Sashe 33
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon shi su ya yi sannan ya ɗora da cewa “Ku biyo ni ina buƙatar ganin ku.” Ya faɗa yana yin gaba.
Su uku suka bi shi Mamma, Abba, Ahmad har office ɗin sa, takardun da ke ɗauke da result ɗin Salim yake kallo yana girgiza kai, hakan ya sa gaban Mamma ke bugawa da mugun sauri ta kai hannu ta dafe saitin zuciyarta, Ahmad ya riƙe mata hannu yana nuna mata ta nutsu. Bayan ya gama ya yi gyaran murya ya soma musu jawabi, “Maganar gaskiya wannan bawan Allah yana cikin mawuyacin hali, duk wanda yake ɗauke da irin wannan raunukan da su karaya gaskiya ba lalle a kawo shi har asibiti yana cikin haiyacinsa ba, amma shi tun da aka ƙare mishi aiki sunan wata ya dinga kira wai ita Khadija, ko kuma ya ce ko Amina ko wa..”
Ajiyar zuciya Ahmad ya sauke ya ce “Likita yanzu wani irin raunika da karaya ne ya samu haka masu muni?”
Takardar ya ɗauka yana kallo ya ce “To abu na farko dai ƙashin haƙarƙarinsa biyu sun karya, ga harsashi da aka fitar masa a fegen cikinsa guda biyu, sannan ya samu buguwa a kansa sosai in da har wajen ya yi rami mai zurfi amma Alhamdu Lillah ƙwaƙwalwarsa ba ta taɓu ba, ƙafarsa ta ji 'yan raunuka, abu na ƙarshe kuma muna buƙatar jini mai yawa wanda zai yi leda uku, domin ya zubar da jini fiye da tunaninku a yi maza-maza a nemo jini a fara sa mishi, tukun ku sayi wannan magungunan da allurori wanda za a sa mishi su kashe masa raɗaɗin ciwo da zugin da jikinta zai yi in ya farka..”
In ban da Inna lillahi babu abin da Mamma ke faɗi hawaye na bin kuncinta, godiya suka mishi Ahmad ya amshi takardar ya kama Mamma suka fito, daret shi ya wuce wajen amso magani da kuma inda za a dibi jininsa su kuma suka koma inda suka baro su Hajiya Babba.
Yana zuwa ya miƙa takarda take suka miƙo masa domin likitan ya kira ya musu bayanin komai shi ya sa suka haɗa mishi da ya zo suka ba shi, da mamaki ya amsa ya zaro kuɗi ya miƙa musu ya yi saurin nufar ɗakin ɗaukan jini, har ya kusa zuwa wani tunani ya faɗo mishi ya ciro wayarsa ya kira Abdoul ya ce ya same shi a ɓangaren ɗaukan jini, Abdoul ya ce to ya sauke wayar ya sake gargadin sojojin da su kula kar su yarda wani ya zo ya ce zai shiga suka amsa da to sannan ya tafi.
A bakin ƙofa ya same shi suka shiga tare, Abdoul ya fara shiga shi ya zauna yana jira ya ji me za su ce, gabaɗaya jikinsa ya yi sanyi sai yanzu yake Allah wadai da shan sigarin da ya dinga yi a shekaru biyu baya da suka wuce, tunani kala-kala suka dinga fareti a ƙwaƙwalwarsa, addu'a kawai yake yana fatan jinin Abdoul ya zo ɗaya da na Salim in kuwa ba su zo ɗaya ba to sai dai su saya.. Fitowa Abdoul ya yi jiki a sanyaye ya kalli Ahmad ya ce “Sun ce nawa bai zo daidai da nashi ba kawo maganin kai ka shiga.”
Miƙa mishi ya yi ya shiga da sallama ta amsa, zama ya yi a kan kujera aka zuƙo jininsa aka ɗauki na Salim aka fara aunawa, shuru ya yi yana jin faduwar gaba Allah-Allah yake yana fatan kar a ce jininsu bai zo ɗaya ba, ko kuma ya zo ɗayan su ce shi yana shan sigari wanda tuni ya gane kuskuren da yake aikatawa ya daina ya tuba, amma yau ya ƙara jin tsanar shaye-shaye fiye da kowacce rana ba ya so a ce jininsa da Salim sun zo ɗaya kuma su gano ya taɓa shan wani abu..
“Yawwa Alhamdu Lillah naka da nashi sun zo ɗaya yanzu za mu ɗauki leda uku, domin na ga kana da jini sosai.”
Da sauri ya buɗe ido yana kallon nurse ɗin cike da farin ciki ya ce “Ko ya fi haka kuke so likita ku ɗauka.”
To ta ce mishi ta nemo jijiyar ɗaukan jini ta soma ɗauka, bayan ta gama ta sa mishi auduga a wajen ta ɗauki jinin suka fito tare.
A bakin kofa ta dakatar da su Abdoul ta miƙa mata maganin da suka sayo ta yi ciki da shi..
Tun da suka zo Andizo duk son ta da kuka kasawa ta yi, saboda idanuwansa sun soye sai kukan zuci take, burinta bai wuce ta ga Salim ya fito daga ɗakin ba yana mata murmushi tare da buɗe mata hannaye kamar yadda ya saba ta zo su rungume juna, juyar da kai gefe ta yi tana sauke ajiyar zuciya.
Suna nan zaune sai kusan La'asar aka ba su damar ganin Salim shima sun ce da bibbiyu za suke shiga kar su yi yawa a ɗakin, sun samu ya yi bacci kuma kar hayaniyarsu ta tashe shi.
Abba da Mamma da Hajiya Babba suka fara shiga, yadda suka ga an jona mishi na'urori abin ya girgiza su sosai iya fuska da hannnunsa ne kawai ba a sa mishi bandeji ba, Mamma ta matso kusan gadon da sauri tana zubar da hawaye ta shafa fuskarsa da ta yi fayau, addu'oʼin samun lafiya ta dinga tofa mishi tana shafa mishi a fuska, bayan sun gama suka fito Hassana da Hussaina suka shiga, da kyar suka tsayar da kuka suka mishi addu'a ganin halin da yayan nasu yake ciki abin ya mugun ɗaga musu hankali matuƙa, bayan sun fito Ahmad ya shiga shi da su Aminatou har Abdoul..
Tana hango shi ta kwace hannunta da ke cikin na Aminatou ta nufo shi da sauri, har za ta sa kuka ta tuna batun likita sai ta rufe bakinta ta dinga kuka tana kallon shi, a hankali ta matso kusa da gadon ta kai hannu ta taba fuskarsa tana faɗin “Allah ya ba ka lafiya mai hankali, wannan wani irin ciwo ne haka duk aka naɗe ma jiki da bandeji? Ya Allah ya dubi maraicina ka ba wa wannan bawan naka lafiya, Allah kaine gatan kowanni bawa amma akwai wanda a duniya yake jiyar da kai daɗi har ka kira shi da gatanka to wannan shi ne gatanmu ni da Adda da ma sauran 'yan'uwansa Ubangijin talikai ka ba shi lafiya.” Ta ƙarasa tana goge hawayen da suka zubo mata, gabaɗaya duniyar ta mata zafi fiye da jiya ganin shi a wannan halin.
Aminatou ta tsaya a ɗayan gefen itama kamar yadda Andizo ta yi addu'a haka ta mishi tana kallon shi cikin alhini da damuwa mai yawa. Bayan sun gama Ahmad ya ce su fito ai kuwa Andizo ta ce ba ta san wannan zancen ba ita a nan za su zauna ita da Aminatou su yi jinyar mijinsu, da kyar da dabara ya fito da ita tana kuka..
Sai ƙarfe 10:pm Ahmad ya ce su tafi gida da safe sun dawo, ba dan sun so ba suka shiga mota Abdoul ya sa ɗaya daga cikin sojoji ya kaisu gida.
Tun da suka isa gida mai aikin su ta kawo musu abinci ba wanda kalli ko wajen da abincin yake bare ma su ji za su iya ci, ƙarshe ma duk ɗaki suka shige ta bi su da kallo ita kanta yau wuni ta yi a gidan tana tunanin halin da Salim ɗin yake ciki, abincin ta ɗauka a kula ta nufi ɗakin Andizo ta kai mata sai ta samu ba ta ciki, ajewa ta yi ta fita tana jin tausayin ta..
Ranar a gidan babu wanda ya yi baccin kirki kusan kwana suka yi suna jera nafila suna mishi addu'a, Andizo kuwa tun da ta kwanta a gado kasa tashi ta yi saboda zazzaɓi da ciwon kai sun mata rufdugu, idan ta ci kuka ta gaji ta yi shuru tana kallon samar ɗakin tana tuna yadda yake ririta ta kamar ya mayar da ita ciki, da tunanin hakan ya zo mata sai ta fashe da kuka ta kudundune a cikin fargo, sai da ƙarfe uku ta yi ta lallaba da kyar ta sauka a gadon, da bin bango ta shiga ta ɗauro alwala tana hucin zazzaɓi..
Jiki na rawa ta tayar da iƙama, tun tana yi a tsaye har ta kasa jure tsayuwar ta zauna tana yi daga zaune, sai da ta ji alarm ɗin wayarta ya buga ƙarfe huɗu da rabi sannan ta yi raka'ar ƙarshe, a sujjadar ta dinga jero wa mijinta addu'ar samun lafiya tana yi tana kuka. Bayan ta salamce ta ci gaba da jan carbi har aka kira Sallah ta gabatar, bayan ta gama ta ji yunwa na neman illata ta babyn cikinta sai motsi yake, hannu ta sa ta dafe cikin tana zubar da hawaye tuna duk asuba kafin ya tafi masallaci sai ya dafa cikin ya yi mata addu'a..
Tashi ta yi ta kyar tana bin bango ta buɗe abincin ta ga ciwo ne da miyar taushe, yau duk san ta da tuwo ji ta yi ba za ta iya ci ba ta rufe nufi waje.
Da kyar ta haɗa ruwan tea ta ɗauko fito ta shige ɗaki, shayin ta shanye ta sha magani sai ta ji kamar za ta iya cin abincin ta janyo ta buɗe, loma uku ta yi ta ji amai na neman zuwa ta haƙura ta rufe abincin tana nishi ta wuce banɗaki, wanke baki ta yi fito tana jin cikints na wani irin juyawa ta dafe ta iso kan gado ta kwanta..
Hayaniyar su Hassana ce ta tashe ta ta sauko ta je ta wanke baki da fuska ta sako hijabi ta fito, kowa ya shirya suka dunguma zuwa asibiti..
Yau ma har suka gama zama bai farka ba hakan ya kara tayar wa da Andizo hankali ta yi ta kuka suna rarrashin ta, ita kuwa Aminatou su Ummi suka zo ta zauna a wajen su Ummi na rarrashin ta.
Dangi da 'yan'uwa na zuwa duba Salim har da makotan su Mamma duk sun zo.