← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 87

Sashe 56

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gaba ki daya hankalinsu ya tashi ganin yadda fiyah duk ta bi ta haukace,tana fixge fixge tana kiran mama.yesmin kuka take sosai don inkaganta zaka dauka sabuwar mahaukaciya ce.
Ganin tana niyyar fixge canuler hannunta yasaka yahadeta dukanta yayi mata wani kyakykyawan ruko cikin jikinsa,yana hura mata iska cikin kunnenta idan kagansu zaka yi mamakin yadda suka hade waje guda,numfashi takeja tana kuka kasa kasa yana shafa kanta tare da yimata alamar lallashi kamar yana lalashin yaro.
Zakiya wani kudulelen abune ya tokare mata wuya,duk yadda take kowa da xuciyarta da kwayar idonta akan kar tayi kuka abun ya ci tura,juya baya tai tana shere kwallarta.
Malik yana lura da ita bai ce mata komi ba,yesmin dai sai sharar kwallarta take.
"Malik ka kira dr pls"
Jinjina kai yayi yana fita daga dakin,zakiyya ma ficewar tai yabita da kallo kasan ransa tausayinta yake,amman bazai iya yin halin ko inkula da safiyya ba bacin tana bukatar taimakonsa.
Ajiyar xuciya yaji tanayi kuma rikon da tayi mashi tana sassautashi,jikinta yana saki ahankali.
dago fuskarta yayi ahankali ta bude idonta ta zuba mashi su lumshe mata nashi yayi yana karkta kai tare da dage girarsa guda,yakai bkinsa kan kunnenta cikin sanyin murya yace"cute baby relax mana,bude idonki ahankali zaki gane inda kike,qanwarki yesmin ma kinganta anan,karki sake rikice man plsss nima zan iya birkicewar oy open ur eyes and relax"
Kalamansa kamar saukar kankara fakejin su cikin xuciyarta,waye yake mata wannan kalaman da takejin suna saukar mata da wata natsuwa ta musanman,jikinta yana sakewa kwalwarta tana dawowa daidai tare da tariyo abubuwan dasuka faru,ahankali yake zare jikinsa daga nata wanda yakejin wata irin kasala tana mamayesa,har yana jin tsikar jikinsa tana tashi.
Komawa tai jikin bango ta tattare kafafunta ta rungume tana kallon dakin har idonta ya sauka akan yesmin,wata nannanuyar ajiyar xuciya ta sauke ahankali bakinta yana rawa tace"yesmin"
Rugowa tayi wajen Addar tata ta rugumeta tana kuka"Adda kin warke ko,kice mun baxaki sake irin abunda kikai ba,kin tayar mun da hankali........dr ne da malik suna shigo ahankali take kallon malik tana kallon Dr ta juya ga Abdoul dake gefe yana dafe da kansa idonsa arufe.
"Sannu qanwata kin tashi ko Allah ya sawake"
Daga kai tayi tana kallon yesmin.
Dr ne ya dubata yace"jiki alhamdulillah xuwa anjima ma idan ruwan can ya kare, ana iya bata sallama,anyi ta barka wlh wasu har rasa hankalinsu suke ta silar wannan allurar,Allah ya kiyaye gaba"
Abdoul ne yace "dr tana gama karya wa zaka sallameta zaman me kuma zata zauna tayi bayan komi success"
"To yallabai yadda kace din amman inso samune anfison ruwan yakare tukun"

"Anjima zan sake dawowa idan ruwan yakare saina bata sallamar",
Ajiyar xuciya yaja yana dora idonsa akanta,akai sa,a itama shi din take kallo.
Tama rasa wane tunani zatai,sadda kai tayi malik ne ya fita yashigo da zakiyya daka kalli idonta kasan tasha kuka ba kadan,tunda ya mata kallo daya ya kauda kai bai sake kallonta ba,don zata raunana mashi xuciya,bacin bacin ran data sakashi.

Toilet yashiga yayi brush ya fito ya zuba breakfast dinsa ga plet yaja gefe yana ci kamar babu kowa dakin,malik yace zakiyya ki zuba ma fiyah ta karya amman kidan kamata ta wanke bakinta."
Yesmin tace "bari na taimaka mata ita ta xuba abincin kafin ta fito,daker take tafiya don gabaki daya jiri takeji,ahaka fa wanke fuskarta da bakinta tayo Alwallah suka fito,capet din dake malale tsakiyar dakin ta zauna sama tana jingina bayanta da bango,idonta nason kallon Alfah Amman tanajin nauyi,tana bukatar nazari don kusan duk abunda ya faru kamar tana sani kamar tanajin wasu abubuwan,amman girman Allurar yahana ta gane meke faruwa amman idan bazata manta ba,wasu kalamai suna mata amsa kuwaa ciki kunnenta da kanta,zakiyya jiki asanyaye ta ajiye komi gaban fiyah bakinta kamar anmata dole tace"yajikin naki"
Ko kusa bata dago ta kalleta ba,saidai ta ansa mata cikin voice dinta data dishe bata fita sosai.
"I'm feeling better"
Daga haka bata sake ce wa komi ba,yesmin ke tayata tana cin abicin,kamar bata so.
"Zan wuce office Alfah tunda jikin yayi sauki,ko akwai abunda za,ai"
Bakinsa yake gogewa da tishu yace"jirani mutai,ka saukeni gida nayi wanka,duk rintsi yau zanje station dinan"
Mikewa yayi yana saka wayarsa gaban aljihu yace"zanje na dawo idan ma bandawo ba driver zai zo ya maidaku gida Allah ya sawake"
Kanta akasa tace"nagode amman kabarshi zamu shiga taxi,ga yesmin nan ai"
"Okay"
Yawuce kurin,zakiyya tashi tai itama tana cewa"Allah ya sawake"
Uffan fiyah batace ba saidai yesmin ta ansa mata,daga ita sai yesmin adakin sunyi shiru kowa da tunaninsa.
"Adda su waye wadannan"
Bata bata ansa ba tana tsakurar dankalin kamar bata so.
Tace"nima ban sansu ba,karki isan da tambaya"
Nurse ce tazo ta mayar da drip din daya rage ba,a idasa saka mata ba,fiyah tace ma yesmin ta zauna tayi break tasan bata yo ba.
Ahankali suke firarsu har rafeea tazo suka cigaba da firar,tana cewa ta auna arxiki sunada interval kwana uku aida abun baiyi ba, feea tace ai tabaro mama na shirin tahowa ita dasu Anty jamila harda kanen mijinta.
Wata faduwar gabace ga samu fiyah badai muhseen bane zai zo,innalillahi Allah yasa to Abdoul karya dawo.

Malik ya sauke alfah ya wuce wajen aikin shikuma yashiga yayi wanka ya dauki kamshi,yayi masifar yin kyau kananan kayansa yasaka t-shet dark blue sai black trouser,combus dinsa blue and white color,yau babu fesin cap dinsa.zakiyya dake falon zaune tana kallo wanda gabaki daya hankalinta ba kan tv yake ba,ta luka duniyar tunani,taji kamshinsa ya mamaye falon
Tsaye yake yana daura agogo ga waya kare ga kunnensa ya makale ta da kafadarsa yana magana,shagala tai dakallon sa wani mahaukacin sonsa yana sake cika ruhinta,dandanan kwallarta ta cika idonta yanzu ace duk yadda wannan guy din yake zai iya zama haramiyarta,wace irin kaddarace wannan data raba tsakaninta da masoyinta,ada Alfah bashida wani buri daya wuce kasancewa da zakiyyarsa,yasota wanda shi kanshi baisan adadi ba.
Ita kanta alokacin har mamakin kaunar da suke ma juna take,ashe akwai lokacin dazai zo saidai ta ringa tunawa.
Ganin zaifita yasa ta dawo natsuwarta tai saurin ringanshi isa wajen kofa tana tare hanyar,idonta da kwalla tace"Bazan bari kafita gidan nan ba yaya Abdoul sai kagaya mun matsayina,na gaji da hakin da kake nuna man acikin gidan nan.gabaki daya ka daina sona kadaina damuwa dani,ka dauki gurbina ka maye da wata watacan da batasan darajark............"inkika sake furta makamanciyar irin wannan kalmar akanta zan baki mamaki,matsa bani waje kafin tafin hannuna yasauka afuskarki,kije kiyo karatun tanatsu inkina son magana dani,stupid girl"
Yasa hannu yajanye ta ya wuce yana jin haushinta har cikin ransa,
Station din yaje ya samu dpo din wajen sukai magana,yake gaya mashi .
"Ai yallabai wadannan yaran kangararrune,tunda aka kawosu ake gana masu azaba akan su fadi wanda ya sasu wannan aikin amman wancen shegen yana hanasu,wai muddin suka fada sai yayi ajalinsu."
Iska Alfah yaja yana fesarwa ya kalli inda aka kulle su idonsa akan mamman,wanda ya canza kammani daga kamanninsa nada.
Yadai samu darajar anmashi aikin kafarsa ancire bulet din,anyi dressing.
Shafa kanshi yayi yana kallon dpo din yace"to waye yace kace saisun fadi wanda ya sasu,ai bama bukatar wanda ya sasu.tunda abun afili yake kucigaba da cin ubansu har sufita hankalinsu,har sanda zan sake dawowa."
"Yallabai sau uku ana zuwa neman belin su muna hana wa,saboda girman laifinsu,aman idan aka sake dawowa zamu iya sakinsu gaskiya,duba da cewar mai zuwa belin babban mutunne"
Kallon dpo din Alfah keyi ransa yana sake baci xuciyarsa ta fara hawa jiyake kamar ya shakesa yaringa naushin dan isaka.
Cikin bala i da rabon dayayisa yajima yace"to kubada din,billahil azim saika rasa wannan yar jskar kujerar,koma ubanwa ye yazo kace ni nace ban lamunta ba,inbanda rashin hankali irin naku har ku bada belin yan iska irin wadannan bacin kuna da tabbacin sudin hadarine,to wlh ka maida hankali na dawo gobe babu su."
Juya wa yayi har yakai kofa dpo din yace"yallabai mahaifinka ne fa"
Cak ya tsaya bai jiyoba yana jin wani emotion yana zagaya wa dashi,wani rauni yana kama zuciyarsa har hakan ya shafi muryarsa yace"koma waye ban lamunta ba,inya sake xuwa just call me zanzo da kaina"
"Okay yallabai"
Ficewa yayi yana jin kamar ya fashe da kuka me hakan yake nufi,da saka hannunsa aka sace fiyah,kokuma yazo ne yayi belinsu don yana dan uwan matarsa,to koma ubanwaye din matarsa wallahi wannan karon saidai ayi uwar da za,ai bazai daga kafa ba.inma ace shine suka farauta zai hkr aman badai rayuwarsa ba safiyya kenan.
Asibitin yayiwa tsinke don yasan drip din ya kare yana son sake ganin yadda jikin nata yake.
Chapter 56 · 0% Book details