← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 87

Sashe 24

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin kwana kin da yayi Australia jinshi yake daban,saboda yadda duk d'abi arsa suke son juyewa sukoma wasu kala dabam,tunda yazo sau d'aya yasha mutuniyarsa,itama kuma baita zauna ba saboda rashin bawa kansa hutu da ishashshem bacci yasa masassara ta kamashi,randa yashata kwana yayi yana amai jikinsa kamar an masa dukan bala,i........daga lokacin bai sake nemanta ba yana son yasha amman daya kai bakinsa kalaman yarinyar da ko sunanta bai sani ba suke dawo mashi ras,kamar lokacin take sanar dashi su.
Fiyah kau saida tayi jinyar kwana uku bata je ko ina ba,da yake juma,a ne kurin ba taje makaranta ba sauran kwanakin anshiga weekend ne.
Baba ya wartsake ya koma hidindumun sa na yauda kullum,ya fita batun Alh muazzam don yanzu zaman lafiya yafie mashi komi da kuma zama cikin iyalinsa,tunda yagane cewar inhar baka dashi to kau kaine wulakantacce,ko da kuwa kwana kake masallaci kana sallah.duniyarce ta lalace anzo wani zamani da saidai ace innalillahi wa inna ilaihir raju,un.
Feea kuwa tana can tan fama da dakon soyayyar Abdoul,ga shirye shiryen bikin Abbanta babu abunda akafasa,don kamar baitab'a aure ba haka yakeji komi na gidansa an sakeshi......har lokacin kuma mominsu bata dawo ba.
B'angaren fiyah da Malik kuwa suna waya sosai don duk rana zai kirata da safe suyi kusan minty talatin suna waya,sannan yakira da rana ya kuma kira da daddare,shakuwa ta shiga tsakanin su sosai fiyah ta sake dashi har idan bai nemeta ba tana kan gaba wajen nemansa.........ana gobe Abdoul zai dawo Anty jamila ta haihu ansamu baby girl.
Fiyah ta shirya kayanta itace yar zaman bakwai,har rigima sukai da yesmin akan ita zata fiyah tace"keda kin cika lalacin tsiya me zaki tsinana mata dallah matsa mun."
Mama tace"Ato nidai ai bazan tura ku kudu ka ba kamar wata wadda bata da hankali,kume ke safiyyah ai ga makaranta da hkr kikai tunda ita ta gama zaman banza take."
Silalewa kasa tayi tana dirje dirjen kafafu don yau rigimar takeji bilhaki da gaskiya "wallahi mama dama nasan saikin kware mun baya,kullin saikin nuna ni baki goyon bayana tsakani da Allah nida nake babba ai ni zakice intai."
Yesmin tace"kiyi hkr Adda wlh ni daman janki nake don inji me zakice."
Ta fada tana dariya mama na taya ta kallonsu take tama kasa cewa komi mama tace"kinji kunya wlh safiyyah kullum ke bakida wani girma saina jiki."
Ranar da daddare bayan sallar magruba ta shirya kayanta zata wuce,baba yace yaya jalal ya raka ta ta samu abun hawa."don kin matsa uwata ai da bari akai saida safe,wlh ni bana son fitar dare."
Yaya jalal din yace "yo baba sai abuna take so don gidansu,ke maza maida wannan akwatin saida safe zakitai,don ubanki kamar wacce ake cizo cikin gidan ko ker mar ubanme take."
B'are baki zatai ta wage da kuka yafaske bakin "kisake inji sautin numfashinki sa niyyar kuka kigani."
Daki na koma nayi kuka na bakuma komi yasa nakeson fitar ba munyi sa malik zaiso bakin titi ya wuce dani baban najiyosa yana cewa"kayi hkr Abdoul jalal barta tai kila itama jamilar tana can jiranta take."
Kwala man kira nai nafito hararata yayi yace"kina iya wucewa muje ai,fitinanar wofi ke ko kunya baki kiji ga yar kanwar ki nan bata addabi kowa ba saike katuwar wofi."
Haka ya tusani har bakin titi sai sababi yake shida Anty jamila insuka fara fada kamar bazasu barka ba,koda ya tari taxi din cewa yake"wlh kika bari naji labarin kin kai saurayi gidan nan zaki gaya masu."
Yabiya mai taxi din mukatai.
Wayata keta haske alamun kira na Ake don silent take kar akirani gabansa inshiga uku.
"Yaya malik yayane ta tarar mun taxi kaganni nan ma mun tafi kabarshi mun hadu gobe ai inada lectures."
"Aa yar qanwata gani nan bayanku fa"
Zaro ido tayi tana lekawa aikuwa shine saurin tsayar da mai taxi din tayi tace"daka ta malam saukeni anan yi tafiyarka."
"Amman hajiya kinajin kashedin yayanki."
Cikin masifa tace"dallah can niba kudin zan ansa ba mak'olo kuma ina ruwanka da shiga sabgar da babu kai."
Hkr yabata sauka tai ta shige motar dariya yake mata yace"haka kike masifa qanwata."
Murmushi tayi tana cewa"yaya malik naga zai kawo mun raini."
"Toya kike kinsan kuwa nayi kewarki."
Jin kalamar nayi kewarkin tayi bala,in sata shock har ta kasa kallonsa kauda kai tayi gefe,yana lura da ita yasake cewa.
"Na saba kullum ina ganinki kwana hudun nan jinsu nake kamar na shekara,koke bakijin yadda nakeji."
Shirun ta sake yi masa dariya yayi kasa kasa yace"tunda baki magana gaya man sunan unguwar."
Daker ta lalubo abun fad'a tace"gwarunfa"
Hira yake mata amman ta kasa cewa komi don yau da wani salo yaxo dashi wanda ya sata shiga shakku.........sakin maganar yayi ya kama wata "kinsan kuwa zakiya aure zatai in the next 4 weeks"
Sai lokacin ta bashi duk kanin hankalinta tace"dagaske!kashhh banji dadi ba amman ya zamuyi yanzu."
Karka ta wa yayi yasa hannu ga Aljihun wandonsa na baya,ya zaro wata pos mai shegen kyau ya mik'o mata.
Ansa tayi tana binsa da kallon karin bayani.
Hankalinsa na kan tuk'i yace"ta yarda ita ne bakin bank,ina gefen hanya nazo shigar da kudi,Allah yasa ni kadai na gani nai saurin dauketa,duba ciki kiga akwai information din duk da mukeso jikin wami card nan,phone number,address da sai sairansu to duk ciki dai ba kamar phone no din itace abu mai muhimmanci,gashinan na bar maki sauran aikin."
Alamar jinjina tayi mashi tama smile dinta mai kyau da gigita wanda ake mawa.
Ajiyar xuciya ya sauke yace"gobe 12:00 na rana zai sauka zakimun rakiya."
Tana rik'e da card din data fiddo tana kallo tace masa"ni kau mezan yo."
Murmushi yayi yace"kece da abunyi kau,zaki je tarbarsa ne harma da guzirin flower."
Dariya tayi tana girgiza kai tace"kaima yaya malik da neman magana kake to miye na wani zuwa da wata flower saika ce wasu lovers."
Rage gudun yayi yana kallonta asace wanda hankalinta yana kan card din dake hannunta,kauda kai yayi ya cigana da tukinsa.
"Ba dole sai masoya ke haka ba,kawai zakiyi masa ne don muga action din dazai bada."
Rausayar dakai tayi tana kallonsa kadan kafin ta kauda kai tace"oky let me see"
Sun iso unguwar lafiya yayi parking bakin get din ya ja kofa taki budewa,juyowa tai ta zuba shi ido kamar yadda ya zuba mata nashi masha Allah..........kasa jura tayi ta janye idonta ta rasa wadannan sale salin da malik yake mata ko namiye......."kin ga"
Daker ta oya sake juyowa don wlh yadda bai tunani bata son hada ido dashi,tana jin kunyar kallon da yake maka mata.
Lumshe ido yayi ya jawo wani d'an gift daga bayan motar an nadesa da irin ledar nan da ake nade gift da ita.
Kasa ansa tayi tana kallonsa tace"na miye yaya malik?"
Ajiyar xuciya yaja yace"just for u,na gani ne yayi mun kyau nace zaifi dacewa da hannunki."
Tunda suka fara muamala yaune ya taba bata abu,don haka bata jin zata bashi kunya cikin sanyi ta mik'a hannu ta ansa.
"Thank u so much yaya malik."
Hannunsa yasa gefen kansa yayi mata salute alamar sara wa.
Murmushi tayi tana masa saida safe.
"Karki manta fa zanzo nan natai dake kizama cikin shiri."
Daga masa kai tayi tana shigewa cikin gidan.
Dora kansa yayi saman sikiyarin motar yana magana can kasa,bazan iya juyo meyake fada ba,yajima wajen sannan yaja motar yabar unguwar.
Chapter 24 · 0% Book details