← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 87

Sashe 60

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fiyah ce zaune gaban baba tayi shirin fita exam don yau suna da peper.
Tare ma suke karya wa mama dan wake tai masu sanan aka dama kunun gyada,suna ci suna hira gwanin sha,awa yesmin na gefe itama ida mama kwanon su guda.
Ganin yadda fiyah ta sake take ta annashuwa hakan yayiwa baba dadi,yaga damace daya kamata yayi anfani da ita wajen yi mata zamcen yaron nan muhseen.
Cikin jan hankali da natsuwa baban yace"uwata wannan jarabawar itace ta karshen gama aji daya ko?"
Tana kurbar kunan gyadar tace"eh baba itace,amman sai munje hutu munkoma mun sake wani karatun munyi wata jarabawar sannan mushiga aji biyu"
Jinjina kai yayi yace"masha Allah kinga daman burina biyune akanku kullum keda yesmin,"
Kallonsa tai tace"baba wane irin buri kake dashi akanmu"
Murmushi yayi yace"inason inga kun fadada iliminku bayan na secondary,inga kuma daidai gwargwado ban tauyeku ba kuma kun samu ilimin da zai taimakeku agobenku,bayan nan uwata kullum fata nake da burin Allah ya fiddo maku da mazajenku nagari wadanda zasu rikemun ku cikin amana da mutunci kamar dai yadda uncle dinku hake rike da antynku cikin kwanciyar hankali babu maijin kansu"
Gabanta yafadi sosai har ta kasa kai dan waken dake hannunta cikin bakinta tace"baba ai banfa gama karatunba,duk fa ko rabi banba akwai aiki gabanmu sosai"
Murmushin yayi yace"ai uwata shi aure baya hana karatu,haka karatu baya hana aure aduk sanda kasamu damar yin guda inhar anyarje maka saikaga kayishi cikin kwanciyar hankali,"
Gabaki daya ta rude dajin kalaman baba meyake nufi da ita,innalillahi Allah kasa ba wannan shegen muhseen din yazo ma baba da wata magana ba,wlh van sonsa bana sonsa.....idonta yadan caza tace"baba ai babu wanda nake kulawa tunda karatu nake in wani yazo saina gabatar dashi wajenka"
Mama kallonta tai ta fahimci wani abu game da diyar tata,idan batai kuskureba tasan maganar da baban ke shirin yi mata,wanda yasa take kakkaucewa.
"Ai kwantar da hankalinki uwata,Allah yana sonki don ya kawo maki miji har gida kuma wanda nake maki fatansa da kwadayinsa,badan abun hannunsa ba ko don kudin magabatansa,aa nagartarsa naduba da hankalinsa da natsuwarsa yasa banyi shawara dake ba nai na,am da maganarsa don haka kowane lokaci zaki iya ganinsa yazo wajenki."
Bata son fiddo kwallarta gabasan yasa ta sadda kai tana kokowa da kwallar cikin kermar murya tace"waye baba,ni banda wani wanda nakeso kuma ban turo kowa ba wlh"
Duk yadda taso karya gane rudewarta saida ya gane yace"kwantar da hankalinki ki natsu uwata,muhseen ne kanen uncle dinku.kema kinsan bashida wata matsala karkiyo tunanin komi,cancanta ce yasa nabashi ke kuma inada yakinin zai kula dake yadda yakamata ahankali zaki fahimceshi kuma har kisoshi."
Idan tace zatai magana kukanta bayyana zaiyyi shiru tai tana zare hannunta daga cikin kwanan dan waken,amman kafin ma tatashi yesmin ta rigata ta fice tana tari da alama kware tai.
Ahankali kamar wadda kwai ya fashe wa aciki take fita daga dakin,kallon yesmin take durkushe gaban maguji tana kuskure bakinta,idan ba gizo idonta yake ba kwallace ke fita daga idonta,tana gogewa kasa kasa tsura mata ido tai harta wanke fuskarta ta shige dakinsu bata kula fiyah ba.
Jinjina kai tayi tana godewa Allah data kawo mata wannan damar,don kuwa bazata iya musawa baba cewa bata son muhseen ba,amman idan ta fahimtar dasu cewar yar uwarta naso hakan zaija hankalinsu su duba maganar.
Wajen dalha taje ta anshi kudin taxi tabar unguwar xuciyarta cike da abubuwa.

💞💞💞💞💞

Wayar da akaimashi can caji office yasa ya tashi don bai niyyar fita ko ina ba yau,shiryawa yayi yanayin sa kwata kwata yau ahargitse yake.neman wanda zai juyewa masifar shi yake.
Har zaifita idonsa akan jikkar fiya.
Dawowa yayi ya dauketa yafifa,ko kallon kitchen baiba inda yake jiyo mktsin mutun yasan zakiyya ce,don har yanzu akuke yake da ita.
Driver sa dasuke fita office ne yazo yace"yallabai yau babu office ne"
Cikin shan kanshi yace"eh"
Juyawa yayi yabarsa don yaga kamar cikin fushi yake.
Yadda ya figi motar kasan kiris yake jira,gudu yake don yaje da wuri dpo din yace mashi ga yallabai nan ya sake dawowa neman belin su.
Shikuma duk bala,in da za ai da masifar da za,ai bazai bari su kubutaba yau zaifuskanceshi bayan tsawon shekaru,yadda yake nuna mashi shidin ba dansa bane shima zai rufe ido ya nuna baima taba sanin sa ba,idan ma kotu za,axaje akan maganar ashirye yake.
Go slow ya tsayar dashi idonsa ya sauka kanta tana cikin taxi,kanta kasa kamar tana duba wani abu.
Saurin dauko bag din yayi zaifita saikuma ya fasa,yana son ganinta akebance wannan damace da zaije gidansu anjima.
Koma wa yayi yana cigaba da kallonta jiyayi duk wani kuncinsa ya na yayewa,xuciyarsa tana sauka sabanin yadda yakejin wata irin temper tana taso mashi.
Kamar kar yatafi yakeji amman babu halin hakan yana gani suka wuce shi shima ya wuce inda zashi.

Malik bai tashi da wuri ba sai kusan shadaya wanka yayi yafito yayi break zakiyya ta gaidashi ta shige daki,binta da kallo yayi yana mamakinta to aibashi ya kashe xomun ba.
Waya sukai da dady yake tambayarsa Andoul na gida.
"Wlh daddy baya nan,yafita tun safe amman bari akirasa aji,"
"Aa kyalesa nasan inda zaije yana station kan case din safiyyah yana can shida mahaifinsa inajin tsoron kar xuciyarsa tajashi wani abu yafaru awajen shiyasa amman bari naje kaima inkana da time mu hadu can."
Ai malik najin haka ya kafa kai ya shanye sauran costand din ya zari wayarsa don bazai fita da mota ba,addua yaje Allah yasa kar yaje ya aikata abunda bashine ba.
Taxi ya tara yagaya mashi inda zai kaishin.

Station

Yana isa yaga motoci har guda uku yasan Abbin ne ya iso,fitowa yayi ya sake hade fuskarshi murtik kamar an aikobmashi da sakon mutuwa.
Wani dan sanda ne yake bakin kofar shigar yasaka kafa ya ingijeshi yashiga.
Biyosa yayi a fusace yana finciko rigarsa ta baya "uban waye kai da har zaka ingijeni kai makahone ehy..............naushin da ya kai mashi shiya janyo duk hankulan mutanen dake cikin station din.
Saida Abdoul yafasa mashi baki sannan ya wurgar dashi yana huci.
Abbi dayayi ido hudu da yaron nashi,duk zafin daya debo don juyewa akanshi saiyaji xuciyarsa ta karye,bayan shekara shidda ashe zai sake yin ido hudu da dansa,gudan jininsa.jikinsa yaji har wata rawa yake saboda tsuma da son rungumeshi ajikinsa,saidai yasan hakan bazata yuwuba yadda yagansa cikin wanna zafin ba tantama idan ya tabosa abun bazayyi kyauba,daman ga yanjarida canawaje sunajiran kiri sushigo sudauki rahoto.
Watairin kaunar dan nashi yaji ta kamashi idonsa kamar zayyi kuka yaje inda yan sanda suka kakkamashi yace"ku sakeshi karkuji mashi rauni mana,ai laifin sane baiga ayadda yashigo wajenba ne zaiyi jaking dinsa."
Sakale sukai da bakisuna kallon sa don sun san ba haka ya shigo ba yana zage zage ya shigo yana cewa duk ubanda ya bada umurninkar abada belinsa akirasa yanajiransa.amman gashi yanzu kuma sunga ba haka ba,shiyasa wani daga cikinsu ya nemo yan jarida yasan zai samu wani abu idan suka amu wannan labarin.
Idon Abdoul yayi jaa yana kallon Abbin nashi can kasan ransa yana jinwani irin feeling amman sabkda abubuwan dasuka ringa dawo mashi na can baya sai yadanne yafixge daga rikonsu yana zakuda kafadarsa cikin bala,I yace"ina ruwanka da koma me zasuyi man?nace meye ne yasha feka dani muazzam,kabari suyi mun koma miye mana meye hadin kifi da kaska."
Abbi jiyayi zuciyarsa tana ragargajewa rauni yana sake kamata wata irin nadama da dana sani suna shigarsa,matsawa yake inda Abdoul din yake muryarsa tana rawa yanason rikosa "daina daga murya yarona,nine fa Abbinka Abbinka ne maionka........dalla malam dakata anan karka sake ka nufoni,don zan maka rashin mutunci nace karka matsoni ko wlh zan maka abunda baka taba tunani ba."
Alfah ke fadara haka yana hawaye,yanajin kamar ya dunga buga kanshi da bango.
Hankulan mutane yafara yowa nan wajen.
Abbi tuni idonsa yafara zubar da kwallar yana cewa"nine babanka Abdoul karka manta dani kar xuciyar ka ta saka maka tsanata,zoga babanka kajiko matso."
Ja baya Abdoul keyi yana sake cewa"wlh idan ka matso inda nake saina kashe kaina,yafige wata bindiga daga hannun wani dan sanda yana saita kanshi da ita,daidai isowar yan jarida kenan da kuma zuwan dady da malik.
Cikin rudu da rikicewa Abbi ya rike hannun dady yana kuka kamar ba babba ba yace"kaimashi magana karya halbi kanshi,kaje ka anshe bindigar yana iya halbawa tsoro nakeji inhar kana sona karka barshi yayi abunda yake niyya........ina sonsa ina son dana kaceceshi."
Riko duka hannayaen Abbi yayi dadyn yana cewa"kwantar da hankalinka bazai aikata ba,ka natsu don Allah kalla fa kaga mutane yadda suke kallonka haba yallabai."
Malik ne yayi saurin rike hannun Abdoul dake saita kanshi da bindigar yana sakin iyakar karfin sa,yana koklwar ansarta.
Bilhakki da gaskoya kuka yake yana cewa,
"Wallahi muffin yah I nasarar ceton wadancen yan ta addan saina yi abunda zaisaka dagani harshi mukare rayuwarmu agidan yari.taya zaoyyi yukurin ceton mutanen dake da hadari cikin al,umma masu satar jama,a suna yimasu allurar maye........kasakeni kafin kaima nayi maka illah...........wani gigitaccen mari dady ya sakar mashi yana sake lafta mashi wani marin,don baida wata dubara da ta wuce haka,yayi gigiceqr da baya saurren kowa.
Shirune ya raysa wajen ya juya ga yan jaridar yace ma yan sandan duk wanda kuka kama cikinsu ku garkame shi tunda neman labari suke sai subada nasu yan iska ,basu da aiki sai neman rahoto suje su yayata."
Abdul silalewa kasa yayi yana wani irin numfashi kirjinsa yana dagawa kamar zakifita daga jikinsa,inbada rawa babu abun da jikinsa keyi dole malik ya cikashi suna xuba mashi ido.

Don Allah kuyi hkr wlh yau nashiga busy ga bakuwa danai ga hidimar gida shiyasa kuka samu wannan kuyi hkr plss.
[9/24, 5:37 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️........50
Chapter 60 · 0% Book details