← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 87

Sashe 4

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun asuba da ta yi salla bata koma ba,kasancewar itakeyin duk ayyukan safe kafin tatafi makaranta,sharar tsakar gida ta farayi sannan ta gyara wajen dabbobi,ta samasu abinci da kajin suma.sannan ta wanke bayinsu ta fiddo wanke-wanke ta share kitchen din,sanwar kalaci ta dora sannan ta fara wanke-wanken,sai lokacin yesmin ta fito daga cikin d'aki tana hamma.
Kallonta tayi tana murmushi tace"kasa uwar bacci sai yanxu aka samu damar tashi,to azo ayimun d'auraya."
Dariya tayi tana kallon gidan tace"sannu Adda nah,kina kokari fah ni ban sanma baccin ya sace ni ba bayan sallar asuba."
Tana d'auraye plet cikin ruwa tace"hada gajiya ke damunki bakya samun hutu sosai,don ma kun samu interval aida abun ya maki yawa."
Zama tayi tana yi mata d'aurayar suna hira.

Tsakaninsu Babu nisa don ashekaru,duka shekara biyuce ta shiga tsakaninsu,suna matukar son junan su duk abunda ya samu guda kamar suduka yasama,mahaifiyarsu tayi tsaye wajen tarbiyyarsu,don suna girmama yayunsu jamila da jalal,watau babban wansu yana aiki ne a kaduna,bai cika zama ba wata secondary school yake koyarwa.
Malam kabir El-ladan shima malamin makaranta ne,amman ya jima dayin retire tun tuni yanzu yana zuwa wani karamin company na hada kujerun amare da gadaje,yana aiki wajen babu laifi yana d'an samun na rufin asirin sa,don kullum ake biyanshi.
Ita kuma maman su kiwo take na dabbobi da kaji,tana daukar d'aid'ai tana siyarwa idan bukatar hakan tatashi,kuma ta kafa shagon sayar da kayan masarufi ak'ofar gidan,babu laifi suna ciniki don duk unguwar babu shago sai nasu,don dole masu kudin unguwar suke siyayya wajen,don inkana son abu dole saika je bakin titi.,ganin wiyar fitar yasa suka hkr suna siye awajensu,don bayarda suka iya,don basu son duk abunda zai hadasu da wannan kaskantaccen talakan,cewarsu kenan.

Kafin mamansu ta fito har fiyah ta dama koko,ta dora juluf din taliyar hausa da zasu had'a da ita.......kafin karfe takwas har tagama komi tayi wanka ta shirya,sai albarka maman take saka masu baban daman tun shidda yake fita,sai goma yadawo ya karya sanan ya koma sai kuma dare don can yake cin narana.
Yesmin ta fiddo wankinsu nata dana Addar ta dana maman,tana yi don yau bazata ko ina ba kasancewar weac da suke amman sun samu hutun kwana biyu.
Fiyah ce ta fito sanye da doguwar rigar atamfa purple and pink sai lemon green,tayi masifar daukarta duk da babu kwalliya fuskar sosai,hakan bai hana tsananin kyanta bayyana ba,purple din hijab tasa iyakar guiwa mai hannu,sai jikarta itama purple din da takalmata,fiyah badai daukar wankaba ta iya had'a matching color,bata yarda tayi hadin gambiza,kuma antyn ta jamila ta koyar da ita salon daukar wanka.........ruwa tasha tana tambayar maman su karfe nawa tace mata ,
"Kina da sauran lokaci ki natsu kigama."
Tana goge takalminta tace"mama jiya ban samu morning lecture ba yadda ya kamata,yau bazan so haka ba."
Takalmin ta sa mamar tana mik'o mata dari biyar tace,
"Gashinan Dari uku yabaki naga bazata isheki ba yasa nace yesmin ta anso maki dari biyu wajen dalha kikara."
Rungume maman tayi tana murmushi"nagode mamana Allah ya barmana ke."
Ta sun baceta ta fice tana ma yesmin by by.
Sauri sauri haka ta fita cikin estate din zuwa bakin titi ta tari taxi.

💞💞💞💞💞💞

Tun safe malik ya fita zuwa company don yana aiki da company Alfah,mai suna *FATION&DESIGNER'S BANGLES COMPANY* nasa ne na kansa,suna siyarda sumfarin yan kunne yan hannu,sark'a da links na maza,agoguna new moden design ba karamin kudi suke samu ba,daga kasashe ake zuwa wajensu siyen d'ai d'ai ko sari,babu kasar da Alfah baya zuwa shida malik akan wannan kasuwancin,gefe guda kuma ga shopping mall d'insa duk malik ke kulawa dasu,bakamar yanzu da abubuwa suka rikice komi yake neman tsayawa ya lalace,dole malik ya tashi tsaye don ganin basuyi asara ba kuma basu rasa customers ba,dafarko cewa yayi yabar aikin bazai sake zuwa ba,saida malik yatusasa gaba yana kuka da ban baki sannan ya amunce yake yin aikin kan computer,duk abunda zaiyi acan office yana yinsa ga computer,saidai guiding din ma,akaitan da ya saka shakikansa dake cikin company suke mashi CID,kuma yana lura da komi ta computer shima,don kwanakin baya saida yakori wasu ma,aikata dasuka so sujawo masu matsala.
haka zalika malik tsaye yake akan dukiyar abokinsa safe rana dare ,kuma duk wata yana fidda albashin ma,aikatan su aba kowa hakkinsa.
don ma kayan yanzu sunyi ramai ramai,suna bukatar sabbin kaya amman yayi-yayi da Alfah su shirya sutai paris da sauran kasashen dasuke zuwa saro kaya masu inganci,yace bazaije ba inkuma ya matsa mashi wlh saida company zai ya kyautar kudin,mafarin ya kyakesa kenan.

Kwance yake wajen swimming yana shan iska,ga table dinsa nan kwalaben win d'insa wajen uku,ya shanye biyu saura guda itama ya sha rabi.
Ko ka dan giya bata bugar dashi,irin yadda take bugar da wasu sukoma kamar mahaukata,zaiji shi yana layi amman daya kwanta yayi bacci zai wartsake,amman idan akai kuskuren tunkarar sa cikin wannan condition din tofa akwai damuwa,don shikanshi baisan 6annar da zai aikata wa kowaye ba,hakan da malik ya lura yasa idan yana cikin mayensa baya kulasa.fita yake yabar mashi gidan har sai ya tabbatar ya lafah sai yadawo.

Malik ne ya iso wajen yana rik'e da computer akwai wasu bayanai da yake son nuna mashi,na email,don sakonnine na abokan kasuwancinsu suka turo suna bukatar zuwa cikin satinan idan ya anshi gaiyyatar, zasuyi wani ciniki idan yana da lokaci.
Idonsa arufe yake yad'ora d'aya kan d'aya,girgiza kai malik yayi zai juya don yasan bazai bashi hadin kai suyi magana ba inhar yanancikin wannan halin.

Jiyai yace mashi"kafasa abunda kazo yine"
Ajiyar zuciya yasauke yana dawowa ya zauna,laptop d'in ya tura mashi gabanshi yana cewa"bak'i garemu suna neman iznin zuwa don suna son siyen kaya,gashi kayan babu masu kyau sosai duk an zab'e shiyasa nace maka yadace kaban dama ni naje idan kai bazaka ba."

Tura mashi system din yayi yana cewa"katura masu acceptance latter,zuwa opper week sai suzo kafinan har kaje kadawo."
Dadi yaji koba komi yau ya sauraresa duk da yana cikin halin maye,mikewa yayi zaibar wajen wayarsa tayi kara,ya duba yaga ba suna dauka yayi yana sallama.
"Wa'alaiku mussalam,da malik nake magana."
Malik yace"yes i'm malik muazzam."
"OK Dr ne don Allah katuro mun address din inda zan sameka."
Kallon Alfah yayi daya kai cup din win dinsa bakinsa yana sha cikin kwanciyar hankali,amman fa kokadan hakan bai nuna kan fuskarsa ba,malik yace"ok dr bari na turo maka ina gida ban kaiga fita ba."
Text ya tura mai sunan unguwar da kuma stress dinsu da no. Gidan nasu.

Wucewa yayi cikin gidan don cigaba da aikinsa.

********
"Yallabai gashi yaturo,amman don Girman Allah yallabai karka saka adaure wannan bawan Allahn,wallahi nagaya maka baicikin natsuwarsa hakan tafaru,kuma naba Rafeea hkr cewar baiyyi don yana sane bah."
Cikin fushi Alhaji kwangila yace"karka raina man wayau Dr fahad,ya d'aga kantamemen hanunsa k'azamin hanunsa ya wanke y'ata da mari,sannan ya zageta har ya hada dani sannan kace inkyalesa wlh ko waye ubansa yau sai ya gane kurensa,saidai shi yaji tsoron sake aikata haka akan wata badai Rafeea ba."
Shiru Dr yayi yana daya sanin sanar dashi cewar yasan sa.
Waya Alhajin yake cikin fushi cewar"yanzu yanzu nakeson kuje ku kama shi,karku ragar mashi har sai nazo zan biya na dauko feea makaranta zamozo tare,ga address din gidan nan zan turo maka."
Kashe wayar yayi yana kallon dr daya sha jinin jikinsa"kodai dan gidankune sai haka dr jibeka yadda duk kawani lafke,garama katashi katai don wlh bazan ragar masa ba,da dai wani yata6o mani ba Yarlelena ba to da saina sassauta mashi,amman wlh bazan lamunci abunda zai ta6a man feea ba."
Ta shi Dr yayi yana jin babu dadi kuma yasan malik zaiga yayi anfani dashi don ya cutar da Alfah bacin ba haka yaso ba,abun yafi karfinsa Alhji kwangila baida tausayi ko alama.

Malik na cikin gida yaji an danna bell d'insu tashi yayi yasan ko za,a shekara dubu ana danna wa Alfah bazai tashi ba balle ya bude.
Ajiye aikin dayake yayi yasaka rigarsa akan singlet din dake jikin sa.
Wuce Alfah yayi yana exercise dinsa,awajen swimming d'in.
Bude k'ofar yayi yana cewa"Dr u Are welcome.......wad'an da yagani ne yasa gaban sa faduwa sosai,bankesa sukai suka shigo cikin gidan,biyosu yayi yana magana cikin tsananin rudewa"yallabai lafiya,ya zaku shigo mana gida kai tsaye,"
Wani daga cikinsu ya shak'osa yana tambayarsa ina guy din daya mari diyar Alhaji kwangila.
Duk abunda kefaruwa Alfah yana hange,ganin yada suka shak'e malik ne abun ya tunzurashi ya jefar da karfen dayake d'agawa ya doso wajen cikin wani irin fushi da zuciya.
Basu san da tahowar shiba kawai ya finciko dan sandan da yashake malik ya wurgar dashi gefe har yana fad'uwa kasa.
Malik ya sha gaban Alfah yana mazurai duk ya gigice don yasan tabbas aikosu akai su kama Alfah......."Aa Kadaina karka jawo mana wani tashin hankali",ogansu da sukazo tare yace"ku fiddo mana wanda ya mari y'ar Alhaji,kokuma mutai daku kuduka."
Cikin muryarsa dakakka yace"nine nan sai akai yaya."
Kallon mamaki suke mai ogan yace"u are under arrest."
KO akwalar rigarsa ya mik'a masu hannunsa suka sa mashi unka,malik duk ya gigice yace"wlh saidai mutai tare bazaku daukesa ba wlh. kunko san kowaye shi kushiga taitayinku kafin .........cikin tsawa yace mashi " *malik!!! Karka sake wata magana anan"*
Ya kalli ogan yace "muje."
Aguje malik ya fito ya bisu abaya taxi ya tara yarufa masu baya,sai station.

Fiyah da Rafeea school din su guda,amman kowa da couse dinsa sun fito hutun minty talatin Abbanta yakirata yace ta taho da qawarta da abun yafaru jiya zasuje police station.........jikin fiyah yayi wani irin bala,in sanyi tace"yanzu fisabilillah feea kin kyauta,saida kika sanar da Abbanku wlh baki kyauta ba to ni innaje mezance sokike nabada shedar dazata saka akullesa,nidai banji dadi bah wlh."
Rafeea itama duk taji jikinta yayi sanyi tace"wlh fiyah shine ya gane bani na sanar dashiba ,ganin shatin marin yayi ga kuncina yace inban fada mashi abunda yafaru ba saiya b'ata man rai,kuma koda nasar dashi cewa nai yabarshi na yafe mashi basai ya dauki mataki ba amman wlh su yah hashim suka tirashi cewar karma araga ma kowaye."
Jinjina kai fiyah tayi tace amman inkinje ai kina iya sake rokon sa asake shi kin yafe kilan ya hakura."
Tace"to zan jaraba muje yace yana bakin get yana jiranmu."
Chapter 4 · 0% Book details