← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 75

Sashe 71

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A daren ranar ma ba ta samu bacci kirki ya takura mata sai da ta dinga mishi kuka sannan ya rabu da ita, zafafan kalaman soyayya babu irin wanda bai faɗa mata, ji yake kamar ya mayar da ita ciki dan so da ta yi motsi dai ya ƙara kankame ta yana rarrashin ta.
Washegari da safe karfe goma da rabi suka shirya zuwa hospital inda za a yi mishi aiki, tun da suka shigo mota tana maƙale a jikinsa ban da kuka babu abin da take, gabaɗaya tsoro ya mamaye mata zuciya gani take kamar in ya shiga ɗakin tiyata shima sai dai a fito mata da gawar shi. Suna packing a harabar asibitin ya ɗago ta fuskarsa ɗauke da damuwa ya ce “My wife kukan ya isa haka kina sagar mini da kwarin gwiwa, ki yi min addu'a ayi aikin nan lafiya karki sa nima na fara kukan.” Ya ƙarashe maganar yana share mata hawaye.
Daina kukan ta yi ta riƙe fuskarsa tana kallon shi wasu hawayen suka zubo ta fara magana cikin raunanniyar murya.
“Amour Wallahi tsoro nake ji ba na son kaima ka tafi ka barni, ka yi mini alƙawarin za ka fito lafiya.”
Kai kawai ya jin mata yana mayar da hawayen da suka cika mata idanu, fita suka yi yana riƙe da ita har office ɗin babban likitan in da ya musu tarba ta musamman.
Suna zaune aka koma haɗa komai na aiki wata doctor ta shigo ta sanar da babban doctor komai da ya zama ready su ake jira, Sultan na tashi ta miƙe ta riƙe shi tana kuka ya yi ta rarrashin ta amma taƙi yarda ta sake shi, sai da aka kira ɗaya daga cikin nurses ta riƙe ta ƙarfi sannan suka fita.

Jiki ba kwari suka shiga wani ɗaki aka ba shi kayan marassa lafiya ya saka, zama ya yi aka fara mishi allura biyu a kowanni hannu sannan suka fara mishi gwaje-gwaje. Da sauri doctor ɗin ke duba Shi ta ɗago ta kalli babban doctor, tambayar tw ya yi me ke faruwa ta dakata daga aikin da take?
Kai ta girgiza sai kuma ta sake mishi gwaji ta ja baya ta zauna a kan kujera, gabaɗaya duk sai ta sa likitocin jikinsu ya yi sanyi suka tambayar ta abin da ta gani game da gwajin da ta yi. Ba ta ba su amsa ba ta cire mishi duk wata na'urar da aka jona mishi, abin da ta gani ta nuna wa babban doctor Shi kansa ya girgiza da ganin abin da gwajin ya nuna, umarni ya ba su su janyo gadon da Sultan ke kwace wanda tuni bacci ya ɗauke shi,suka fita da shi zuwa wani ɗaki wanda ya fi wannan kayan aiki aka ɗora shi a wani baƙin gado tare da sa mishi wata hula mai aiki da lantarki duk suka koma gefe suka bar babban doctor....

_Maman Nusaiba ce_
[7/20, 12:06 AM] Ummu Amjad: ADZ

50

A kan idanunta aka fito da shi daga ɗakin tiyata zuwa ɗayan ɗakin sai ta muƙe zumbur za ta bi su, har ta kusa zuwa ta ji an kira sunanta ta tsaya cak a wajen har sai da aka sake kiran ta sannan ta juyo. Limat ta gani ita da Taufiƙ tsaye a inda ta tashi, a hankali ta tako ta iso har gaban su ta kalli Limat idanuwanta sun cika da ruwa, baki take motsawa tana son yin magana amma ta kasa, hakan ya sa ta kama ta ta zaunar cikin sigar rarrashi ta dinga magana.
“Am sorry kin ji babu abin da zai same shi in sha Allah za a yi aiki lafiya, ki yi mishi addu'a.”
Kasa riƙe kukan da ya zo mata ta yi ta rufe baki dinga yin shi marar sauti, sosai ta ba su tausayi Taufiƙ ma ya zauna suka ci gaba da rarrashin ta har suka samu ta daina kuka amma idanuwanta a kan kofar ɗakin da yake ciki.
Zuwa can sai ga Doctor ta fito ta yo inda suke, ta miƙe da sauri jikinta na ɓari tun kafin ma ta fara magana ta riga ta, “Doctor kar dai ki ce mini ya rasu? Idan ya mutu nima bin shi zan yi don Allah ki taimaki rayuwar marainiyar Allah.”
Janyo ta Limat ta yi ganin ta fara fita daga haiyacinta suka bi bayan Doctor zuwa office ɗin babban likita. Suna isa duk suka zauna ya dube su yana murmushi sai ta saki baki tana kallon shi, bayan ya gama rubuce-rubuce a kan takardar da ke ƙunshe da bayanan cutar Sultan ya ɗago ya kalle su, duk zuba mishi ido suka domin sun ƙagara su ji me zai faɗa musu ita kanta Limat jikinta ya yi sanyi, gyara zama ya yi sannan ya fara musu bayani.
“Gaskiya na yi matuƙar mamaki game da Mr J ban taɓa jin karo da majinyaci irin shi ba.”
Saurin katse shi Taufiƙ ya yi, “Doctor me yake faruwa da abokina? Ka mana bayani kai tsaye domin zuƙatanmu su samu sauƙi.
Murmushi ya yi a karo na biyu ya ɗora da cewa, “A wancan satin da ya zo na faɗa mishi ya yi maza ya dawo London domin ƙodarsa ɗayar ta lalace, da farko ya ƙi yarda da abin da na fara mishi sai da ya je Nigeria ya kwanta ciwo nan suka tabbatar mishi matuƙar ba a cire ƙodarsa ɗaya ba to za ta iya harbar ɗayar itama ta kamu da cuta, idan hakan ta faru kuma akwai gagarumar matsala. To yanzu yau da ya dawo mun kai shi ɗakin tiyata har an gama mishi allurori an haɗa komai na aiki, da doctor Julie ta yi gwaji sai abin ya firgita ta, ni kaina da na gani sai na kamu da mamaki ta ya mutumin da ƙodarsa ta lalace a zo za a mishi aiki kuma a samu lafiyar su ƙalau babu wannan cutar ko ƙwaya ɗaya, shi ya sa muka fito da shi zuwa ɗakin miƙe gwaji na musamman amma duka abu ɗaya ya nuna mana lafiya yake babu komai a jikinsa.”
Kallon juna Taufiƙ da Limat suka yi a tare suka ce “To ya aka yi haka?”
Girgiza kai ya yi ya miƙa musu takardar ya ce “Ni kaina ban sani ba amma abin ya girgiza ni sosai.”
Andizo ta ɗaga hannu tana dubar da hawayen farin ciki ta ce “Alhamdu Lillah Allah na gode maka da addu'a ta ta karɓu, Allah ka ƙara wa mijina lafiya ka kare shi.”
Amin suka ce suka tashi cike da farin ciki suka nufi ɗakin da yake kwance.
A tare suka shiga ɗakin duk ta ƙagu ta ganshi, kwance suka same shi ta yi saurin ƙarasawa bakin gadon tare da sunkuyawa ta manna mishi kiss a goshi ta sa hannu tana shafa kwantacccan gashin kansa, Limat ta ja mijinta suka iso ta ce “To Laila da Majnun sai ki daina kukan tun da ba a farke miki cikin miji ba.”
Dariya mai sauti ta yi tana goge fuskarta da hijabi za ta yi magana ta ga ya fara motsawa, hannunsa ta riƙe tana faɗin “Sannu Amour.”
A hankali ya fara buɗe idanuwansa tun yana ganin dishi-dishi har ya washe, Taufiƙ ya matso kusa da shi yana jera mishi sannu. Taimaka mishi ya yi ya tashi zaune cike da mamaki yake kallon jikinsa sai shafa ciki yake, Andizo ta ruƙo masa hannu tana mai nuna tsantsan farin ciki ta ce “Amour ya kake jin jikin naka yanzu?”
Lumshe ido ya yi Taufiƙ ya ce “Ka yi mamaki da ba ka ji alamar ciwo a jikinka ba ko?”
Buɗe ido ya yi ya ce “Sosai ma Taufiƙ wai me ya faru ne? Ko lokacin fara aikin ne bai yi ba? Amma kuma ai ni da kaina na shiga ɗakin tiyata na kwanta a kan gado aka mini allurori daga nan dai ban san komai ba sai yanzu.”
Zama ya yi a ɗaya daga a ɗayar kujera ya zayyano mishi duk abin da Doctor ya sanar da su, baki ya buɗe yana kallon Taufiƙ sai kuma ya juya ya kalle ta, kama hannun Limat ta yi ya ce su sun tafi gida ya bi su da kallo har suka bar ɗakin.
“Amour ka ga ikon Allah ko? Mu kanmu mun yi mamaki ko na ce mun ma fi ka Allah ne ya dube mu da idanun rahama amma dai abin akwai ɗaure kai duk da ba a ja da ikon Allah.”
Ajiyar zuciya ya sauke ya sa hannu ya ɗago ta ta taimaka mishi ta hayo gadon, kallon juna suka dinga yi na ɗan wasu second sannan ya ce “Gaskiya ina ta al'ajabi My wife, yau fa da safe ji na yi kamar ana yankan naman jikina har muka iso asibiti, a lokacin dauriya nake ganin yadda kika ruɗe amma kuma yanzu sai a ce wai lafiya ta ƙalau? To duk da haka dai Alhamdu Lillah.”
Murmushi ta yi ta sauka a gadon ta kama shi ya sauko sun nufo ƙofa sai ga doctor ya shigo, kallon juna suka yi ya miƙa mishi hannu ya ce “Congratulations.”
Murmushi ya yi suka fita tare yana ƙara mishi bayanin dukkan abin da suka gani har ya gamsu. Har bakin mota ya rako su sai da ya ga tafiyar su sannan ya dawo.
Chapter 71 · 0% Book details