← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 87

Sashe 16

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wani irin kerma kafafunta ke mata amman iyakar dauriya ta aro ta yafa akan fuskarta,malik kau gefe yaja yana kallonsu yana jin tsoron abunda zaije yazo.
Saida ya kusan shigewa jikinta sannan yaja burki idonsa akanta,wanda ta kasa cigaba da kallonsu saboda tsabar abunda yake fitowa daga cikinsu.
Cikin kakkausar murya wadda kaushinta bai hanata fitar da wani sauti mai dadin amo ba,runtse ido tayi saboda har sautin maganarsa yana sauka akan fuskarta.
"Kee ubanwa ya kawoki nan gidan,bai gaya maki sak'ona ba cewar idan na sake ganin bakar fuskarki saina kasheki.to in bai sanar dake ba yanzu kinji,don haka wlh in na sake hada ido dake ko ahanya ne saina kwalkwale idonki idiot stupid girl oya get out wawuya village girl dake."
Sai lokacin ta d'ago dara daran idonta tubar kalla masha Allah farare tas kamar takarda ta zuba mashi su,idan da yasan yadda xuciyarta ke masifar bugawa da baikai ga gaya mata irin wannan zafafan kalaman ba,amman baka tab'a gane hakan akan fuskarta wani dak'ik'in kallo take watsa mashi,tana juya kwayar idonta kamar ba tata ba,kafin taja baya tana dad'e hanci da baki kamar taga kashi ko wata k'azanta.bacin salon nata kenan don dai kawai itama ta rama dizginsa da wulakancinsa,ja baya tayi tace cikin wata siririyar murya mai dadin saurare "dallah malam matsa ya zaka wani matsoni kana wannan smelling d'in,ka kuwa ji yadda kake tashi da alamar hancinka baya jin kamshi balle wari,aida kai kanka ka kyamaci kanka.har kake kirana stupid akwai wani stupid bayan ka,dubeka don Allah a haka kamar duka kenan,yo taya ma mutane zasu rab'eka kana warin giya mts!!! Move me kana wani tsaye bisa kaina."
Dalalo idanu yayi kamar yaga sabuwar halitta,yana jin kalamanta kamar sukar mashi cikin kirjinsa juya wa tayi tana sauri don ta fice kafin ya kai ga saka mata kafa ya tad'oyeta,banda bugawa babu abunda kirjinta yake,har wani fitsari takejin yana taho mata bata wani buri daya wuce ta ganta tabar unguwar.........saidai kashhh tunaninta bai ci ba jitai anyomata wata irin fizga kamar zaitai da hannun nata.
Afirgice ta ganta zube k'asa gabanshi fuskar nan ta sake rinewa cike da zafin xuciya ya daga k'afarsa zai taka mata hannu,cikin zafin nama malik ya karaso yajanye ta cike da b'acin rai yace mashi.
"Mekake shirin yi Alfah,ina ruwanka da ita gunka tazo kokuwa ta kula da lamarinka banson cin zalin kaga kawuce kabarta tunda dai kaine ka fara tada wannan fitinar."
Wata ingiza ya yiwa malik yace"karka gaya man nonsense malik,meye hadinka da ita miye alakarta da nan gidan,wallahi inka bari ta sake takowa nan yafada yana doka kafarsa da k'asa cike da mazan taka yacigaba da cewa to billahil azim za,a kwashi gawarta."
Malik xai magana ta rigashi cike da tsiwa da rashin kunyar data aro babu jimawa tace"ni kuma saina zo,nan gidan dai ko to kadauka kamar gidan ubana yake haka xan mayar dashi,kwana ne kurun bazan ba kama hangoni gani can har dakin baccin ka,angaya maka kowa sakaraine da zaka ringa yiwa mutane hauka,yo waye bai iya haukan ba dallah can da kai mtsss!!cike da bala i yace"ke don ubanki ni kike gayaa magana tun kararta yake yana zaro ido tatare siket dinta tayi zata baza aguje don idan ya kamata ta bani ta lalace.......kotaki guda batai ba ya cabko hannunta ya dage cicin karfinsa ya watsata gefe tayi wata kalar fad'uwa har tana gurje guiwa..........ta fashe da kuka bakinta bai mutu ba tace"Allah ya isa na mugu Azzalumi macuci.......faske mata baki yayi yana huci "don kutumar ubanki tashi kifita shigiya mayya."
"Kaine maye azzalumi macuci kuma sai Allah ya sakaan mugu mashayin giya.......tana fadar haka ta rarumi jikarta ra ranta cikin na kare......shima ya rufa mata baya aguje malik shima yabisu yana son yin dariya amman halin yinta bai zoba sai yaga yar mutane ta bar unguwar sannan.
Cikin sa,a tama fita taga taxi ta tareta tashiga cikin azama.
Tace"maza muje karka tsaya muje muje maitama estate zamu."
Shashsheka kurin take ta leko ta danna mashi dak'uwa tana mashi gwalo.
Zubewa malik yayi bakin k'ofar yana kwasar dariya harda rik'e ciki,don wannan wasan yayi masifar burgesa,koba komi fiyah zata ringa saka Alfah magana ta wannan hanyar zafin ransa zairagu tun yama biyeta wataran dole zai dawo hankalinsa idan yaga tana niyyar mayar dashi cikekken mahaukaci.
Huci kurin Alfa keyi yana jin bakin cikin rashin kamata da baiba kallon wulakanci yayi wa malik cike da haushi yace"kana sane kayi haka ko,don ka b'ata man rai to kayo nasara amman kasani bataci lallai ba zanso ta sake zuwa zakaga abunda zai faru,saina cire mata kafar baya alokacin zata gane ko waye ni don ubanta."
Ya wuce malik yana dariya gaskiya fiyah ta mamesa baizaton haduwar farko zatayi irin wannan karfi halin ba.

Tana isowa gida taji kafarta ta rik'e sai yanzu faduwar da tayi takejin ciwonta,daker ta fito daga taxi ta salamesa ta nufi gidan cikin karfin hali.........mama tafara cin karo da ita zaune tsakar gida tabuga tagumi,ga yesmin gefe tana ta kuka......dandanan taji ciwon ya b'ace ta isa garesu cikin tsananin damuwa bakinta har kerma yake tace"mamana lafiya meya faru,naganku cikin wannan yanayin....yesmin daina kuka gani sanar dani don Allah meya faru."
Mama kasa tankata tayi tana share hawayenta yesmince ta iya kallonta tace cikin kuka"Adda sofiyyah babane........sai kuma ta fashe da kuka ai fiyah najin ance baba ne cikinta yayi wata irin katsawa cikin rikicewa tace"sanar dani kanwata daure ki sanar dani meya samu baban yana ina babu dai abunda ya samai ko kigaya man don Allah."
Tuni itama idonta ya fara zubar da kwallah ta tashin hankali komawa tayi wajen mama dake sharen hawaye tace"haba mama kunbarni cikin duhu don Allah kusanar dani ahalin da yake ciki,don Allah xuciyata bugawa take."
Mamarce ta iya cewa cike da raunin xuciya "safiyyah babanku ne aka kama yana police station,tun bayan fitarsa ashe yaa can suka kamashi,kuma sunk'i fadar ainahin abunda yayi kuma sun hana belinsa,tun shabiyu jalal yake can shida dalha amman babu magana ingantatta da sukafada,hardai korarsu sukai cewa kozasu kwana anan bazasu canza umurnin da aka basu ba."
Zaman dirshan fiyah tayi tana zubar da kwallah cikin kid'ima ta riko hannun mama tace"innalillahi wa inna ilaihir raju,un mama waye yasa aka yiwa baba haka,meyayi mashi wlh mama inada yak'inin baba bazai abunda ba shine ba waye shi wane macucinne azzalumi."
Cikin jan majina tace"Alh muazzam ne bansan abunda ya hadashi dashi ba,amman daman ai yana cike dashi yanada wani kudiri aransa tsawon shekaru,kullum hanya yake nema dazai wulakanta shi allah bai bashi ba sai yau tsotsai nasan komi ma yafaru wlh babanku bada niyya zai ba,saidai tsotsai da rabon wahala."
Hawaye take sharewa cike da jinjina magamar mama,Alh muazzam yasa aka kama baba,kenan banu wanda ya isa yasaka asakesa idan har ba shine yaga dama.........yanzu ya zasuyi wagaresu waye zai tsaya masu dazai ceto masu mahaifi.
Cikin hawaye tace"yanzu kenan mama babu wanda zai taimakemu waye zaitsaya mana mama bamuda kowa daya wuce yah jalal,shikuma ba wani abin hannune dashiba sai rufin asirin Allah......mama haka zamu zuba ido baba yayita zama can."
Itama cikin halin k'unci tace"Allah shine gatanmu sofiyyah,shine zai taimakemu shizamu kaiwa kukanmu kutashi kuyi Alwallah ga magruba can anfara kira mukaiwa Allah kukanmu don Alh muazzam baida wani mak'iyi cikin unguwar nan daya wuce mahaifinku,bai shiga gonarsa ba ma ya ya iya dashi balle yashiga,muje musanar da Allah kukanmu shine zai share mana hawaye.
Daidai sallamar yah jalal kenan shida dalha maitsaron shago.

*kuyihkr yauda kullum ce sai Allah*

Mrs bb ce
Mom muhseen.

I really proud of u fans Allah ya kara mana kaunar juna.
[9/17, 3:37 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........16
Chapter 16 · 0% Book details