← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 87

Sashe 9

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Don ubanki cewa nai zan sha."
Dariya fiyah tayi tana kunna kayan kallo tace"Allah yabaki hkr,naji ai sai bayani take kora maki kuma inba siye zakiyi ba mezai kawota."
Tsaki taja tana shigewa wata k'ofa tana cewa"to siyen zan don uban mutun ya hanani,ince kud'i nane bana wani ba."
Fiyah dai dariyar take don sun saba indai halin anty jamcy ne.
Fitowa tai da wata fation leda ga hannu ta zauna daker don cikinta yatsufa.
Tace Mata "inkina jin yunwa ga abinci can kan dining,akwai kunun aya a frig don naga kinaso nasa akai maki."
Cikin jin dadi tace"aikuwa wlh ngd Anty kinsan kuwa na kwana biyu ban sha ba,Allah yasa baiyyi k'ankara ba."
Ta fad'a tana isa wajen frig din ta dauko"aikuwa baiba nagode anty,Allah yaraba lfy."
Hararata tayi tana murmushi "baki cin abincin kenan"
Kunun ayar take sha tana lumshe ido tace"aa anty ban jima da cin julluf a cap ba,barni da wannan ma wlh ya isan.ina uncle yahya."
Gyara kishingidar ta tayi tace"bai kai ga dawowa ba,mezai maki."
Dariya tayi "aa nikuwa mezai mani anty,daga tambaya."
Tab'e baki tai tace"ga sak'onki inji muhsen,naso ku had'u kuyi bankwana da Allah kadai yasan arzikin da zaki samu."
Fara,ar dake kan fuskarta ta ragu sosai,cikin halin ko in kula tace"ni wlh da baki ansa ba,banson wannan bibiyar da yake mun ni nace bayanzu zan fara soyayya ba,balle akai ga maganar aure duk wannan hidimar bata da anfani ki ajiye mashi kayansa sadda ya dawo kibashi ni gaskiya bana so."
Wani kallo take mata cike da haushi,cikin fad'a tace"iyye,oh ke baki tashi soyayya ba balle ai maganar aure,kina nufin duk godolon da yake akanki baida wani anfani,yaro natsatstse kyakkyawa son kowa k'in wanda yarasa,kimaida hankali ki sakeshi ba fata nake maki ba daker zaki samu kamar sa."
Turo baki take tana k'unk'uni k'asa k'asa.
Dungure mata kai tayi tace"ubanme kike cewa halan ma zagina kike."
"Ni anty ba zaginki nake ba,wlh idan baba yasan ina kula wani fada xai man kuma yace aure zanyi in bar karatuna."
Harara take dalla mata "dallah can sokuwa ni ba saida nai aure na gama karatun ba,meyasa man kuma shikanshi baban idan yasan kin samu tsayayye ai murna zaiyyi,tunda baida wani buri daya wuce yaganki gidan miji."
Murmusa ido take tana y'an harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*."
"Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu."
Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya."n harare harare aranta tana cewa "wlh insha Allah kozan aure saina ga bayan matsalar *ABOUL-NASS*."
"Ubanme kike cewa kikiyayeni wlh,kibar ganina da wannan cikin ubanki zanci anshi nan kisata caji kafin sadda zaki tai,kuma inkinje gida kicewa mama da baba uncle dinku ya baki nasan bakinsu zai mutu."
Cikin rashin walwala ta ansa tana dubawa kwalin waya ne sabuwar Samsung galaxy s9 pink color dandanan kaunar wayar ya kamata,badan komi ba saidan suringa communicating da malik,murmushi tayi tace"ashe wayace anty,aikuwa ngd kice ina mashi godiya."
Kallon mamaki take mata da tuhuma.
"Ai nai zaton wani abunne na daban ba waya ba don yanzu nafi bukatar ta wlh."
Sake dungure mata kai tayi tace"banza kawai ki hanzarta kisa caji ga no dinsa nan ki kirasa don har sabon layi yasa maki da katin dubu da dari biyar,don Allah fiya kikirashi wlh muhseen yana masifar sonki,zanso ki samai kinga gani gaki kuma mahaifiyarsu batada wata matsala wlh lafoya lau zaku zauna kina ganin dai yadda nake zama dasu kamar zasu goyani."
Tabbas maganarta haka take iyayensu mutanen kirmine kuma yan gidansu basu wata matsala,muhseen da uncle yahya uwa daya uba daya suke,kuma suka dai ne maza sai kannensu mata su biyu,sun matukar son Anty jamila kamar yaua haka suka dauketa mamansu kau d'iya ta dauketa,sunada arx'iki sosai kuma baisa sun dauki kansu wata tsiya ba.
Kasai muhseen dinne ya cika yaga ko wata macen bata gwada mashi iyayi,kilan in iya saurarensa idan nagama da matsalar su ABDOUL-NAS.
murmushi tayi tana kallon Antyn tace"sorry anty zanty tunani akai don allah kiban lokaci,kuma zan kirashin idan naje gida yanxu test zan je nayi makaranta."
Cikin jin dadi antyn tace"kokefa sofyn mama,wlh muhsen baida matsala zakiji dadinsa."
Nata ce komi ba ta tashi ta sata cajin sannan suka cigaba da hirar su kamar komi bai faru ba.
Sai wajen karfe uku tatafi kasamcewar tayi waya da wata yar class dinsu cewar malamin bai zoba yace kowa yatai sai gobe da yamma.
Gida ta wuce tana murnan wayar,don asaukake basai tayi ta daukar ma mama waya ba.
KO da taje gida da wayar mama said mamaki take saida taji daga inda wayar take sannan hankalinta yakwanta,amman duk da hka tana tsoron abunda baban su zaice kan wayar.
Yes min kuwa kamar itace mai wayar sai jin dadi take,wayar tashiga dubawa kasancewar irin wadannan wayoyin tasan su tana anfani dasu wajen y'an class dinsu,yanzu kuwa ta huce wulakanci idan zatai browsing,basai taje tayi ta are are ba.
No din malik ta saka tayi save da sunan sa Abdul-malik.
Bayan dawowar baban su mama take sanar dashi wayar da mijin jamila ya ba fiyah,kiranta yayi tazo da wayar ahannu yace"sofiyya bazan hana ki rik'e waya ba,amman don Allah zan rokeki kirike mutuncinki,kar waya ta canza maki d'abi,u kar waya ta canza maki hali kar ta jaki ga abunda kika san zaki samu damuwa kisaka kanki."
Gabanta yafadi saitake ganin kamar Baban yasan manufarta,amman ai Allah bazai kamata da laifi ba tunda dai harga Allah taimako take niyyar yi tana son mai doshi cikin rayuwa irin wadda yayi duk da dai basanin abunda ya faru dashi tayi ba.
Cikin sanyin jiki tace"insha Allah baba zan kiyaue kasa mun Albarka to"
Murmishi yayi yace"sofiyna kenan to Allah yayi maki Albarka ya baku miji na gari."
Yesmin ta shagwabe fuska tayi tace"baba nifah to."
Dariya duk aka yi mata yace "kema Allah yayi maki Albarka ya baki miji nagari."
Tana jin dadi tace "ameen baba."
Bayan sun koma d'aki ta shiga kiran no d'in malik,lokacin ma yanata aiki don cikin satin yake saka ran zuwa switzerland saro kaya.
Alfah yana zaune kan kujera idonsa a lumshe ya shiga duniyar tunani,ahankali kuma zaka ga hawaye suna bin gefen idonsa,gorgiza kainkawai malik yake don baisannya zayyi da Alfah ba,yakasa daukar kaddara yakasa hkr da rayuwar ya ansheta ayanda tazo mashi.
Wayarsa yaji tayi kara ya dan kalla yaga babu suna kamar zai share saikua ya tsaya da aiki ayakin ya dauka,
tare da sallama.
Tana kwance lokacin ma harnyesmin tayi bacci don bata da wuyar bacci .
Itama cikin cool voice d'inta tayi mashi sallamar.
"Assalamu alaikum,ina wuni yah malik."
Jingina yayi daga jiin kuerar yaa maida hakalinsa kan wayar don yamaso saiwaye.
"Wa,alaiki salam wake magana pls."
"Sofiyya E-ladan."
Murmushi yayi yace"okyy fiyah ce,ykk yakika koma gida."
Idonsa nakan Alfah da har lokacin bai bude idonsa ba kuma ba bacci yake ba.
"Lafiya lau wlh yah malik ya na barka ya kuma rikitacce abokin ka."
Murmushinsa ya fidda mai sauti yace"bari nabaki shi sai ku gaisa."
Zaro ido tai kamar yana gabanta tace"rufan asiri ina zaman lfy wannan ai saika yah malik,wazai iya da wannan rikicin."
Dariyarsa ta fito har Alfah ya bude idonsa yana kallonsa "kin cika tsoro wlh,amman soon zaku saba yanzu ya zai muhad'u gobe around 4:00."
Ajiyar zuciya tayi tace "inada test lokacin yah malik amman mezai hana da safe zuwa yammar."
"OK hakan ma is ok 10:am yayi mki ko."
Murmushi tayi tace "yes yayi insha Allah amman ina zan sameka."
D'an shiru yayi yana kallon yadda alfah yake mashi kallon tuhuma yace"zan maki text da safen."
"OK yah malik sai da safe zan kwanta."
Sallama sukai ya ajiye wayar har lokacin idon Alfah na kanshi yasan soyake yayi mashi bayanin wacece amman miskilancinsa bazai barshi ya tamaya ba,shima kuma sai ybiye shin yayi shiru ya cigaa a aikinsa.
Zuwa can ya tashi cikin fushin sa na farillah yayi ball da table d'in dake gaban sa ya wuce bed room d'in sa.
Malik yace "Allah ya yaye maka ya kawo maka sauki cikin lamarinka."

DON ALLAH KUYI HKR HIDIMAR SUNA MUKA SHIGA SHIYASA BAKWAJINA KULUM,AMMAN DAMUN GAMA INSHA ALLAH ZAKUJINI KUYI MALEJI DA WANNAN.

MRS BB CE
MOM MUHSEEN.
[9/17, 3:36 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

*Wannan page d'in nakune masoyana,inhar kinsan ke masoyiyata ce mai nuna kauna gareni to nakine na sadaukar dashi gareku,saboda irin soyayyar da nake samu daga wajenku,Allah yabarmun ku ya kuma kara mana kaunar juna,kuma baby humaira tana gaida kowa da kowa da irin aduar da take samu daga gareku.*

🅿️.........10
Chapter 9 · 0% Book details