Sashe 1
Andizo Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[5/20, 10:01 PM] Ummu Amjad: _LITTAFIN ANDIZO NA KUƊI NE N300. +966577675904_
16
Mutsu-mutsu ta dinga yi tana kawar da kanta dan ta kauce wa rungumar da yake son mata tana daga kwance, komawa gefe ya yi ya kwanta yana huci hakan ya ba ta damar faɗo wa daga gadon tana kuka wanda sautin shi baya fita dan bakin a manne yake, kafin ta yi wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ganin shi ta yi a gaban ta yana ƙoƙarin kwanciya. Cikin maye ya fara maganar da ta sa numfashi Andizo ya ɗauke na wucin gadi.
“Kin san tsawon shekaru nawa na ɗauka ina dakon soyayyar ki Khadija? Tun lokacin da kika fasa mini gilashin mota kallon farko naji na kamu da son ki, shekaru huɗu kenan ina ɗauke da cutar soyayyar ki. Hakan ya sa na dinga bibiyar ki ta yadda zan sa a kamo mini ke. Yanzu ga shi kin zama matata jiya aka ɗaura mana aure ni da ke.” Ya faɗa yana ɗago da ita ya zaunar.
Idanuwan Andizo kamar su faɗo kasa saboda tashin hankalin da ta shiga, kalmar aure ita tafi hautsi ƴar jaririyar ƙwaƙwalwarta nan da nan kanta ya ɗauki zafi ganin ta ya tsaya na 'yan daƙiƙu. Sai da ya girgiza ta sannan ta buɗe ido tana kallon shi ta rasa me za ta faɗa masa, ita dai duk duniya ta san masoyinta ɗaya ne wato Saminu mai fanke, sai kuma Salim da a haukanta ta ce zai kaisu birni ita da Saminu su yi karatu in sun girma a musu aure. Sai yanzu take tunanin kenan Salim ma irin haka ne yake so a mata ita da shi? Girgiza kai ta yi ya ja mata hanci yana dariya ya ce “Sai kin haifi yara uku sannan zan kaiki ki gano danginki, kin ga lokacin za su fi farin cikin ganin ki da yaranki ba za su ce komai ba..”
Ita dai kallon shi take hawaye na bin kuncinta, so take ta zazzage shi ko za ta samu sassaucin abin da take ji amma babu hali, cire mata gam ɗin ya yi yana wani irin shan yaji ya ce “Khadija yi magana na ji, nasan kina son ki ce wani abu.”
Fashewa ta yi da kuka mai ƙarfi, gabaɗaya jikinta rawa yake tsoron shi ya kama ta musamman yadda ta ga jikinsa duk gashi ne kwance, sai da ta yi mai isar ta sannan ta tsagaita yana zaune yana surutan shi bai hana ta yin kukan ba sai ma dariya da yake mata.
Tana shashekar kuka ta ce “Allah ya isa tsaknina da kai azzalumi ɗan iska marar albarka, uban wa ya ce ka aure ni? Ko ba ka san ba ina da masoyina Saminu mai fanke? Kuma shima mai hankali ya ce zai aure ni ya kaimu birni ni da Saminu mu zama 'yan gayu, shi ne ka tafi ka aure ni saboda kai sheɗan ne..” Ta faɗa tana huci..
Kasancewar ba ya cikin haiyacinsa dariya kawai yake yi yana tafa hannu tare da cewa “Very good beautiful girl, you are the best friend.”
Matsawa ta yi dan ita dai ba ta san ba abin da yake faɗa, a masifance ta ce “To wa ya sani ma ko yaren su ne na 'yan iska yake faɗa mini dan nima na zama irin shi.”
Yunƙurowa ya yi zai mata amai ta matsa da sauri tana nuna shi da tsaya sai kuma ta sa kuka tana faɗin “Waiyo Allah Saminu ina kake yau ga Dijanka wani ɗan iska ya aure ta, Allah ya fidda ni daga gidan nan..”
Bacci ne ya ɗauke shi ta tashi tsaye tana kall-kalle ko za ta samu hanyar da za ta gudu kafin ya tashi, sai da ta gama duba ko'ina na ɗakin amma ba ta samu ƙofa ba dole ta dawo ta zauna a bakin gadon tana kallon waje ɗaya.
Tana nan zaune ta ji ƙaran buɗe kofar, da sauri ta kalli wajen suka haɗa ido da ita, ta tashi da sauri ta tare ta tana zubar da hawaye ta ce. “Don Allah baiwar Allah ki fitar da ni daga gidan nan na koma ƙauyenmu, ki taimake ni..”
Kallon ba ki da hankali ta mata ta wuce ta ɗauke kayan shaye-shayen da Sultan ya baje, sai da ta nufi kofar fita ta juyo ta kalli Andizo ta ce “Ai yarinya ke da fita daga ɗakin nan har abada, saboda ba a ƙasarku kike ba ballantana na taimaka miki ki gudu ki koma gida.”
Dafe ƙirji ta yi ta ce “Na shiga uku ni Dije! To a wata duniyar nake.”.
“Kina Abuja Nigeria, dan haka ki daina ma tunanin guduwa dan na san babu inda kika sani a cikin garin nan.” Tana gama faɗin haka ta kama kofar za ta fita Andizo ta yi saurin kama hannunta ta ce “Don Allah to ki nuna mini inda zan yo alwala rabon da na yi Sallah tun ranar da aka sato ni.”
Fisge hannunta ta yi ta fice Andizo ya mara mata baya amma tana zuwa kan kofar ta ji an hankaɗo ta an dawo da ita cikin ɗakin kofar ta mayar da kanta ta rufe..
Jim kaɗan sai ga ta ta dawo, kama hannunta ta yi ta nufi wani dan lungu da ke cikin ɗakin sai ga su a bakin wata ƙofa, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallon wajen dan ko kaɗan ba ta ga k'ofar ba sai yanzu.. Nuna mata komai ta yi ta yadda za kunna ruwan sannan ta fi ta yi tafiyar ta.. Andizo ta kasa kunna ruwan sai kallon banɗakin yake, da kyar ta iya kunnawa fitsarin ma a ƙasa ta yi saboda tsaron wajen da ta nuna mata take, alwalar ta ɗaura ta fito ta bi inda ta ga sun biyo ta dawo..
Shuru ta yi tana tunanin ina za ta ga kayan Sallah, bincike ta dinga yi a ɗaki har ta buɗe wardrobe ta samu wani dogon Hijabi da darduma a haɗe, cike da mamaki ta ɗauka ta shinfiɗa. Har za ta kabbara ta ji ta sake dawowa ɗakin, kallon ta ta yi ta ce “Anty ina ne alƙibila.”
Nuna mata ta yi ta wuce banɗakin ta wanke ita kuam ta tayar da Sallah. Haka ta dinga jero salloli har sai da ta ji bacci na ɗibar ta sannan ta zame ta kwanta a nan..
_NIGER_
Suna isa asibiti aka fito da gado Ahmad ya fito a sukwane suka ɗaura shi aka yi ciki da shi, kasa rufe motar Ahmad ya yi sai da Hassana ta zagayo kashe ta biyo bayan su..
A bakin ƙofar suka zauna Mamma da Ahmad duk suka yi tsaye suna kallon ƙofar . Suna nan tsaye sai ga Aminatou ta shigo asibitin afujajan mayafi a hannu tana rusa kuka, taro ta Mamma ta yi suka ƙaraso ta zaunar da ita tana ba ta haƙuri.
Ɗagowa ta yi ta kalli Ahmad cike da tsana ta ce “Kaine sanadin jefa shi cikin wannan halin, da ba ka je garin su waccan 'yar ƙauyen ba ai ba zai ganta ya ce yana so ba, har soyayya ta zame masa matsala. Ba shi da wani zance sai na Khadija kamar ita ce Autar matan duniya, Allah ya isa tsakani na da kai ban yafe maka ba na cutar mini da miji da ka yi.” Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye..
Baki buɗe Hajiya Babba ke kallon Aminatou ita da Mamma, shi kuwa Ahmad runtse idanu ya yi yana jin wani mugun takaici ya mamaye masa zuciya, in da tasan irin tashin hankalin da yake ciki bai kamata ta faɗa mata irin waɗannan kalaman ba. Girgiza kai ya yi ya juyo ya kalle ya, gabaɗaya ta ƙara ɓata masa rai ya ce “Wace ce ke a wajen shi? Ke jininsa ce ko danginki ne shi? Ai iya miji ne a gareki ko? Kuma ko da mutuwa ya yi wani za ki sake aura ki manta da shafin rayuwar da kuka yi da shi ni kuma fa ? Jinina ne wanda ko da mutuwa ya yi ba zan taɓa samun kamar shi ba har abada, ki kama kanki ba na son tashin hankali a halin da nake ciki, da banzar maganarki zan ji ko da halin da yayana yake ciki? Ni kin san ba tsaran ki ba ne yanzu kike son na miki jahilci Wallahi.”
Duk wannan maganar da yake faɗi in ba Hajiya babba da ke gefen shi ba babu wanda ya ji me yake faɗa mata, wani irin kallo ya aika mata ya ja tsaki ya ƙara da cewa “Zulwajahaini kawai, kamar wata ta Allah ke wai irin kina mutuwar son yaya Salim ko? To ki ci gaba da shiga gonata zan shata miki layi yadda ba kya tunani, ƴar rainin hankali in kin yi wasa da tunaninsu ni ba ki isa ki yi wasa da nawa tunanin ba dan na fi ki sanin duniyanci, kuma mu zuba ni da ke mu gani za ki gane Borno a gabas take.”
Dafa shi Hajiya Babba ta yi ta girgiza masa kai tana masa nuni da ya rabu da ita, ita kuwa ta cika ta yi fam sai gyaɗa kai take kamar ƙadangaruwa..
Tun da aka shiga da Salim likitoci suka dukufa kanshi, sun shafe fiye da awa huɗu suna ƙoƙarin daidai bugun zuciyarsa amma abin ya gagara, sai da yamma ta yi lis sannan suka samu nasara ya farfaɗo, kalmar farko da ya furta yana kallon samar ɗakin ita ce Khadija.
“Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ina Khadijana take? Don Allah ku ce ba da gaske ba ne tana gida, ina Ahmad yake? Ahmad zo ka ƙaryata mini abin da kunnena ya juyo mini ka ce wasa kake mini babu abin ya faru da Khadija..”
Cike da tausayawa babban likitan ya fito waje dan ya kira Khadijar da ya ji yana kira, gabaɗaya suka yo kanshi suna tambayar shi ko ya farfaɗo. Cire galashi ya yi ya dube su ya ce “Don Allah wace ce Khadija a nan? Sannan waye Ahmad?”
Da sauri Ahmad ya matso baki na rawa ta ce “N.. Ni ne likita, amma babu Khadija a nan.”
“To ku biyun nan tun da ya farfaɗo yake kiran sunanku, ka fara shiga kai ɗaya ban da hayaniya.”