← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 87

Sashe 87

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

taga kulawa wajen mami da mama kowa dake sonta yana son cikinta yaya jalal yazo sai lokacin suka shirya sosai yana kuma nuna mata jin dadin samun aikin sa,feea tazo har gidan mami inda suka sauka sunsha fira da ita take cewa har yau ba,a fiddo dady ba amman Abbi ya sauko yace zaitaimaka insha Allah zai fito lokacin bikinta ya taho baifi saura sati uku ba.
Shima yaya jalal ansaka ranarsa da hasana ta wajen inna balaraba anyi bikin feea da sati guda za,ai nashi.
Zakiyya ma cikinta yafito amman fiyah saita rigata haihuwashoyasa mami tace Abdoul nan zaibar fiyah harta haihu shikuma yace bazai koma ba har saita haihu sukoma tare.
Mami tace"kota haihun saita gama wanka inkana kama hanya katai katafi ajiko"
Badan ya so ba fiyah harda kuka ranar daxai tai dama malik shi yana nan abunsa,bayan tafiyarsa da sati uku akai bikin yaya jalal ya dawo ya hakarci taron daurin aure ya kuma ba ango kudi masu dama sosai.
Anan cikin estate din Abbi ya bashI gida akasa hasana aciki,lokacin cikina wata tara zakiyya kuma bakwai kuma kamar yadda Yaya Abdoul kefata twis ne mace da namiji kullum zullumin zuwan haihuwar nake karshe dai tazo da matsala dole akai cs akafiddosu yara masu ruwan kyau inji Anty da yesmin.
Yesmin din itama lokacin danata rabon wata shidda ,wadannan jarirai sunga gata baga ubansu ba baga kakarsu mace ba ba kakansu maza ba kowa dokinsu yake naga gata nikaina ,babansu kamar zai cinyemu nidasu haka muka dawo gida nai jinyar ciwona komi mami da ni,ima keyi mun mama da nata gujiri take aikowa ana kawomun ranar suna yara sukaci mamana da Abbin yaya Abdoul.
Munga hidima mai sunan hidima tunda babansu ya dawo yaki komawa har saida na gama wanka duk da na towel ne saida nacika arba,in cif

Nasha gyara mami gwanace sosai ganin ina samun kulawa daga mami yasa mama ta kwantar da hankalinta duk da banma haihu da kaina ba saida ta gyarani sosai yadda bazan cutu ba har kunyarta nakeji amman ita babu ruwanta.
Jaririyar ana ce mata afnan jaririn kuma Affan sun ganin kauna kowa sonsu yake yadda suke da shegen kyau kamar ba diyar africa ba.

Dazamu wuce kuka riris nake yi daker na baro gidan mama itama mamin kamar zan ballata haka aka rabamu jirginmu yatashi sai zakiyya ta haihu kozan zo ni.
Mami ta hadani da yar aikinta guda yar yarinya ce bata wuce shekara sha biyar ba uwarta ma tana tare da mami.
Nakoji dadinta don tana kulawa dasu Affan.
.
Yaya Abdoul kuwa kamar zai maidani cikinsa haka yake likemun gani nake ma yanzu yafi nanikemun akan sadda ina ina amarya nima kuma ina enjoying sosai don kamar wani sabon amarci mukeci don yayi hkr sosai rabonshi dani yafi wata hudu tun cikina yana wata takwas naji kuma ban son abun.
Har na haihu kuma nai wata wajen biyu sannan ai yayi kokari.
Muncigaba da rayuwarmu cikin kwanciyar hankali ina kulawa da twis sosai Abdoul yana sonmu yana mana komi zakiyya ta haihu ta samu namiji sunan baban yaya malik akasaka suna kiransa da walid.
Yesmin ma ta haihu itakuma mace ana ce mata salma haka rayuwar ta cigaba cike da jin dadi duk da baka rasa kalubale ba ni nawa yan matane suka addabi habibi kullum ina cikin kishi amman ganin shi bata su yake ba yasa na maida hankalina kan mijina ina kulawa dashi yadda ya kamata.

Dadyn feea ya fito bacin bakar wahakar ya caza kamanni ba ma lallai ka ganeshi ba.su mamman har yau suna magarkama babu ma ranar fiddosu.umma kau saidai mukaji labarin mutuwarta gawar kuma gudaje suka hau kai sunaci abundai babu kyaun gani bayan shekara biyar na sake haihuwar mace sunana aka samata saboda Abdoul yana masifar sona muna kiranta mimi daga nan ban sake haihuwa ba muka cigaba da tarbiyartar da yaranmu na gama karatuna amman bana aiki saboda Yaya Abdoul ya gama mani komi kasuwanci nake kasa ruka zan iya cewa komi sai hamdala zakiyya yaranta biyar cif yesmin kuma uku kamar ni Anty biyar itama hasanar yaya jalal daya.
Rayuwa tayi kyau komi Alhamdulillah munzama family na gaske nidasu Abdoul

*ALHAMDULILLHAI TAMMAT ANAN NAKAWO KARSHEN ABDOUL-NASSER DARASIN DAKE CIKI ALLAH YASA YAJE GA MASU KARATU NGD DA SOYAYYARKU ALLAH YASADAU DA ALKAIRI IDAN NAIMA WANI BADAIDAI BA YAYI HKR HAKA TSARIN RUBUTUN YAZO,SAI MUN HADU CIKIN ABU KHALIPHA INA ALFAHRI DAKU*

BISSALAM.
Chapter 87 · 0% Book details