Sashe 14
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallon ta kawai yake tana kai masa duka ta ko'ina, sai da ta gaji dan kanta sannan ta daina tana huci ta ce “Ni ka tashi ka kaini wajen Hajiya Babba ba zan kwana a nan ba..” Ta faɗa tana jan hunnunsa ta sauka daga kan gadon.
Janyo ya yi ta yo baya ya zaunar da ita, a tausashe ya soma mata magana a daidai saitin kunnenta cikin kihima yadda za ta yi laushi.
“Haba matar Salim meye na rigima da daren nan? Ba dai gidan Hajiya babba kike son komawa ba?”
Gyaɗa masa kai ta yi tana turo baki gaba, hannu ya sa ya shafa bakin ya ɗora da cewa “Ai su gidansu ba shi da kyau irin nan, kinga fa duk girman wajen nan naki ne da duk abin da yake ciki har tv ga shi can a palo, idan kina so kike kallo ina kaiki makaranta ki daina rigima kin ji kuma ban da ƙin bin umarnina.” Ya ƙarashe maganar yana ɗago da ita jin ta saki jiki ta daina kukan, kallon ta ya yi itama ta kalle shi sai ta sa dariya tana tashi tsaye, gadon ta hau tsakiya ta soma tsalle tana faɗin “Kai Alƙur'an gadon nan akwai daɗin hawa, zan dinga haya abuna ina shan daɗin katifa.”
Dariya shima ya yi ya tashi ya ce “To zo mu je mu yi Sallah mu gode wa Allah da ya ba mu ikon zama mata da miji.”
Har za ta yi gardama ta tuna alƙawarin da ta yi wa Hajja sai ta sauko ta rike hannunsa suka nufi banɗaki.. Makilin ya ba ta ya ce ta goge bakinta, kallon shi ta yi tana cewa “Goga haƙorin zan yi ko na haɗa da ruwa na tofar?”
Nasa ya ɗauko ya sa makilin ɗin ya nuna mata yadda ake yi, to ta ce ta goge itama ya ce ta yi alwala yana nan zuwa. Alwalar ta ɗaura tana kallon banɗaki domin ya birge ta kwarai da gaske, fitowa ta yi ta same shi ya shinfiɗa darduma yana jiran ta. Ba ta ce masa komai ba ya buɗe wardrobe ya ɗauko mata hijabi ta sa ya ja su Sallah, bayan sun gama ya dafa kanta ya dinga jero musu addu'oin samun zaman lafiya da kawar da fitina a tsakanin su. Tambayoyi ya mata game da addini ta dinga amsa masa tana wani kawar da kai, bayan ya gama suka yi addu'a suka shafa ta tashi ta cire hijabin har ɗankwali ta kalle shi. Murmushi ya mata ta ce “Mai hankali yanzu ni a nan ɗakin zan kwana?”
Gyaɗa mata kai ya yi sai ta rausayar da kai ta ce “Kai fa ina za ka kwana?”
Da hannu ya nuna gadon ta zaro ido ta ce “Gadon nawa ne za ka kwanan mini a kai? To ba zai yiyu ba ka sa katifar ta lomaƙe da wuri, kalle ka fa babba da kai..”
Dariya ya yi ya girgiza kai ya tashi ya fita a ɗakin a tunaninta ya tafi inda zai kwanta ne, har ta haye gadon ta ga ya shigo da ledojin da ya shigo da su ɗazu, kallon shi ta yi sai ta ji ƙamshin kaza ya kawo mata ziyara ta yi saurin saukowa ta iso gaban shi ta sa hannu ta amshe ledar. Waje ya samu ya zauna ya ce “Nasan kina jin yunwa amma tashi muje ku gaisa da Aminatou sannan mu dawo.”
Shuru ta yi tana tunani can ta kalle shi ta ce “To matarka kenan?”
E ya ce mata ta samu gefen gado ta aje ledar ta ce “To mu yi sauri mu dawo ni dai bacci nake ji mai yawa.”
To ya ce mata ya ce ta sa hijabi amma ta ce ita fa zafi take ji su tafi a haka kawai, ba yadda ya iya dole suka tafi kanta ko ɗankwali baki..
Aminatou na zaune a palo suna waya da Sabrin tana sanar da ita ai tun tuni Salim ya shige sashen amarya bai fito ba ko ya zo ya duba ta kafin ya shiga. Suna tsaka da maganar ta ji ana kwankwasa mata kofa, da sauri ta tashi ta ce “Sabrin ga shi nan ya zo.”
“Yawwa ki san yadda za ki hana shi kwana a can wajen yarinyar.”
Murmushi ta yi ta amsa da to sannan ta kashe wayar, buɗe ƙofar ta yi a hankali tana miƙa irin bacci ya soma ɗaukan ta, kallon su ta yi tana murmushi ta ce “A a haba ya za ka ɗauko amarya ka zo da ita bayan ta gaji? Wannan ai ɗaukan alhaki ne, da ganin ta bacci take ji ko Khadija?” Ta faɗa tana kallon Andizo da ta riƙe hannun Salim tana wasa da zoben da ke yatsarsa.
Kallon ta Andizo ta yi ta ɗaure fuska ta ce “Ai sai da na ce masa bacci zan yi ya tafi wajen kwanan shi ya ce zai kawo ni mu gaisa.” Ta faɗa tana kumbura baki.
“Gaskiya dai bai kyauta miki ba ƙanwata amma tun da kun zo ai sai ku shigo a gaisa ko?”
Kallon su Salim ya yi yana murmushi ya ce “ To ai sai ki ba mu waje mu shiga ko.”
Dariya Aminatou ta yi ta matsa suka shigo, a kan kujera suka zauna Salim ya gyara zama ya soma musu nasiha..
“Abin da ya sa na ce mu zo dan na ga lafiyarki kuma na miki godiya a kan namijin ƙoƙarin da kika yi a wannan lamarin, Allah ya miki albarka ya sa mu a gidan aljanna.”
“Amin ya Rabbi, a haba dai meye kuma na godiya sai ka ce ni na ba ka kuɗin auren ko na biya sadaki?”
“Haka nan ma naji daɗi yadda kika ba ni gwarin gwiwa, Aminatou ga Khadija nan ina so ku zauna lafiya nasan daga ke har ita babu mai matsala a cikin ku, amma Bahaushe ya ce yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, kuma an ce zo mu zauna zo mu saɓa, Khadija yarinya ce duk yadda kika bi ta a haka za ta dauke ki, ki kama girmanki saboda ta dinga ganin ki da girma a ko'ina, sannan ki ba ta matsayin ta na ƙarama kema Khadija ki girmama ta ki ba ta matsayin ta na wadda ta girme ki, ba na son fitina ko wasu abubuwan da za su kawo rikici, Allah ya muku albarka..”
Andizo da ta yi lamo a kan kafaɗarsa ta ce “In sha Allah zan ba ta girman ta, ai Hajja ta ce duk wanda ya girme ni na girmama shi na masa biyayya, amma in na ga yana zubar da girman shi na take na wuce, kuma ta ce duk abin ka umarceni kar na yi muso ko na ce ba za yi maka ba, har ita Aminatou Hajja ta ce na dinga zuwa ina gaishe ta da safe kuma na mata biyayya tun da ita ce uwar gida, kuma kar na mata rashin kunya kar kuma dan ina mata biyayya ta ce za ta mayar da ni baiwa, in tana mini haka to na daina mata biyayyar.” Ta faɗa tana turo baki gaba..
Duk da Aminatou ta ji haushin wasu daga cikin kalaman Andizo amma ta ji daɗi da aka ce ta mata biyayya ta ba ta girman ta na uwar gida, murmushin yaƙe ta yi ta ce “Karki damu Khadija in sha Allah ba mai jin kanmu kin ji.”
To ta ce daga haka ba ta kuma cewa komai ba, Salim ya miƙa wa Aminatou ledar da ya shigo da ita ta amsa ta mishi godiya, ganin zai tashi sai ta dinga jan shi da hira..
Wasa-wasa ta hana shi tafiya sai narke mishi take ƙarshe ma kuka ta sa mishi ta ce za ta yi kewar shi na kwanakin da zai yi a ɗakin Andizo, shi kuwa da ba ya son ganin hawayenta ya dinga rarrashin ta yana ba ta haƙuri, yayin da ita kuwa Andizo ta daɗe da yin bacci kanta a kafaɗarsa ta zayaye hannayenta a cikinsa. Sai da ƙarfe 12 daidai ta buga ya kalli agogon palon cike da mamaki ya ce “Kai ashe dare ya yi bari mu wuce ita har ta yi bacci.” Tashi ta yi tsaye tana cewa “E Wallahi ka yi hakuri fa na hana ku tafiya hirar ce ta mini daɗi.”
Ba komai ya ce mata ya ɗago da Andizo ya soma tashin ta, a hankali ta buɗe idanuwanta ya ce “Mu je ki kwanta.” miƙar da ita ya yi tsaye ya tashi ya kama hannunta suka nufi kofar fita Aminatou na biye da su, suna isa bakin ƙofa Andizo ta yi ƙasa ta jingina da ƙafar Salim ya yi saurin ɗago ta, ganin bacci ya ci ƙarfin ta ya sunkuya ya ɗauke ya saɓa ta a kafaɗa ya yi wa Aminatou sai da safe sannan ya fita ta rufe ƙofarta.. A jikin ƙofar ta tsaya tana tuna yadda Salim ya sunkuya a gaban ta ya ɗauki wata ya haɗa ta da jikinsa ya yi ficewar shi, fashewa ta yi da kuka ta isa kan kujera ta ɗauki pilo ta rungume tana tsine wa Andizo..
Suna shiga ya kwantar da ita ya je ya shirya cikin kayan bacci ya dawo, kayan bacci ya ɗauko ya cire mata na jikinta ya sa mata riga da wando farare sol, wandon bakin gwiwa rigar ƴar ƙarama ko cikinta ba ta ida rufewa ba. Tsayawa ya yi yana ƙare wa surar jikinta kallo, sosai ta masa kyau a cikin kayan ya hayo gadon ya kwanta tare da ɗauko ta ya kwantar da ita a kan ƙirjinsa ya lumshe idanu..
Bacci yake son yi amma ya kasa saboda yadda take juyi son ranta a kanshi, dole ya juya ya kwantar da ita ya rungume ta sai kusan asuba bacci ɓarawo ya kwashe shi, saboda ko runtse ido ya yi surar jikinta yake gani zuciyarsa na ingiza shi amma ya danna yana girgiza kai ya rufe ido da ƙarfi har ya yi bacci..
Kiran Sallah ne ya tayar farkar da Andizo, miƙa ta dinga yi tana salati ta buɗe idanuwanta ta ga mutum ya kanannnaɗe ta, kallon kayan da ke jikinta ta yi tana mamaki yadda aka yi aka canja mata wanda ta yi bacci da shi..