← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 87

Sashe 51

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuna ma dadyn yayi yace"gasunan dady zamu fara da videon ne ko mu gama sauraren audion sannan"
Bayan ya duba yace "kunna audion muji"
Jikin malik na rawa ya ja aro din computer zuwa wajen audio ya yi double click dinsa,dan danan yafara loading zai bude.sudukan gabansu ke faduwa don basu san me zasu saurara ba,yadauki almost 3mint sannan ya bude muryace tafara magana,wadda nan take suka dago ko murya waye.
Watau muryar umma tana cewa"kwangila ina cikin tashin hankali,bacin tsana da kiyyar danake yiwa Yaron nan Abdoul nasser ya sake jefa kanshi cikin wani bala,in domin kuwa ajiya ina mai tabbatar maka da cewar ya gannmu sadda muke aikata son ranmu,idona idonsa bakin window wlh har ihun da kake yi akan kunnensa har saida yatoshe kunnensa,yajinjina kai yayi kwana yabar wajen.duk da nasan bazai gaya makowa ba dole ne mudauki mataki akansa,don kuwa zai zamemana barazana ga zamanmu dagani har kai"
Alh kwangila ya sauke numfashi yana share gumi yace"innalillahi nashiga uku wane irin bakin labari kike gaya mun,har kice bazai sanar dakowa ba taya kikasan haka,to gaskiya niba zan dauki lokaci waje ganin mun kubuta tunda bacin shi babu wanda yasan ina zuwa wajenki muna muamala dajuna,kuma bacin haka mariya banajin akwai wanda xai dakatar dani daga muamala dake,kin sani tun kuna farkon xuwa unguwar nan nazama mijinki na biyu,kina mun dadin da matana bata taimun,don haka dolene zai dauki mummuna mataki akansa,kinga hanyar dakike nema wajen ganin kin kawar dashi daga gidan,domin kisamu damar tattare komi kafin plan B ya fara aiki ko"
Dariya suka kwashe suduka harda sautin kashewa dasukai dajuna,tace"in maka na turawa zat wai ai lobiyu"suka sake kwashe wa da dariya kamar mahaukata.
Yace"yanzu kina da wata dubara kowata shawarar yadda zamufara bulloma lamarin ko kinbar komi hannuna."
Jim tayi tana nazari tace"abunda nake so kwangila wani tuggu nakeson ahada mashi,wanda bama mutanen cikin gidanna kadai ba har jama,ar gari kowa yatsanesa incusa tsanarsa cikin ran mahaifinsa ta yadda zai mashi mummunan kalamin da koxuciyar kare garai bazai sake tako kafarsa hanyar unguwar nan ba,ta haka zan saka mamman ya maye gurbinsa mumallake abunda nake hari shekara talatin tun ranar da aka haifeshi shegen yaro yazo da arxikin da shikanshi uban baiyyi tunanin zai samesa ba.shegiyar uwarsa daman ni bana kallonta wata matsalata da zaran na kora dan nata itakuma nasan ta inda zan biyo mata."
"Kinata surutu baki gaya mun yadda plan din zai kasan ce ba"
Murmushi tayi tace mekake ci na baka na xuba,zakaji amman saina gama tsara komi kasan zakiyyata suke soyayya,da har nafara daukar mataki akai sai yanzu kuma wani tunani yazo mun,don haka dole da zakiyya zanyi anfani,katashi katai kafin yarana sudawo su sameka don kosu ban bari sunsan ina bin mazan waje ba"
"Mariya kice bani kadai nake nitso cikin fadamarki ba,har wasu kike bi awaje"
Tsaki taja tace"to meye kaidinma ai bani kadai kake ma aiki ba,ansha gaya mun kana xuwa hotal kana shanawarka da yan shilan yara,to donme zan zauna dakai kaidaya kamar rai,mijina ma ban zauna dashi shikadai ba saikai,nimubar wannan maganar katashi katai zan sake tunani kafin na nemeka,nasan ma kafin na nemonka kai kakawo kanka maye kawai,kai mace bata taba isarka."
Dariya yayi yace"inma zaki karaman wlh so nake don waccen dusar yadda kikasan hanyar da babu titi haka take,"
"Nibanson wulakanci,matarka mace mai kirki da tsafta da kiyaye wa amman karinga cin amanarta wlh sai Allah yasaka mata,amman dai shikenan tashi kabi ta baya kafece kafin aganka"
"Shikenan saina sake zuwa"
Daidainan audio guda ya kare.

Shiru sukai kowa yana saka wa yana warwarwwa cikin ransa,dady yajima yakasa magana don wallahi daman zargin dayake kenan,amman bai taba kawo cewar suna neman juna ba kawai dai yasan cewar umma da Alh kwangila akwai saka hannunsa cikin wannana lamarin.

Malik daskarewa yai yaka sa motsawa,maganganun sunyi masifar daure mashi kai,har rashin imanin umma yakai haka.
Wata xuciyar tace bakaji komi na sai ka gama saurarar sauran.
Ajiyar xuciya yaja yana kallon agogonsa yadago daker yace"dady zanje na duba jikin Abdoul wata kila ansallamesa yanzu,zuwa gobe insha Allah sai mu idasa sauraren sauran,zanbar computer anan saboda tsaro."
Dady bai iya magana ba saidaga kai dayai,malik yafice daga falon yanajin kafafunsa suna mashi nauyi.

*kuyi hkr da wannan insha Allah zan baku na dare*

Don't share it plss
Bcos its for sale 300 naira ne gamai bukata.ya tuntubi wannan no din.
09034722970
[9/17, 3:42 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........42

"Naam"
Can kasan makoshi ta ansa kiran da yayi mata
Shiru suka sakeyi sai musayar numfashi dasuke,dan maxewa tayi muryarta kamar daga frig aka fiddota tace"wake magana,nai tunanin yaya malik ne sai naji ba muryarsa bane,who is on d line"
Idonsa dake lumshe ya budesu akan malik dake kallon news,sannan yabude baki daker yace"malik kai take nema"
Gabanta yafadi badai ajiye wayar zai ba yabarta da wannan kullellen mikin dake cin ranta,malik yace "ba nema na take ba kaidain dai take nema kasake saurare kaji"
Taji abunda malik din yafada ras tayi murmushi kasa kasa tasake kwanciya tace"oh sorry yaya Abdoul ne ashe ina wuni,ya karfin jiki Allah yasa kaffarane"
Ajiyar xuciya yasauke yana cewa"nagode,yajikin baban?"
Bata san sanda muryarta take komawa yar karama ba tace"yana samun sauki,may be gobe musamu asallamesa"
"Okay"
Jin muryarta yake kamar yau yafara jinta,tundaga yatsansa na kafa yajin wani yanayi har cikin kansa,shirun itama tayi tana kwance kamar zata tsaga katifar tashige cikinta.
"Ina zakiyya?"
Bude idonsa yayi yabin hanyar dakinta da kallo,sai yasamu kansa cewa"gata nan kusa dani"
Wani kullutune yazo mata wuya ya tsaya,duk miyan da take hadiyewa yaki wucewa,shiru tayi shikuma yasake anfani da yin shirunta yace"yana mun firane inasamu bacci,taje ta hado mun tea insha idan ta dawo zan baki saiku gaisa"
Runtse idonta tai tana damkar zanen gado tare da sauke wani wahalellen nishi,mai tafe da hawaye.saurin rufe bakinta tai don ba wuya kukan na iya tahowa.
"Are u on the line"
Shiru tayi tana sake rufe bakinta,tana kukanta ahankali can kasa sosai.
Natsuwa yayi don fahimtar yanayin ta,ahankali yakejin numfashinta yana sauka da sauri,yanayin kukanta yana shiga kunnensa.
Tsikar jikinsa ce tatashi don kukan ta yatada mashi hankali ainun.
Kin nuna mata yayi badan hakan baya taba shi ba,aa yana tabashi har cikin ransa amman dole zai bita ahaka badan yaso ba.
*"sofiyyerh"*
Ahankali cikin voice dinta data sha kuka tace"naam"
Runtse ido yayi yana damke hannunsa jiyake kamar tana tafiya da numfashinsa,muryarsa silently so sweet yace"kina kuka ne"
Daker tace "uh uh"
"To menene?bakison zakiyya na mun firane"
Ajiyar xuciya ta sauke tace"ina ruwana da hirar da take maka,meye nawa idan nace kar ta maka fira,kunfi kusa ai karka sake sani cikin batunku pls"
Murmushin da bai shirya ba yayi har tana jin sautinsa yace"oky don't worry baza asake ba,hope kinyi exams lafiya"
Kin bashi ansa tai tace"zanyi bacci saida safe"
Lauya muryar yayi yace"oh sorry to kiyi baccin ki mana,zan so haka ma"
Tsaki taja kasa kasa tace"kashe wayarka"
"Kekika kirani ashe?"
"Ban Sani na malam karka mun gori ai ban roki kakira ni ba balle ka raina mun hankali,"
Dariya tafara cinsa wadda bazaice ga lokaci. Daya yita ba.
"Masifatu kurin,karki sake ki mun rashin kuya wlh har nan kan gadon naki zanzo na baki punishment,wanda nasan zai ladaftar dake."
Yafada da wata irin murya hade da salo wanda nan take ya idasa kashe bakin fiyar.
Shirunta dayaji yasa yayi murmushi don yasan sakon yaje,dariya yayi ta burgewa yace"matsoraciya,har kin tsorata da wuri tun kafin ma inzo,uhmm kinsan hukuncin naki ashe shiyasa kikai shiru."
Ahankali kamar mai koyon magana tace"angaya maka ni Allahn musuruce dallah can saida safe karka sake kirana"
"Okay Zane ringa kiranki sau uku arana,yayi maki ko"
Tsaki taja tace cikin masifa"dalla cewa nai karka sake kirana"
"Oh yayi maki kadan sau ukun,kenan sau biyar zan kira din."
Batasan dariya ta kubce mata ba,don yadda yake juya mata magana abun ma saiya bata dariya.
Shima taya ta yayi da murmushi mai tsada wanda da agabanta yake saita kusan suma don yadda zai daukar mata hankali.
"Angaya maka ina bukatar kiranka?to inkakira ni mezan maka kokuma meza kaimun"
Kamar yana rada yace"wai in ringa ladabtar da bakin nan naki mai rashin kunya"
Babu shiri tayanke wayar don yama shirin kaita inda bata da mai maidota.
Wanna dare dai xukatan mutun uku basu huta ba,zakiyya sabon son Abdoul dinne yayi mata dirar mikiya,jitake kamar yanzu ne tafara sosan bata da wani fata da burin taga sun june har takaisu ga mallakar juna,amman tasan akwai kalubale sosai don Abdoul hankalinsa baya kanta ahalin yanxu,ya zatai ta dawo da soyayuarta sabuwa cikin ransa.
*SOFIYYAH* wata xuciyar ta anbata mata tabbas zata iya daidaita su har ma kilan sudawo sufi da son juna,zata nemota itace kurin hope dinta.
Abdul kuwa saida yayi dagaske sannan ya samu bacci don kwata kwata xuciyarsa babu komi ciki sai shaukin son kasamcewa da wannan yarinya mai daukar hankali,gabaki daya baisan yadda zai misalta yadda yakeji ba,shidai yasan yana shan wuyar kewarta na kwana biyunnan.
Haka yake ga fiya murje murje taitayi agado xuciyarta tana saka mata tana kwance mata,amman kishin zakiyya yaddane duk wani feelings dinta akanshi,hakika yadda takeji ga xuciyarta bazata iya shiga tsakaninsa da zakiyya ba,don ita masaniya gareta akan soyayyarsu.koda xuciyarta tayi kokarin ganin ta kaita inda bata dace da wajen ba,ita zata janye kanta.don bata iya daukar rebel sai goshin asuba bacci ya dauketa.

Washe gari da wuri tatai school don eight sukeda exams yau sai shidda zasu dawo gida,don ko break bata tsaya ba feea na xuwa suka wuce yau da mota tafito.
Mama tace idan tataso tayo gida kurin don da rana zasu sallamesa suyo gida.
Chapter 51 · 0% Book details