Sashe 45
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tsaye ya yi a tsakar ɗakin yana wurga na mijiyarsa ko zai ga inda ta aje akwatin, gaban wardrobe ɗin ta ya isa ya buɗe. Yadda ta jera kayanta da na su Nour sai ya birge shi, hannu ya kai ya soma buɗa kayan ko zai gani, wata ambulan ce ta faɗo fara ya sunkuya ya ɗauka. Buɗewa ya yi ya fito da abin da yake ciki, photon Salim ne sun fi talatin wani shi da ita sun rungumi juna suna dariya, wani kuma ta turo baki gaba ta harare shi aka ɗauki photon. Shagala ya yi da kallon photunan ba ƙaramin birge shi suka yi ba sai murmushi yake, a hankali ta buɗe banɗakin ta fito tana kallon ƙofar ta ga baya nan, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin “Mutum sai shegiyar mugunta ya sa a gaban shi, to Wallahi ko me za ka yi ba ka isa na ba ka wannan akwatin ba, daga kai har shi babu wanda ya ishe ni kallo shima har wani cewa yake zai kaini ƙasar waje ya ɗauka zai rude ni da kuɗi na yarda,to ko Salim da ya aure ni ba dan kuɗinsa nake son shi ba saboda ya iya soyayya da bada kulawa ga sanin darajar iyali.” Hannu ta sa ta goge hawayen da suka zubo mata tunawa da masoyin nata ta ɗora da cewa “Allah ya jiƙan ka mijina ba zan taɓa mantawa da kai ba a rayuwata.”
Duk abin da take yana jin ta shi sam ya rasa me ya sa ta kasa sassauta wa zuciyata a kan soyayyar Salim wanda kasa ta rufe idonsa, a hankali ya tako ya iso kusa da ita tare da sa hannu ya dafa kafaɗarta. Da sauri ta juyo suka haɗa ido, hararar shi ta yi ta bige hannun ta yi gaba ta zauna a kan gado, kallon ta ya yi da wani irin yanayi yana jin ciwon furta masa kalmar da ta yi jiya, zuciyarsa ce take bugawa da sauri-sauri kamar ana turo shi ya ƙaraso ya tsugunna a gaban ta, kallon shi ta yi da ta ga idanuwansa sun cika taf da ruwa ya yi kalar tausayi sai mamaki ya kama ta. Hannunsa ya ɗora a kan cinyarta cikin wani kalar voice ya ce “Khadija ki yarda da ni.”
Kallon ban gane ba ta jefa masa duk da ya ba ta tausayi amma ba ta jin har akwai ranar da za ta ba wa Ahmad yarda.
Zama ya yi da kyau a ƙasa ya kamo kafarta yana ja mata 'yan yatsu, lumshe ido ta yi dama ƙafafuwan nata sun kumbura kamar na mai tsohon ciki, ganin yadda take lumshe ido sai ya ƙara da matsa mata ƙafar a hankali yana jera mata sannu. Shuru ta yi tana jin shi babu abin da take tunawa sai lokacin da duk ta tayar da rigimar jikinta ciwo Salim zai zauna ya yi ta matsa mata jiki. Can kuma ta buɗe ido da sauri ta janye ƙafarta tana yin istigifari, kallon ta ya yi ya sakar mata murmushi mai ƙayatarwa sannan ya miƙe tsaye, sai da ya kusa kaiwa ƙofar fita ya juyo ya ce “Khadija ki yi haƙuri ki a je komai mu yi auren nan, nasan ba kya sona amma mu yi hakan ba dan kanmu ba sai dan yaran nan su tashi tare da uwa da uba.”
Juya mishi baya ta yi ta ce “Ka bar ma wannan maganar ba zan taɓa yarda da hakan ba.”
Bai sake ce mata komai ba ya buɗe ƙofa ya wuce.
Sai da ta ji fitar sa sannan ta gyara kwantaciyar ta tana sauke ajiyar zuciya, gabaɗaya duk ya bi ya takura wa rayuwarta ta ja tsaki ta janyo bargo ta rufa.
Sai da ta yi kwana biyu ba ta je ècole ba saboda yadda take kwana da zazzaɓi har garin Allah ya waye ba ya sauka sai rana ta, Mamma ta ce likita ya zo ya duba ta amma sam ta ƙi ta ce ai ta samu sauƙi ma, ganin ba za su daina maganar zuwa asibiti da kiran likita ba washegari ta shirya ƙarfe 7:30am zuwa makaranta.
Tana fitowa palon gaisawa suka yi da Hajiya Babba da take sababi ita kaɗai a palon, zama ta yi tana faɗin “Hajiya waye ya taɓo mana ke kike faɗa da safiyar nan?”
Gefen kitchen ta kalla ta tofar da yawu ta ce “Da ni da wancan ɗan butar uwar mana, ya zo yana faɗa mini maganar banza ni sa'ar shi ce da zai ke faɗa mini duk wata maganar da ta zo bakinsa? To ni ba ƴar banza ba ce bari uban nasa ya dawo zai ga me zai faru, ko kuma zan haɗa shi da Saddiƙu.”
Dariya Andizo ta yi ta miƙe tana faɗin “To wa zai shiga tsakanin ku ke da ɗan lelen ki? Ni na tafi sai na dawo.”
Kwafa ta yi tana faɗin “Daɗin ta ma kema ba barin ki ba ya yi har da kika ƙi tayani yi mishi faɗa, za ku dawo ku same ni yau a gidan nan ba mai yin girki kowa ya girka nashi ya ci.”
Dariya Andizo ta kuma yi tana gyara zaman hijabin jikinta ta wuce.
A harabar gidan ta same shi ya yi tsaye hannayensa cikin aljihu yana kallon gefe, ƙura mishi ido ta yi tana ƙare mishi kallo, yadda yake a tsaye ƙyam sak Salim ga shi ɗan wanka sai ta ga ya mata wani kalar kwarjini, sai take ganin kamar Salim ne take tunkara hakan ya sa ta dinga sakar masa sayayyan murmushi irin na masoya, sanjensa da yankwanta luf a fuskarsa ta bi da kallo tana faɗin “Wannan shi ne mijina.”
Karaf maganar a kan kunnensa ya juyo cikin jin daɗin abin da ta faɗa ya miƙa mata hannu ganin ta kusa zuwa da nufin ta ba shi jakar makaranta, sai da suka haɗa ido ta ga ya juye ya dawo Ahmad nan da nan annurin kan fuskarta ya ɗauke ta ja tsaki ta kauce, hawayen da suka cika mata ido ne suka samu damar zubowa ta kai hannu ta goge, shi kuwa da kallo ya bi ta ganin yadda lokaci ɗaya ta haɗe rai.
Wajen direba ta duba yana ganin ta ya ƙaraso tare da rusunawa ya ce “Madam barka da fitowa.”
“Yawwa barka dai baba ècole nake son zuwa.” Ta faɗa tana yatsina fuska. Kallon Ahmad ya yi hakan ya sa ta gane sai ya ba shi umarni abin sai ya ɓata rai, ba ta son ta makara dan haka ta juya ta nufi ƙofar fita da sauri. Murmushi ya yi ya ce “Baba ka rabu da ita karka ɗauke ta ni zan ke kaita.”
Jinjina kai ya yi ya koma inda ya zauna shi kuma ya shiga mota ya fita, sai da ya bar unguwarsu sannan ya hango ta can naisa da shi bakin hanya tana ƙoƙarin tsayar da motar haya, dafe kai ya yi ya ce “Oh Khadija rigimar ki ba ta ƙarewa, shi ya sa Yaya Salim yake cewa zai ga lokacin da za ki yi hankali.”
Har ta tsayar mota tana sanar da shi inda zai kai ta sai ga wasu motoci biyu sun paka a gefen su, wani ƙaƙƙarfan namiji ne ya fito daga mazaunin direba ya iso wajen su, da kallo Andizo ta bi shi sai kuma ta kawar da kai tana yin tsaki, cike da gadara ya ce “Kai ɗan sahu wuce abin ka wannan ba kalar hawa irin motarku ba ce.”
Da mamaki Andizo take kallon mutumin har mai motar ya wuce, cike da girmamawa ya ɗan rusuna ya ce “Madam mu je oga yana jiran ki a mota.”
Kallon ba ka da hankali ta mishi tana jin kamar ta zabga mishi mari, agogon da ke daure a tsintsinyar hannunta ta kalla ta ga ƙarfe 7:45am rai ɓace ta kalle shi ta ce “Waye wani Oga? Kawai daga gani na sai ka ce wai na je Oga na jira na ka sanni ne?”
Girgiza kai ya yi cikin girmamawa ya ce “No Madam mu je dai ki ganshi karki makara ya ce mini makaranta kike son zuwa.”
Banza ta mishi ta ci gaba da tsayuwa tana ƙoƙarin tare mota, amma duk wanda ya yi ƙoƙarin tsayawa sai wannan mutumin ya kalle shi dole ya ƙara wa motarsa gudu, dafe kai ta yi kamar za ta fashe da kuka ta ɗago kai sai ta ga Amira a gaban ta, da mamaki ta ce “Amira!”
Ba ta amsa ba sai hannunta da ta kama ta ja ta suka nufi motar, kamar raƙumi da akala haka ta dinga bin ta har ta buɗe ɗayar motar ta saka ta ta rufe sannan ta dawo ta gaba da su ta shiga suka soma tafiya.
Ahmad yana kallon su sai ya tuna abin da Andizo ta faɗa lokacin da ta ga Sultan, “Mene ne haɗin ka da Amira.” Ya nanata maganar take ya gane Sultan né ta ɗauke ta, kwafa ya yi ya juya kan motar ya nufi wajen aikinsa.
Kasa yin tuƙin motar ya yi ya koma bakin hanya yana sauke ajiyar zuciya, kishin ta yake ji sosai wanda har yake barazanar ɗaukewar numfashinsa kamar mai ciwon asma, dafe saitin zuciyarsa ya yi da karfi jin yadda take bugawa da mugun gudu. Ya jima a haka sai addu'a yake ta karantowa ko zai samu sassauci, sai da ɗauki kusan minti shabiyar sannan ya dawo daidai amma kana ganin shi kasan yana cikin ɓacin rai, wayarsa ya ciro daga aljihu ya lulibo wata number ya danna mata kira, ana ɗauka ya ɗan saki fuska ya ce “Assalam alaikum Maigari Angon Hajja barka da safiya.”
Daga can ɓangaren Maigari da yake hanyar dawowa gida daga masallaci ya ce “Wa alaikum salam Ahmadu ya kuke kun tashi lafiya? Ya wajen su uwar masu gari?”
“Tana nan lafiya maganar ta ce ma nake so mu yi shi ya sa na kira.”
“A to ba damuwa in ce dai lafiya ba wani abu ba ne marar kyau ya faru ko? Dan ni na ce ma ta dawo gida zaman haka ya isa ta samu ta yi aure.”