← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 75

Sashe 67

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Daret dinner suka nufa Mom na ganin su ta kalli Sultan da ya ƙi sakin hannunta sai mutsu-mutsu ya sake ta ya ƙi, hararar shi ta yi ta ce “Wai ba za ka sake mata hannu ba?”
Sakin hannun nata ya yi ya ja mata kujera har za ta zauna sai ta fasa ta dalla mishi harara ta dawo kusan Mom ta ce “Mom ni a kusa da ke zan zauna.”
Baki ya saki yana kallon ta cik da mamaki Sultana ta sheƙe da dariya ta ce “An gaishe da Anty amarya.”
Kujerar kusa da ita Mom ta ja mata ta zauna, ɗaure fuska ya yi ya zauna suka fara cin abinci. Kasa cin abincin ya yi sai cokalin yake juyawa yana kallon ta ta gefen ido, duk abin da yake tana lura da shi ta sunkuyar da kai ta ci gaba da cin abincinta.
Mom ta fara tashi ta wuce gabaɗaya ma ta bar palon, ganin Mom ta tashi ya dawo kujerar da ta tashi ya tura mata abincinsa, Doctor Rahama ta miƙe tsaye tana goge baki ta kalli su Sultana ta ce “Kunga ku tashi ku bar masoya su ci abinci.”
Tashi suka yi suna tsokanar su Andizo ta yi shuru har suka bar wajen, wani kallo ta mishi da ya sa shi lumshe ido ta ce “Daddyn Farrah me ya sa ba ka ci abinci ba?”
Ƙara tura mata abincin ya yi kamar wani ƙaramin yaro ya ce “Ni ke za ki ba ni.”
Waro ido ta yi sai kuma ta turo baki a shagwaɓe ta ce “Gaskiya ni ka yi ƙato dayawa.”
Tashi ya yi tsaye ya ce “OK to ba zan ci ba.”
Da kallo ta bi shi ya juya nufi sama, janye idanunta ta yi daga kallon shi tana mamakin yadda yake mata wasu abubuwan kamar ƙaramin yaro daga jiya zuwa yau. Tashi ta yi ta nufi sama, har ta yi nisa sai kuma ta juyo tana tunanin anya ta kyauta wa mijin nata kuwa in ta bar shi ya kwanta bai ci abinci ba? Girgiza kai ta yi ta ɗauki plate ɗin abincin ta wuce.
A hankali ta buɗe ƙofar ta shiga da sallama, a kan gado ta ganshi kwance ya yi ruf-da-ciki ta aje abinci a kan carpet ta tsaya a kan shi.

“Daddyn Farrah tashi ka sauko in ba ka abincin da hannuna ba ma da cokali ba.”
Yana jin ta ya yi kamar mai bacci sosai ya ji daɗin yadda ta biyo shi da abincin, ganin ya ƙi motsawa ta hayo kan gadon ta leƙa fuskarsa ta soma bubbuga mishi kumatu, “Daga shigowa har ka fara bacci ka tashi mana.”
Miƙa ya yi irin kamar mai bacci gaske ya matso ya kwanta a kan cinyarta, hannunta ya kamo ya ɗora a kansa yana yawo da shi, gane abin da yake nufi sai ta shiga shafa sumar, a sayayye ta kuma cewa “Abincin fa.”
Sai a lokacin ya iya cewa da ita “Tea kawai zan sha.”
Ture shi ta yi tana sauka daga kan gadon ta ce “Tea? Ba dai yanzu ba sauko ni bacci nake ji.” Ta faɗa irin ba wasa ɗin nan, dariya ta so ba shi ya fisge ya tashi ya sauko ta harare shi.
Zama ta yi ta wuce toilet ta wanke kannunta ta dawo ya gyara zama, abincin ta dinga ɗiba tana ba shi a baki idan ta sa mishi sai ya haɗa har da yatsunta ya tsosa son ransa sannan ya sakar mata yatsun, banza ta yi da shi ta ci gaba da b shi har ya ƙoshi ta miƙe ta dauki plate ɗin za ta fita ya yi saurin ruƙo ta.
“Ina za ki je?”
“Zan mayar da plate ɗin ne.” Ta ba shi amsa a taƙaice tana ƙoƙarin kwace ruƙon da ya mata.
“No dawo ki aje mu kwanta ba yanzu ba.”
Har za ta ce ba za ta dawo ba sai kuma ta tuna irin jan kunne da doguwar nasiha mai ratsa jiki da Umma matar Abie ta yi mata a waya, haka ma Mamma ta yi mata nasiha sosai game da yi wa miji gardama ko faɗa mishi magana kai tsaye, ta so ta botsare ta ce ta fasa auren ta gudo, amma ganin yadda Mom da 'yan'uwan Sultan ke tarairayar ta sai ta ji jikinta ya yi sanyi. Ajiyar zuciya ta sauke ta dawo ta aje plate ɗin ta bi shi zuwa toilet, tsaye ta same shi yana sa makilin a broch ta yi shuru kamar ba ta shigo ba. Sai da ya gama goge ya juyo ya ganta murmushi ya sakar mata itama ta mayar masa da martani, hannunta ya kamo ya kawo bakin famfo ya wanke mata ya ɗauko broch sabo ya sa mata makilin ya nufi bakinta ta yi saurin kaucewa.
“Ya kika kauce My wife broch ba za miki.”
Wani kallo ta mishi ta ce “To shi kenan komai sai ka ce sai ka mini har broch ɗin ma?”
“Sosai ai duk wani abu ni zan ke miki shi kema kina yi mini, hakan zai ƙara mana so da ƙaunar junanmu kuma wannan shi ake kira da kyautata a zamantakewa, matso na miki kar mu tsawaita magana a toilet.”
Matsowa ta yi ya ce ta buɗe bakinta, sai da ta harare shi sannan ta buɗe ya goge mata. Bayan sun fito ya ciro mata Sleeping dressing ring da wando, rigar iya ciki wandon bakin gwiwa, ta yi sororo tana kallon kayan sai Salim ya faɗo mata a rai, ba za ta manta ranar da ya taɓa ba ta sleeping dressing irin wannan ta ce ita ba ƴar iska ba ce ba za ta sa ba, ya yi ta dariya yana rokon ta ta amsa ta sam ita fa ba ƴar iska ba ce, haka suka dinga zagaye ɗaki har ya ci sa'ar damƙo ta ya sa mata ai kuwa ta tayar ta aljannu dole ya cire mata ya barta da wanda take so.
Kumatunta ta ji ana shafewa ta ɗago kai suka haɗa ido, girgiza mata kai ya yi ganin hawayen abar ƙaunar tasa duk sai ya shiga damuwa, a sanyaye ya soma tambayar ta, “My wife why are you crying?” Ya faɗa yana ƙara share mata hawaye.
Ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin mayar da kukan da yake son kubce mata amma ta kasa, fashewa ta yi da kuka mai ƙarfi ta faɗa jikinsa, hankalin Sultan ya yi matuƙar tashi sai ƙara rungume ta yake yana bubbuga bayanta, ganin tsayuwar ba za ta musu ba ya ja ta suka koma kan gado ya kwanta ya dora ta a kanshi yana rarrashin ta kamar shima zai yi kukan.

“My wife don Allah ki daina kukan nan yana tayar mini da hankali, idan wani abu ne na miki wanda ya ɓata miki rai ba kuka ya kamata ki yi ba faɗa mini za ki sai na gyara, ko ba ki da lafiya ne?” Ya ɗago da ita.
Ganin yadda ya damu sai ta tsayar da kukan ta yi shuru ba ta mishi ko uffan ba, sake mayar da ita ya yi jikinsa. “Am sorry kin ji ki faɗa mini abin da yake damun ki, kinga ke amana ce a hannuna babu irin kashedin da Ahmad bai mini ba a kan na kula da ke fiye da kaina kar na bari ki yi kuka sai ga shi daga zuwan mu kin fara kuka me ya faru ?”
Tashi ta yi zaune ta shafe fuskarta shima ya tashi ya fuskance ta, a hankali ta ce “Wani abu ne na tuna shi ya sa ni yin kuka, sannan ina son ganin yarana tun da aka ɗauke su ni da su sai dai a waya don Allah ka sa Yaya Ahmad in za su zo su kawo mini su na gansu ko na kwana ɗaya ne.” Ta ƙarasa maganar murya na rawa.
Tausayi ta ba shi ya ya kama hannunta ya ce “In sha Allahu in dai dan su Nour ne za ki gansu da zarar sun shirya zuwa nan zan faɗa masa ya je ya kawo miki su ki gansu, ki daina tunanin komai na miki alƙawarin zan faranta miki fiye da tunaninki, ban sani ba ko tunanin marigayin mijinki kika yi har kika yi kuka, amma ba komai zan kyautata miki iyakar iyawata ko na ce fiye da Salim ma.”
Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai ya dora da cewa “Yes ba lefi ba ne dan kin yi tunanin Salim in ya faɗo miki a rai, mutumin da ka rayu da shi na sati ko wata ya kyautata maka ba za ka taɓa mantawa da shi ba, ballantana kuma wanda kuka kasance a karkashin inuwa ɗaya ai ba abin mantawa ba ne, amma don Allah karki cika yawan tunani irin haka gudun ya kawo miki matsala a zamanmu.”
Shuru ta yi tana sauraron shi har ya dasa aya, gyara zama ta yi ta ce “In sha Allahu hakan ba za ta sake faruwa ba, nima zan yi ƙoƙarin yin maka biyayya iya bakin ƙoƙarina duk da har yanzu hankalina ya kasa kwanciya a kan zamana matarka.”
Dariya ya yi ya ce “Y kamata na sanar da ke komai kar ki kasa yin bacci.”
Gyara zama ta yi domin ta ƙagara ta ji yadda aka yi.”
Chapter 67 · 0% Book details