← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 75

Sashe 35

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna zuwa gida motar Abie ma na isowa suka shigo gidan tare, sai da aka rufe su Andizo a ɗaki sannan aka shigo da gawar Salim ɗakin Mamma a nan aka mishi wanka aka shirya shi, bayan sun gama suka zo ɗaya bayan ɗaya suna mishi addu'a. Ana buɗe su Hajiya Babba da wata makociyarsu suka shigo da su ɗakin, rungume gawar Salim suka yi suna ta kuka duk da ana hana su yin kukan, Andizo kamar za ta yi hauka da aka zo ɗauke gawar za a fita da ita, ƙarshe daga ita har Aminatou sake suma suka yi ba su san ba lokacin da aka fitar da gawar..

_Maman Nusaiba🤙🏻_
[6/12, 2:13 AM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_

34

A harabar gidan aka aje gawar Salim suka sallace shi, Ahmad da kyar ya iya tsayuwar sallar duk dauriyar da yake nunawa ana salamcewa kuka ya subce mishi, Abdoul ya bubbuga kafaɗarsa shima hawaye na bin kuncinsa, sosai yake jin mutuwar Salim har ƙasan zuciyarsa gabaɗaya ya ji aikin soja ya fitar masa a kai. Jan shi ya yi gefe ya danne nashi kukan ya daure a kyar ya ce “Ahmad ka yi haƙuri mana ka masa addu'a ba kuka ba, za kake yi wa mamaci kuka bayan kasan ba a so wannan aikin ai sai mata aka sani da kuka mai sauti ba maza ba, ka daure mu tafi in kuma ba za ka iya zuwa ba ka zauna a gida mu je mu dawo.”
Girgiza kai ya yi ya goge hawaye ya ce “Dole na yi kuka Abdoul mutuwar Salim kamar mutuwar wani sashe na jikina ne.”

“Ba komai ka yo mishi addu'a kawai.”
Hannunsa ya kama suka shiga ɗaya daga cikin motocin da suke ɗaukan mutane zuwa maƙabarta, Abba da Abie su ne suak sa gawar Salim a tsakiya da limamin unguwarsu da wasu daga cikin malamai. Tun da Abba ya sunkuyar da kai kukan zuci yake yana tuna nagartaccan ɗansa wanda duk cikin yaransa ya fi jin sa a ranshi, iska ya fesar yana ta salati yana karanto addu'a yana tofawa..

Bayan sun isa an gama komai daam su ake jira, aka ɗauko gawar masu binnewa suka ce makusantan mamaci su matso, Abba, Abie, Ahmad, Abdoul da biyu daga cikin 'ya'yan Abie da suka zo tare suka matso su duka. A kansa Ahmad ya saka gawar Salim a rami shi da Abdoul, runtse ido ya yi yana ta addu'a ya matsa daga bakin ramin yan kallo suka gama rufe ƙabarin, bayan an gama duk aka tsaya ana ta yi wa mamaci addu'ar neman afuwa a cikin makwancinsa sunan amsawa da amin har aka gama. Kowa ya tafi ya bar Ahmad har su Abba sai da suka gama yin addu'oin da za su yi suka bar shi a wajen, Abdoul ya koma jikin mota yana jiran shi..

Hannu biyu ya ɗora a kan ƙabarin hawaye sun cika masa ido ya shanye su yana sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce “Ɗan'uwana zan yi kewar ka sosai, Allah ya yi maka rahama aiyukan da ka yi na alkhairi da ɗawainiyar da ka yi da mu Allah ya biya ka, ina kyautata maka zaton samun aljanna mafificiya Yaya Salim, Allah haskaka wannan gida naka matanka da ka bari da ciki Allah ya sauke su lafiya su haifa mana masu kama da kai sak ko za mu samu sassauci, ba zan gaji da yi maka addu'a ba har gaban abada, zan ci gaba da ziyartar ka in sha Allah ɗan'uwana bissalam..”
Tashi ya yi a hankali ya miƙe yana kallon ƙabarin, girgiza kai ya yi ya juya ya tafi yana kukan zuci..

Ana dawowa aka kafa runfuna a harabar gidan aka soma karɓar gaisuwa.

Tun da Andizo ta Aminatou suka sume sai da suka kwana suka wuni ba su farfado ba, har sai da Hajiya Babba ta ce likitar da aka kawo tana duba su su tafi asibiti kar a yi rashi da yawa sai kuma Aminatou ta farfaɗo, tana buɗe ido babu abin da nema sai kallon su take, ganin Ummi a kusa da ita ta soma ƙoƙarin mikewa za ta fita suka ruƙo ta aka zaunar da ita, addu'a Ummi ke yi mata tana mata nasiha a kan haƙuri da dangana yayin da aka yi maka mutuwa, sai a lokacin ta samu damar kuka ta dinga yi ba wanda ya hana ta, har wata ƙanwar Ummi za ta hana ta Hajiya Babba ta ce ta barta ta yi kukan za ta samu sassaucin radadin da take ji a zuciyarta mutuwar miji ciwon ta ya fi gaban kwatance. Sai da ta yi mai isar ta sannan ta kalli Ummi ta ce “Ummi ina Khadija take? Ku kaini wajen ta don Allah.”
Tashi Hassana ta yi ta kama ta ta ce “Muje na kaiki ki ganta.”
Da kallon tausayi suka bi ta har su soam tafiya Mamma ta ce su dawo za a kawo Khadija nan itama ta farfado, dawowa suka yi Aminatou ta zuba wa kofar shigowa ido tana share hawaye, tafi jin tausayin Andizo fiye da kanta.
Inna da Ɗahare suka shigo da Andizo da ta zama kamar kurma sai kallon mutanen ɗakin take, har kusan Aminatou suka kawo ta aka zaunar da ita Aminatou ta rungume ta ta sake sa sabon kuka ta ce “Ki yi haƙuri kin ji Khadija Allah ya fi mu son Salim shi ya sa ya ɗauke mana shi, kar ki yi kuka kin ji ki daure..”
Kowa da ɗakin sai da kalaman Aminatou ya saka shi zubar da hawaye, Andizo ta ɗago kai ta kalli Aminatou ta ce “Yanzu Adda shi kenan ba za mu sake ganin mai hankali ba? Waiyo Allah ni Dije ya zan yi da rayuwata babu kai a cikin mijina? Adda hannuna cikin nasa ya rasu fa, jiya da dare har kusan ƙarfe ɗaya muna hira ya ce so yake ya ga mun haifa masa yaransa ashe ba zai gansu ba, yanzu ina gawar tashi take ina so zan yi mishi addu'a tashi ki kaini Adda na ga fuskarsa gani na ƙarshe..” Ta ƙarasa tana sakin kuka mai tsuma zuciyar..

Girgiza kai Aminatou ta yi ta ce “Ki yi haƙuri Khadija ai tun jiya aka kai shi gidansa na gaskiya, nima sai yanzu nake ji labari a wajen su Ummi.”
Kanta ta kwanto a kafaɗar Amiantou suka ci gaba da kuka suna ta surutai kamar sun fita daga haiyacinsu, da kyar aka shayo kansu suka daina kukan.

Haka aka yi ta karɓar gaisuwa har aka yi sadakar uku, Andizo da Aminatou kuwa a gado ɗaya suke kwana saboda dukkan su in suka kwanta daban-daban ba sa iya bacci suna kuka domin tuna mijinsu kowacce tana faɗin da yana nan tare za su yi bacci rungume da juna cikin nishaɗi. Da farko an so a raba musu su kowacce take kwana a gado ita ɗaya amma suka ƙi dole aak haƙura aka rabu da su.

Sai ranar sadakar sati mutanen da suka rage suka tafi aka bar 'yan gidan, sai a lokacin Ahmad ya samu damar shigowa cikin gida da yamma. Saurin kallon shi Andizo ta yi sai ta ga kamar Salim ne ke nufo ta, gane hakan ya sa Ahmad ya zo har gaban ta ya durƙusa amma ba ta daina kallon shi ba, ganin daga ita sai Aminatou a palon ya hura mata iska yana faɗin “Khadija ya dai? Wannan kallo haka ko dan kin kwana biyu ba ki ganni ba.”
Hawaye ne suka zubo mata ta kalle shi still dai fuskar mijinta take gani a fuskar Ahmad, runtse ido ta yi yana faɗin “Allah ya jiƙan ka da rahama.” Ta buɗe ido ta ta sake kallon shi, a hankali ta ga yana canja mata har fuskar Salim ta ɓace a ganin ta, ajiyar zuciya ta sauke ta ce “Ka yi hakuri.” Iya abin da ta faɗa daga haka ba ta sake cewa komai ba..

Girgiza kai ya yi ya kalli Aminatou ya ce “Ya jikin naku fatan dai komai lafiya babu inda yake muku ciwo?”
Kai ta gyaɗa mishi ta nisa ta ce “Alhamdu Lillah ba ma jin komai.”
Tashi ya yi tsaye ya sa hannu a aljihu ya juya yana fadin “To Alhamdu Lillah idan sati ya zagayo likita za ta zo ta duba lafiyarku, amma don Allah kafin lokacin ku yi ƙoƙari ku rage yawan tunani kar hawan jini ya kama ku, ku cika wa Yaya Salim alƙawarin da kuka ɗauka.”
In sha Allah Aminatou ta faɗa ya fita ya bar palon.

Washegari Inna ta ce su za su tafi da Andizo gida a kula da ita Hajiya Babba ta dube ta ta ce “Kar ku tafi da ita ƙauye, za mu ci gaba da kula da ita har ta haihu ita da ƙauye sai ziyara dan in ta gama takaba mu za mu aurar da ita ga duk wanda take so, domin Maigari ya ba ni ita amana.”
Murmushi Inna ta yi tana jinjina kirki irin na wannan dangi, gyara hijabi ta yi ta ce “Ayya to ai ban san kun yi haka ba, to shi kenan Allah sauke ta lafiya za mu sake dawowa in an samu kwanaki biyu haka.”
Allah kiyaye hanya suka musu Andizo tana kallo suka fita da kyar ta iya ce musu su gaida gida, sai da Dahare za ta tafi ne ma ta yi kuka ganin ita kaɗai a ɗakin, rarrashin ta ta yi ta ƙara yi mata nasiha sannan ta tafi..
Giɗaɗo ya so ganin Andizo amma bai samu dama ba sai haƙura ya yi suka tafi gida..

Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji har Salim ya yi wata ɗaya a kabari, a ranar ne kuma Mom da Farrah suka diro garin Niamey. Kasancewar Farrah ta san sunan Unguwar suka dinga tambaya har suka iso kofar gidan, hon suka yi aka buɗe musu suka shigo..
Chapter 35 · 0% Book details