da fatan duk kuna lafiya? Ya, wajen Hajiya ?”
Sunkuyar da kai ya yi ya ce “Duk suna nan cikin ƙoshin lafiya sun ce a gaishe ka har Khadija.”
“To ma sha Allah ina amsawa ita uwar masu gari yaushe za ta zo ne? Ta ce mini fa za ta zo mana ziyara kuma naji shuru.”
Murmushi ya yi yaba rausayar da kai ya ce “E jarabawa garesu a makaranta shi ya sa ba ta zo ba, amma da an musu hutu ni da kaina zan kawo ta.”
“Madalla.” Cewar Maigari, gyara zama ya yi sannan ya fara gabatar da maƙasudin zuwan nashi. “Maigari dama na zo ne a kan maganar da muka fara da kai ta waya kwanakin baya, to yanzu mun gama komai su Abba sa su zo a su nema mini auren Khadija.”
“Kai madalla gaskiya naji daɗin wannan abu sosai, ai dama tun tuni na fara maka babu wata matsala in dai kun shirya a tsakanin ku za mu fi ku ma jin daɗin haɗin, yanzu abin da za a yi idan ka je gida ka sanar da s Musa sai su sa lokaci ko nan da sati ɗaya ne sai su zo a ɗaura aure, ba ba son a sa bikin ya yi nisa.”
Daɗi sosai ya mamaye zuciyar Ahmad ya ce “In sha Allahu Maigari zan sanar da su, amma ya kamata a sa ko wata biyu ne saboda a yi gyare-gyare a gidan nawa, idan sun zo kawai ka sa wata biyu.”
Jinjina kai Maigari ya yi ya ce an gama hakan za a yi tun da ya fi so a kai bikin nasu har nan da wata biyu,godiya sosai ya yi wa Maigari ya aje mishi kuɗi mai yawa sannan suka fito. Sai da ya shiga ciki suka gaisa da su Hajja suna ta wasa sai ga su Umar, gaisawa suka yi suna ta tambayar su Andizo da yaranta ya amsa musu da lafiya lau suke suna nan zuwa su kawo musu ziyara. Har bakin mota suka raka shi Giɗaɗo ya dubi Ahmad bayan su Umar sun wuce ya ce “Ungo ka sa mini numéro ɗin Surbajo ina son yin magana da ita.”
Sai da ya kalli shi ya kuma kalli sabuwar wayar da yake miƙa mishi sannan ya ce “To shi kenan bari na sa maka.” Sa mishi numéro ɗin ya yi suka sallama ya tafi shima ya ja motarsa ya bar ƙauye cike da farin ciki.
Yana komawa gida ya sanar da Abba maganar, sanin yanzu suna ganin tsakanin su har hira suke sai ya yi farin ciki da wannan maganar, ya ce in sha Allah za su je shi da Abie. Bayan kwana biyu suka shirya tsaf har da abokansu suka isa ƙauyen su Andizo in da suka samu kyakkyawar tarba, sai da suka huta suka ba da duk wani abu da ake yi na neman aure sannan aka sa bikin nan da wata bi kamar yadda shi mai gayya mai aiki ya ce, haka suka dawo gida cikin farin ciki suna jinjina halin dattijantaka irin ta Maigari akwai son jama'a.
Da dare duk bayan sun gama cin abinci sun dawo palo Abba ya yi gyaran murya ya ce “Khadija su Maigari suna gaishe ki.”
Murmushi ta yi tana wasa da 'yan yatsun ƙafarta sam yau ta kasa samun kwanciyar hankali tun da Ahmad ya sanar da ita jiya ya je neman izinin auren ta wajen su Maigari, da kyar ta yi bacci domin ita Allah ya ga zuciyarta babu soyayyar Ahmad a ciki duk da kuwa yanzu yana nuna mata soyayya da kulawa, idan kuma ta tuna da ta auri mazinaci dan shaye-shaye wanda ko sallah ba ya yi gara dai ta zauna da Ahmad ɗin shi nashi mai sauƙi ne ta san halayensa..
Taɓa ta da Hassana ta yi ya sa ta firgita tare da ɗago kai ta ce “Abba me ka ce?”
Ƴar dariya ya yi ya ce “Tunanin me kik haka muna ta miki magana kin yi shuru?”
“Ba komai Abba kawai dai ina son ganin su Khadija ne da su Hajja, ina so na tafi da su can idan mun samu hutu.”
Murmushi Abba ya yi yana faɗin “To Allah ya kaimu su kuma yara zan sa Ahmad gobe ya tafi Diffa ya kawo miki su sai ku tafi tare, dama ina sanar da ke an sa ranar bikin ku ke da Ahmad wata biyu masu zuwa, da fatan babu wata matsala ko? Idan kuma akwai ki sanar da ni karki ɓoye mini komai ni ɗin tamkar mahaifinki nake karki duba sukunta kin ji, ko ba ki aure ɗana ba zan riƙe ki saboda mun zama dangin juna.”
Sunkuyar da kai ta yi ƙasa nan da nan idanuwanta suka cika taf da ruwa ta yi jarumtar riƙe su, zuciyarta ta kasa aminta da maganar auren nan amma sai ta dinga jero addu'o'i ko za ta ji sauƙi, idan ta ce ba za ta auri Ahmad ba gani take tamkar ta yi wa su Abba butulci, ita kuma ba ta son a ce yau ita ce ta ɓata ran mutanen da suka gyara rayuwarta. Da kyar ta haɗiyi yawu sakamakon maƙoshinta da ya bushe, a hankali ta ce “To Abba Allah ya kaimu.” Tana faɗin haka ta tashi da sauri ta wuce ɗaki Ahmad ya bi bayan ta. Dariya Hassana ta yi suna tafawa ita da Hussaina ta ce “Kan bala'i! Tom and jerry za a zama miji da mata wai.”
Dariya duk suka yi Mamma ta j dogon numfashi ta ce “Wallahi ni duk na fi ku ji farin cikin wannan haɗin, a baya da ta ƙi ina ta tunanin wacce yarinya Ahmad zai je ya kwaso mana? Ya halayenta suke? Amma yanzu Alhamdu Lillah naji daɗi matuƙa Wallahi.”
Kowa murna yake ana ta sa albarka.
Tana shiga shima yana shiga ya dafa kafaɗarta a sanyaye ya ce “Khadija mene ne yake damun ki? Kin san dai abin da likita ya ce ki daina yawan tunani ko? Nasan Yaya Salim kike tunawa kina ganin kamar kin ci amanar, ki kawar da wannan tunanin babu abin da ya yi kama da cin amana a auren da za mu yi, kinga zan ɗauke ke ki mu tafi Diffa can Abie ya samo mini aiki kinga za kike zuwa gidan Umma kullum ni zan ke kaiki ma.”
Hawayen da take riƙewa ne suka samu damar zubowa, gaban ta ya dawo yana kallon ta da wani irin yanayi ya ce “Ki yi haƙuri kin ji na takura miki da surutu ko?”
Girgiza kai ta yi ta tsayar da hawayen tana rarrashin zuciyarta ta ce “Ba komai kawai dai naji abin ne banbarakwai wai na auri ƙanen mijina.”
“Ki daina irin wannan tunanin Khadija ba shi da amfani, ina so ki ba ni dama kafin lokacin auren mu zan saka ki cikin farin ciki ta yadda za ki yarda da cewa ba auren cin amana muka yi ba, kin ba ni dama daga yau?”
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce “E na ba ka Yaya Ahmad.” Ta ƙarashe maganar tana sakin marayan kuka, hannunta ya janyo ya rungume ta abin da ba ta yi zato ba har za ta ture shi sai kuma ta kasa. Bubbuga bayanta ya dinga yi yana nusar da ita irin son da yake mata tun ma kafin Salim ya ce yana son ta, da yadda ya shiga damuwa bayan auren ta da Salim har ya samu ya kawar da komai ya ci gaba da harkar gaban shi. Sai da ya ga ta yi bacci sannan ya bar ɗakin ya ƙudiri aniyar zai faranta mata rai sosai ya ba ta kulawa kafin wata biyun su cika, ya watsar da duk wani musguna mata da ya ce zai yi idan ta shigo gidansa.