← Book details Andizo Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 75

Sashe 26

Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Andizo ta yi dariya ta ce “Wallahi da wannan hannun naki mai bleaching ya taɓa naman jikina in duk garin nan gatan ki ne sai na sa an daure, shegiya mai baƙar zuciya dama ni tun da na miki kallon farko naji ba ki kwanta mini a rai ba ƴar wahala, in ma kika sake zuwa gidan nan tun da naji abin da kika ce wa Adda sa wa zan yi ta danne mini ke na miki balle-balle a mazaunai, ke har bille sai na miki irin na fullo..”

Har Sabrin ta tsaya sai kuma ta sha kanwa ta wuce fu ta fita daga gidan, sosai ta ji zafin abin da suka mata musamman ma Aminatou ta kuma sha alwashin sai ta rama abun da suka mata..

Shugowa ta yi tana kumbura baki ya ce “Ki rabu da ita Adda, ai dama mai hankali ya faɗa mini ke mutuniyar kirki ce kina da biyayya ita ce take son mayar da ke wani abin..”

Murmushi ta yi tana ƙara jin son Salim tabbas ta yarda shi ɗin jajirtaccan namiji ne, tun da har zai iya yaba halayenta a gaban abokiyar zaman ta. Kitchen suka nufa suka girka abinci mai rai da lafiya sai ƙamshi yake tashi, babu abin da yake damun Aminatou irin gorin haihuwar da soma mata, addu'a ta cigaba da yi Allah ya ba ta ciki itama ko za ta ga gudan jininta a duniya...

Da gudu ta fito ta leƙa wajen Aminatou ta ce “Adda na tafi na taro ƙawata ta zo.”

To ta ce mata ta fito ta nufi bakin get, budewa ta yi ta leƙa ta ga mota biyu a tsaye, har za ta koma saboda sun ba ta tsoro sai ta ga Farrah ta fito daga cikin motar ta nufo ta.

Dariya ta dinga yi tana kallon ta har ta iso suka rungume juna suna murna da ganin juna, ciki ta ja suka shige part ɗin..

Kallon ta kofar gidan direban da ya kawo Farrah ya yi, ya yi saurin janyo waya ya kalli photon ya kuma hasko na Andizo, da sauri danna kira.

“Hello oga yau dai mun ga gidan su yarinyar da ka ce mu nemo tun watannin baya, ashe ma ita ce ƙawar Farrah.”
Shuru ya yi na 'yan daƙiƙu ya jinjina kai ya ce “OK sir wannan karon ba za mu bari a samu matsala za mu kawo maka ita..”

_Maman Nusaiba ce_
[6/5, 5:53 PM] Ummu Amjad: _*AREWABOOKS@SARATALKASUM88*_

29

Sauke wayar Sultan ya yi yana sakin wani shu'umin murmushi, taku biyu zuwa uku ya yi ya ce “Oh my wife ina matuƙar kewarki sosai da sosai, ban san dalilin da ya sa kika bari aka aura miki wani daban ba bayan ni da nake da matsayin mijinki, amma ba komai duk na kusa kawo ƙarshen komai ko kin daina azabtar da zuciyata.” Tashi ya yi da sauri ya fito palo inda ya samu Jennifer zaune tana kallo daga ita sai wani ɗan pant da bra, tana ganin shi ta saki murmushi ta matsa tana nuna mishi kusa da ita ta ce “Sweetheart come here.”
Hararar ta ya yi ya koma ɗayar kujerar ya zauna yana kada ƙafa, cike da raini yake kallon ta yana jan tsaki, da idan ta yi irin wannan shigar gabaɗaya susuce mata yake har sai ya samu abin da yake so yake barin ta, wani lokacin ma sai su wuni a manne da juna suna shan soyayya, hakan ya sa Jennifer duk ta kori samarin da suke sheɗanci ta tsaya a wajen Sultan, domin ita a rayuwarta Allah ya mata mugun son namiji ɗan Africa musamman ma irin Sultan tsayayyan namiji ga kwarjini ga nuna izo, ga shi kakkarfan jarumi a fagen buga bal. Shi ya sa ta ƙudiri aniyar wannan karon da ita zai tafi Nigeria ta je ta ga ahalinsa, in daga can ma sai a ɗaura musu aure, yayin da duk wani motsin ta Sultan na gani yana mata mahaukaciya, shi yanzu gabaɗaya ta fitar masa a rai ba ya jin sha'awar zama da ita kwata-kwata, tun da ya haɗu da Andizo ya yanke alaka da duk wata mace daga kan turawa har na gida Nigeria in ya je da suke zuwa..

Tashi ta yi ta iso gaban shi ta zauna a kan cinyarsa tana shafa shi kamar yadda suka saba ya kawar da kai ya ce “Jennifer go.”
Ƙin tashi ta yi ya sake mata magana amma taƙi tashi, a fusace ya hankaɗa ta ta faɗi tim ya zabga mata mari amma taƙi barin inda yake sai so take ta rungume shi, cikin hargowa ya ce “Jennifer na ce ba na so ki ƙara taɓa ni, oya get out of my house.”

Gefe ta koma tana kuka saboda marin ya shige ta sosai, da yake ya koya mata Hausa tana ji sosai ta gane me ya faɗa mata, nuna ta ya yi da hannu ya ce “Na faɗa miki ni yanzu ina da mata na daina kula kowacce mace ki je can ki ƙarata da sauran 'yan iskan samarinki.” Ya faɗa yana juya mata baya.

Tashi ta yi tana share hawaye murya na rawa ta ce “Babu inda zan je ina nan a tare da kai, ba ka isa ba Sultan sai ka aure ni babu ruwana da matarka, a baya ba ka ce mini addininku ya ba ku dama ku auri mata 4 ba? To ka zauna da mu biyu mana I really love you Sultan, ba zan iya rayuwa da kowanni namiji ba in ba kai ba. Kuma ina nan a gidan nan dole ka tafi da ni Nigeria, ko dan ka ga iyayena sun mutu ina hannunka shi ya sa har kake dukana? Ko mai za ka yi sai mun je tare har gidanku an mana aure..” Tana gama faɗin haka ta ja jikinta ta shige ɗaki ta banko ƙofar.

Kallon ƙofar ɗakin ya yi ya ja tsaki ya wuce a gidan fuu, dan shi yanzu ba ta ita yake ba ta yadda zai dawo da abar ƙaunarsa yake.

Ranar Andizo da Farrah wuni suka yi suna shirme, har girki Andizo ta zo ta musu na taliya fara da yaji da manja suka ci. Da yamma Salim ya dawo daret ya wuce part ɗin ta, tun kafin ma ya shiga ya dinga juyo dariyarsu ya yi murmushi ya ce “Oh su Dije ƙawa ta ƙaraso ashe, ko me suke yi?” Ya faɗa yana kwankwasa ƙofar.

Da sauri Andizo ta tashi tana kallon jikinta ta ga ba komai, ɗaki ta nufa da gudu ta je ta ɗauki turaren da Aishatou ta ba ta ta ce in mijinta zai dawo daga office ta sa ta tarbe shi da shi, lumshe ido ta yi ta ce “Alƙur'an akwai ƙamshi mai daɗi.”
Fita ta yi da sauri Farrah kuwa ta tashi ta shige ɗakin da aka kai mata kayanta, domin ta ɗauko wayarta ta kira Mom vidéo call su gaisa..

Buɗe ƙofar ta yi a hankali tana sakar mishi da murmushi, wani daɗin ƙamshi ne ya ziyarci Salim ya lumshe ido ya shaka. Hannu ta miƙa ta amshi jakar computer ta ce “Sannu da zuwa mijina.”

Waro ido ya yi baki buɗe yana kallon ta cike da mamaki, far ta yi masa da idanu tana dariya, yau ɗin nan ta rantse duk wani abu da Aishatou ta koya mata sai ta yi wa Salim ta gani zai ji daɗi kamar yadda take faɗa mata maza na son irin haka.

“Wow ma femme Wallahi je t'aime.” Ya faɗa yana jan hancinta. Dariya ta yi ta kama hannnunsa suka iso cikin palon, har za ta ja shi kan kujare sai ta yi jim ko me ta tuna sai ta ja shi suka yi gaba, shi kuma bin ta yake kamar raƙumi da akala.
Inda ta ga yana aje computer ta kai ta aje, kallon shi ta yi ta ce “Wanka za ka yi ko kuma na zubo maka abinci? Yau kaima taliya da manja za ka ci..”
Ƙara kashe shi ta yi da mamaki ya yi tagumi yana kallon ta, turo baki ta yi ta ce “To alƙur'an sai in fasa.”
Murmushi ya yi ya ce “Haba ni na isa Khadija, zan fara yin wanka sai a kawo mini taliya da manja.” Ya faɗa yana dariya dan shi ya manta rabon da ya ci taliya da manja, in bai manta ba tun sun makarantar kwana ta aikin soja.

Banɗaki ta shiga ta haɗa mishi ruwa sannan ta fito ta ce “To je ka yi wankan.”
To ya ce mata ya zo cire kaya nan ma ta haye kan gado ta ce ita za ta taya shi ya fidda, bai mata muso ba ta taya shi ya cire kayan ya sa towel ya shige banɗaki..

Yana fitowa ta gama kawo masa abincin ta jera, bayan ya kimtsa ya zo ya zauna yana kallon abincin, daurewa dai ya yi ya juya taliyar ya kai baki dan kar ya ƙi ci yau ta hana shi bacci cikin nutsuwa, mamaki ya yi jin yajin ya yi daɗi. Kafin ya ankara ya cinye tas tana mishi hira yana amsawa da eh ko a'a bai san ya cinye ba sai da ya sa cokali ya ji ba komai, kallon juna suka yi Andizo ta sa dariya ta ce “Yee alƙur'an ya cinye duka taliyar, da har kake wani yatsina fuska kamar ka ga kashi.”
Jinjina kai ya yi ya je ya wanke hannu da bakinsa ya dawo, ruwa mai sanyi ta miƙa mishi ya amsa ya sha..
Chapter 26 · 0% Book details