Sashe 55
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ihun ta ne ya tayar da su ƙarfe uku da rabi na dare, ta fito a guje ta nufi ƙofar palo tana son fita Mamma ta iso wajen ta tana salati, ruƙo hannunta ta yi ta ce “Ke Khadija lafiya ina za ki je.”
Ƙoƙarin kwacewa take tana faɗin “Fita zan yi ki sake ni na tafi.”
Ta kwace ta ƙarasa buɗe kofar Mamma ta juya da sauri tana kiran Ahmad, can cikin bacci ya ji kiran hakan ya sa ya buɗe ido ya yi zaton ko mafarki ne yake amma ya ƙara jin kiran, da sauri ya mike ya fito ya ga Mamma a firgice tana ganin shi ta ce “Don Allah maza bi ta Khadija ce ta fita da gudu yi sauri na rike ta ta kwace har da ture ni ta yi.”
Kafin ma ta ƙarasa ya wuce da sauri ya fito waje ya same ta ita da maigadi suna ta fama, ƙarasowa ya yi ya kamo hannunta tana turjewa tana kai masa duka sai fadi take ya rabu da ita za ta fita, ganin abin na neman fin ƙarfinsa ya daddage ya ɗauke ta cak ya dawo da ita ciki. A palo duk suka zauna tana matse a jikin Ahmad sai kuka take tana son kwacewa, Abba ya matso ya dinga mata karatu yana fito mata, tun tana mutsu-mutsu har ta saki jiki bacci ya ɗauke ta, kowa ajiyar zuciya ya sauke yana kallon fuskar Andizo yadda ta yi kaca-kaca da ruwan hawaye da majina,Hajiya Babba ta nisa ta ce “Ni dai ban taɓa ganin Khadija ta yi irin wannan abin ba, ko ma meye ke son samun ta Allah ya yi mata katangar ƙarfe da shi.”
Amin suka ce a tare Mamma ta ce Ahmad ya kaita ɗakin Hajiya babba ya amsa da to. Yana kaita ya hau kan gadon ya kwantar da ita, gabaɗaya duk sai ta ba shi tausayi yana ta mata addu'a, zama ya yi a bakin gadon ya zuba mata ido har sai da Hajiya ta shigo ɗakin ya fita ba dan ransa ya so ba....
_*Maman Nusaiba ce*_
[7/3, 5:26 PM] Ummu Amjad: ADZ
43
Daren ranar Ahmad bai sake komawa bacci ba har aka kira assalatu ya miƙe ya shiga banɗaki ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da raka'a tainun fajur ya zauna yana yi wa Andizo addu'ar samun sauƙi, domin ya matuƙar firgita da ganin abin da ta yi yau da kyar ya iya sarrafa ta duk ji da yake shi cikakken namiji ne mai ƙarfi. Ajiyar zuciya ya sauke ya tashi ya fice domin zuwa masallaci, a hanya suka haɗu da Abba suka wuce a motarsa.
Ƙarfe 7:am na bugawa Andizo ta farka tana miƙa, kallon inda take a kwance ta yi tana zaro ido cike da mamakin yadda aka yi ta zo ɗakin Hajiya Babba, ba ta gama shan mamakin ganin ta a ɗakin ba sai da ta ga duk yan gidan sun shigo ɗakin kowa yana jero mata sannu, kallon su kawai take har sai da Mamma ta zo kusa da ita ta taɓa jikinta ta ji ba zafi, murmushi ta sakar mata ta ce “Sannu Khadija yanzu ina yake miki ciwo?”
Girgiza kai ta yi ta ce “Kaina kawai yake ciwo Mamma amma me ya kawo ni ɗakin Hajiya?”
Ba wanda ya ba ta amsa sai kama ta da Mamma ta yi ta sauko ta raka ta har banɗaki tana sanar ta ita ta yi Sallah har ƙarfe bakwai ta yi, sosai ta sha mamaki domin ita ba ta makara har ta kai bakwai ba ta yi sallah ba, haka dai ta yi alwala ta yi sallah ta yi zaune tana tunani ko za ta tuna yadda aka yi ta zo ɗakin Hajiya tun da su sun ƙi ba ta amsa amma sam ta kasa tunawa.
Ƙamshin turarensa ne ya kawo wa hancinta ziyara ta ɗago kai ta kalli ƙofa karaf idanunsu ya sarke da na juna, murmushi yake sakar mata yana takowa zuwa gareta, itama murmushi ta mishi bai taɓa yi mata kyau da kwarjini ba irin yau ta kasa ɗauke idanunta daga kallon shi kamar yadda shima yake a ɓangarensa. Sai da ya iso ya durƙusa gwiwowunsa har ƙasa ya yi magana murya can ƙasa, “Bonjour ma belle comment vas tu aujourd'hui ?”
Sunkuyar da kai ta yi cike da jin kunyar kallon da ta mishi, a hankali ta amsa da “Alhamdu Lillah.”
“Ma sha Allah naji daɗin haka, yanzu ki tashi mu tafi asibiti a duba lafiyarki, duba ki ga daga jiya zuwa yau yadda kika zabge kamar kazar mayu.”
Turo baki gaba ta yi ta ɓata rai ta ce “Ni fa na samu lafiya ba sai mun je asibiti ba.”
“Ai kuwa ba ki isa ba sai mun je, tashi maza ki ɗauki hijabinki mu tafi kar na makara wajen aiki.”
Kallon shi ta yi ta ce “Wai Yaya aikin me kake yi? A baya fa ka ce ba ka son koyarwa kaima sojan kake son zama, ni dai ina tsoro don Allah karka tafi aikin soja ba na son kaima wani abu ya faru da kai.” Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata. Murmushi ya yi ya kamo hannayenta ta ce “Haba Khadija ai ba zan yi aikin soja ba yanzu, da dai ina da ra'ayi amma yanzu ba ma za a bar ni ba saboda abubuwan da suka faru, ba wia kuma muna yiwa Allah dabara ba ne kawai dai naji a raina aikin ya fice mini a rai, yanzu ni 'yan jami'a nake koyarwa.”
Murmushi ta yi ta ɗaga baki za ta yi magana sai kuma ta fasa ta miƙe a hankali ta koma bakin gado, ganin hakan ya sa ya wuce yana ƙara jidadda mata kar fa ta jima ta amsa da to tana hararar bayan sa.
Ba dan ta so ba ta fita daga ɗakin ta nufi nata ta ɗauko hijabi ta fito, kiciɓus suka yi da shi a bakin ƙofa ya yi saurin taro ta ganin ta yi baya za ta faɗi ya haɗa ta da jikinsa, shuru ta yi tana jin sautin bugun zuciyarsa da sauri-sauri can kuma da ɗago sauri, kallon ta ya yi ya mata alamar me ya sa ta tashi, sunkuyar da kai ta yi za ta raɓa ta gefen shi ta wuce ya ruƙo ta suka fito a tare. Buɗe mota ya yi ya saka ta ya rufe sannan ya zagaya ya shiga suka tafi, sai da suka yi nisa ta ɗan kalle shi kamar wata munafuka ta ce “Yaya ba ka da lafiya ne?”
Murmushi ya sakar mata bai ce komai ba, itama daga hakan ba ta kuma faɗin ko kalma ɗaya ba ganin ya ƙi ba ta amsa. Suna isa daret wata ƙofa ta ga ya kwankwasa aka ba su izinin shiga, da sallama suka shiga inda suka samu wata babbar mace a ciki ta hakimce a kan kujera tana ta rubutu, suka zauna Ahmad ya gaishe ta ta ɗago kai tana murmushi ta ce “A'a sannun ku da zuwa yau kaine da kanka ɗan Abie?”
Sosa kai ya yi sannan ya kalli Andizo da ta kusan dawowa kansa sai rawar sanyi take ya kai hannu ya ɗago ta yana ƴar dariya ya ce “Matsoraciya daga ganin likita sai ki kama rawar sanyi tun ma ba a duba ki ba?”
Saurin komawa ta yi kan cinyarsa ɗaya ta kwanta tana lulluɓa da hijabin jikinta, kallon su likitar ta yi tana murmushi ta ce “Ko ita ce Khadijar da aka sa muku rana?”
“Ita ce Mami ba ta da lafiya ne jiya ta hana mu bacci shi ne na kawo ta a duba mini ita, tun da aka sa bikin nan namu duk ta taƙi sakin jikinta musamman shekaranjiya da jiya.” Ya faɗa fuska ɗauke da damuwa. Girgiza kai matar ta yi ta miƙa hannu ta ce “Zo nan 'yata karki ji tsoro kin ji zan duba ki ne.”
Maƙale kafaɗa ta yi nan da nan idanuwanta suka cika da ruwa baki na rawa ta ce “Ni dai ba na so gida zan koma.”
Dariya Ahmad ya yi yana ɓamɓare ta daga jikinsa ya ce “Ai kuwa ba ki isa ba sai an duba ki tun da mun zo har cikin office ɗin Mami.”
Kuka ta sa musu tana ƙara ƙanƙame Ahmad, hakan ya sa Mami ta kalli Ahmad ta ce “Riƙe ta a haka in duba ta.”
Ɗauko ta ya yi cak daga kan kujera ya rungume ta sosai ta yadda ba za ta subce masa ba, da haka Mami ta fara auna ta ta ɗibi jininta kaɗan ta koma can fege, allura ta ɗauko ta fasa kwalbar ta zuƙa ta nufo su, ai kuwa ƙara ta sa tun kafin ma a tsira mata allurar Mami ta yi murmushi tana faɗin “Kai ko Ahmad wannan mata taka akwai mugun tsoron allura.”
Dariya shima ya yi ya ce “Kuma fa ta taɓa haihuwa amma take tsoron allura.”
Riƙe ta ya ƙara yi sannan aka mata allura guda biyu, bayan an gama ta yi rubutu a kan wata takarda ta miƙa masa ta ce “Gaskiya tana fama da zazzaɓi da ciwon kai mai zafin gaske amma dai ta rage tunani, wannan maganin da na rubuta su za ku saya take sha ko sun ƙare a ƙara sayo mata domin zai taimaka mata matuƙa.” Ta faɗa tana kallon Andizo da take murtsika ido.
Godiya ya mata ya tashi ya kama hannun Andizo suka tafi, da kyar ta isa mota da ƙafarta saboda allurar da aka mata ta ɗan riƙe mata ƙafa.