← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 87

Sashe 73

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shiruce ta biyo baya sai yanzu baban yakejin bai kyauta ba,hakika safiyya yarinyace mai hkr dakawaici da kauda kai,yayi imanin duk abunda ya yanke akan alakarta da Abdoul haka xata karba tayi mashi biyayya,tausayinta ya cika shi har ya kasa cewa komi Abdoul din ya mike yana cewa"baba Allah ya bamu alkairi Allah yasa hakan shine Alkairinmu saida safe"
Yafice yana ganin bibbiyu don har wata juwa take daukarsa,metake nufi kenan ta bada damar da za,a nisanta shi da ita safiyya daman bata son sa bai sani ba,meyasa zata karya mashi xucya har haka daker ya iya gano get din gidansu yana shiga kau kamar jira ya yanke jiki ya fadi.........akan idon zakiyya ta fito daga sashen su khadija ta kaimasu abinci.....aguje ra karasa tana fasa kara tana jijjigashi dan da nan aka taru kanshi,sojojin dake waje suka daukai suka sashi mota,shigowar malik kenan yaga wannan tashin hankalin,kwana yayi yarufa masu baya don yasan asibiti za,aje dashi duk inda hankalinsa yak yayi masifar tashi don har yamance rabon dayaga Alfah cikin wanan hali,tabas abunda Abbi ya gaya mashi dazun akan maganar safiyyah da Alfah shine zai cosing wannan matsalar,kodai yaje gidan baban ya korai kokuma ya gaya mashi kai tsaye bazai bashi yarsa ba.
Mami da ni,ima kuka suka kamayi gashi Abi baikai ga dawowa daga wajen aiki ba,babu shiri mami ta kirasa ta gaya mashi ai yafi kowa rudewa da tashin hankali..............

Mama kanta tasha takaicin baba shiyasa ko saida safe batai mashi ba ta shige dakin ta kwanta,wane irin halin rikaune da babansu yana gani yaran nan suna son junan su amman saboda wani ra,ayi can nashi na daban zai cutar dasu da haushinsa ta kwana shikanshi yaga canji amman bai iyace mata komi ba.
Fiyah saboda kuka cikin dare zazzabi ya rufeta har hakoranta suna haduwa saboda kerma,hankalin yesmin ya tashi taita shafa mata ruwa saboda yadda jikin ya kidime baki daya banda kuka babu abunda yesmin keyi,fiyah kau bama ta cikin hayyacinta ganin dare yasa yesmin bata tado mama ba amman asubar fari dataga fiyahr har suma take agigice tafito tana kwalama mama kira cike da tashin hankali.
"Yesmin kanki daya baki iya salati ba kike ihu da kururuwa menene"
Tana shashsheka tana nuna dakinsu daker maganar take fitowa "Adda.......Adda ce gata can......su.....suma take tun cikin dare bata lafiya mama karta mutu...."
Tare suka karasa cikin dakin duk sun rude mama had jikinta rawa yake tana jijjiga fiyah amman bata numfashi..........rungumta tai tana kuka lokacin baba yaje masallaci dan danan mamar ta kira anty jamila don basu san wanda zasu nemi taimakonshi ba wajen mota idan ba su ba.
"Jamila kiceda yahya don Allah yayi hanzari yazo yakai safiyyah asibiti gata nan suma take"
Ai xunbur tai daga kan gado tana fitowa har bakin get tana jiran shigowarsa daga masallaci ta gaya mashi kayan baccine jikinta ta saka abaya suka taho agigice,tabar little fiyah ga mairenonta.

Sorry for d let update
[10/13, 12:32 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSEER*
*(ALFAH)*

WRITTEN BY

MRS BB
MOM MUHSEEN

FOR SALE 300 NAIRA ONLY 09034722970

🅿️............60

Ansamu nasarar daidaiton numfashinta amman bugu xuciyarta bai dawo daidai ba,saboda jininta daya dan hau shiyasa amman sunyi iyakar bakin kokarinsu akanta sunyiwa uncle yahya bayanin cewa zata tatashi insha Allah,damuwace zata haifar mata da masassarar kuma dama akwai maleria jikinta.amman yanzu da bukatar ta huta tasamu rest of mind da alama tana da matsala da bacci amman data farka tasha magunguna kuma ga ruwa yana shigarta komi normal insha Allah"
Godiya uncle yayi mashi yana komawa wajen baba da mama dasukai xugum xugum kamar masu zaman gaisuwa.
"Yaya dai yahya me likitan yace?Allah yasa ba wani mugun abubane ya faru da ita?"mamace cikin damuwa harda yan kwallarta take mashi magana.
"Ki kwantar da hankalinki mama safiyya zata tashi cikin koshin lafiya,ba wata matsala yamun bayani gamsasshe maleria ce da damuwa don har BP dinta yadan hau kadan amman yace data sha magani insha Allah normal,yamata allurar bacci data maleria karku damu abarta ta huta din kamar yadda yace"
Jinjina kai tayi tana zama kusada Anty jamila da tayi tagumi,inhar akan wannan mutumen fiyah take wannan ciwon gara abata shi hankalin kowa ya kwanta,yarinya da yan shekaru harta samu hawa jini.
Mama Ko kallon baba batai ba don har lokacin kule take da shi,ko magana ma batai mashi ba.
Baban da uncle suka ware gefe suna magana akan matsalar data faru uncle yana bada shawara da fadar yadda yadace.................haka aka bar mama wajenta yesmin zataje ta shigar mata exam don yau suke ta karshe tana adduar Allah yasa ta iya ansa mata question din daidai,don bata san me za,a tambaya ba.duk yadda baban yaso magana da mama kiyawa tai saidai ta kauda kai kurin dole suka wuce gida suka kyaleta.dalha ne zai kawo mata kalacinta,Anty jamila tace zataje tayo wanka sai tadawo tataya mamar zama.

*************
Duk inda hankulan iyalan Alh muazzam yake yakai kololuwar tashi,don kuwa ga Abdoul nan kwance gamar gawa baya numfashi,likitoci ukune kanshi suna bakin kokarinsu amman Abbi gani yake basu yin komi zarya yake bakin kofar dakin yana leke ta glass din kofar,daga can kuma mami ce dasu ni,ima zakiyya da malik kuka kurin suke,malik ne keta kokarin nuna dauriya.........dadyne ya iso shima cikin damuwa yake tambayar abi abunda yake faruwa kasa mashi bayani yayi yana kwalla,malik ne tace "dady duk ta kare yaje gidan su safiyya ne babanta ya korai kokuma kai tsaye yayi mashi iyaka da ita,abunda zai ita jefashi cikin wannan halin kenan don Abdoul yana ma safiyya soyayya mai zafi,rasata kamar yana barazanar shina rasa tashi rayuwar don gaskita cikin kwanakin nan inaganin canji sosai tare dashi,alamun sunriga sun daidaita da ita yarinyar gaskiya abunda nake zaton zai jefa shi cikin wannan yanayin kena"
Xunbur Abbi yatashi zaifice dady yarikoshi "ina zaka?badai koma wa zakai ba duk irin abunda ya gaya mana rannan"
Kamar abbi zai kuka yace"Abdullahi ina son rayuwar dana shekara nawa bana tare dashi,sai lokacin da komi ya wuce kuma wata matsalar xata shigo,zanje karo na uku na sake rokonsa kome yake son nai mashi inhar zaibarsu su auri juna wlh zan mashi,koda cewa yayi inkwanta ya bita kaina"
Ficewa yayi dadyn ya bi bayansa don yana iya cewa acikin wannan halin zaija mota.

**************
*****************

Fiyah cikin kwana uku tatashi ta samu sauki,ta dauki hkr ta sama xuciyarta amman fa ta rage walwala sosai da sosai don saita yini cikin daki bata fito ba idan ba wani abun xatai ba,zaka samu kowa tsakar gida amman ita tana daki babu yadda mama batai ba,babu irin lallashin da batai ba amman fiyah ta kasa dawowa daidai,abunda ya taba yesmin da mamar kenan shi kanshi baban yanajin babu dadi,shiyasa yaketa kokarin jawota jikinsa ko zata sake saidai murmushi kurin duk maganar da zakai mata idan har ba yazame mata dole ba bazakaji muryarta ba.tun Anty jamila na fushi da ita harta sauko tana jan yar uwartata jiki,jalal kau ko kallon inda yake batai ko ya mata magana uffan bata ce mashi.ana cikin haka aka saka ranar yesmin da muhseen alokacinne baba ya kira fiyah dakinsa da safe bayan angama karyawa.
"Uwata kinsan dai nine mahaifinki ko,kuma kinsan irin son danake maki bazan yi abunda zai cutar dake ba,duk abunda zanyi inayine don martabarki da kimarki yanzu ma wata alfarma nakeso daga gareki"
Dagowa tai tana kallonsa da fararen idanunta fuskarta ta saki daka kalleta kasan tana cikin damuwa don har wata irin rama tai.
"Baba ni banace kayimun ba daidai bane,kawai inakokarin ganin na manta da komi zan dawo daidai kuma komi kake son yankewa akaina baba basai ka nemi alfarmata ba kana da ikon yanke hukuncin duk da ka ga dama akan rayuwata"
Wani tausayinta yaji ya dirar mashi har kwalla ta cika idonsa "shikenan uwata Allah yayi maki albarka Allah ya albarkaci rayuwarki,wanine keson aurenki harna bashi dama ya turo iyayensa don harna yanke hukuncin saka rana guda keda yar uwarki,nan da wata uku idan Allah ya kaimu"
Wani irin bugawa kirjinta yayi dan danan kanta ya sara damn ciwo yake,daker take jawi numfashinta ta dake sosai tace"Allah ya sa haa shine mafi alkairi baba"
Tatashi tafice tabarsa yana binta da kallo,mamace ta shigo cikin tashin hankali take kallon baban "mekake shirin yi babansu?waikai bakajin digon tausayin yarinyarnan shin wace irin xuciya ce dakai babansu,inajin yaron nan har yau yana asibiti karshe dole aka fitar dashi kasar waje,duk da haka bazaka tausaya masu ba.har gida iyayensa suka zo suna magiya da roko amman vanji kace masu komi ba,gaskiya idan ka aurar da safiyya ga wani ba wannan yaron ba ka cutar dasu,kadaina ganin bata maka gardama Allah kadai yasan kuncin da kasasu baka tunanin Allah ya tambayeka.................ya i sheki nace ya isheki hakanan,ke zaki gaya mun abunda zanyi inace nima yatace,gaya maki kai ba nasonta?kinfini sanin daidai da ba daidai ba?to kinga daman kyaleki nake akan wannan abun,tunda akafara maganar nan kiketa mun wasu halaye marasa dadi safiyya dai yata ce kuma nine nakeda alhakin zaba mata miji wanda yake daidai da rayuwarta,don haka wannan yazama na karshe inajin kinji me nace"
Ya saka hularsa ya fice yabar gidan.
Tunda mma tazo gidan nan matsayin matarsa magana kwatan kwacin irin wannan mai zafi da daga murya baitaba mata ba,duk sabaninsu zasuyi abu su surufe sushirya babu wanda ya sani,kuma kullum suna cikin fahimtar juna daba juna uxiri,amman saigashi yazu da girmansu suke irin abunda baidace ba,har yaransu sunaji.
Kukan da mama ta manta batai ba shine take yi,suma can fiyah da yesmin kukan suke,don basu tabajin irin haka da iyayen nasu ba.
Fiyah naji nagani aka shiga shirye shiryen bikinsu itada yesmin,tun tana kuka tana damuwa tana kuncin,har ta shanye tazo ta zama kamar abun baya damunta,gidan koda yaushe da mutane yanuwan mama dana baba ana hidimar hada gara su cincin da dublan da alkaki da sauransu,shiyasa ma bata zama gidan tana gidan inna balaraba wajen hasana,ko tatai wajen feea.

Wannan kenan......
Chapter 73 · 0% Book details