← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 87

Sashe 36

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallonsa yayi na yan seconds ya dauke kai ya cigaba da tsane gashin kanshi dana fuskarshi,gaban mirrow din dakin nasa yayi burki yana dauko hand drayer ya jona yana busar da gashinsa,kamar ba mutun adakin bai niyyar cewa komi ba saida ya gama,malik ya zuba mashi ido yana kallonsa kafin murmushi ya kubce mashi.
"Yau kuma azumin magana aka tashi dashi?"
Mai yake shafawa ya kallai sannan yace cikin lallausar muryar shi "saidai idan azumin dole kake niyar tirsasani,tunda ko ruwa baka ban ba da safen nan,sai yanxu kake shigomun kana mun wani zance dabam."
Ajiyar xuciya malik yaja yana zama saman gadonsa yace"sorry sir,me kake bukata to"
Uffan ba ce mashi ba yaciga ba da abunda yake,kamar maijin tsoron fatar tashi haka yake shafa man.
Fita malik yayi yaje yadauko mashi break din daya ajiye masa a falo tun goma na safe.
Table yaja ya ajiye masa yana mashi nuni da break din.
"Gashinan ranka yadade"
Dan murmushi yayi kadan yace "tare dakai"
Kaya ya fiddo suit farar shet da farar coat sai black trozer wanke su yayi da turare sannan ya hau sakawa,yana satar kalon malik zuwa can yace masa.
"Karkaga wanan yarinyar bata zoba ta riga tace ba zata sake dawowa ba"
Cike da madaukakin mamaki malik yace"wani abun ka sake mata ahanya ko?"
Kafadarsa yadaga yace"daman nayi zaton haka zakace,toni ban mata uwar komi ba sarkin zargi"
Murmushi malik yayi yace"saika shirya anjima muje ban hkr"
Zaro kyawawan idanunsa yayi yana kallon malik yace"bcos?"
Murmushi malik yayi yace"bcos of u,u Abdul kaine kaja har tayi wannan furucin,safiyyah yarinyace mai hakuri da kauda kai,yadda kake tunaninta ba haka take ba,she is innocent girl kaine ka kure hkr rinta shiyasa tunjiyan zuwa yau banga kiranta ba,nasan arina don haka kashirya anjima tonight zamuje dakai har gidan antynta."
Dariya yaji Alfah nayi yana shan black tea har dariyar taso tea din ya zubar mashi ga kaya,ajiyewa yayi yana kallonsa kafin ya girgiza kai yace"u mean zan raka ka zance kome kake nufi,ina ruwana da zuwa bata hkr ainine ma zata dawo ba hkr saboda nitayiwa rashin kunya,imagine ta kallan tana furta mun Allah ya isa and nida Allah for what reason,inba sokake kasaka na zane ta cikin gidansu ba ajiye wannan maganar,suwaye bakin dake jirana office"
"Shikenan na ajiye maganar amman bada na barta ba,i don't know KO suwaye sai idan munje inson ma inje nagaida daddy kozaka"
Hararasa yayi yana cigaba da break dinsa.

Tare suka fita amman kowa cikin motarsa,malik ya wuce store don duba halin da yake ciki sanan suyi lisafi afidda albashin ma aikata na wannan watan.
Alfah kuma ya wuce company don haduwa da bakin nasa.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Suna yayi kyau mutane da dama su xo cikinsu kau harda momin feea takanas tataso daga katsina tazo sunan,don suna yi sosai da mama cikin estate din duka mutum biyu sukaje ma mama suna gidan Jamila.
Fiyah kau anacan ana hidima da baki bakinta har kunne tayi takwara,suna tare da hasana sa,ata ce baifi one year dake tsakaninta da fiyah ba,umaimaice suke d same years.
Dakinta suka sauka sunata hirar yaushe gamo,sai idan baki sun zo sufita su zuba masu abinci don ma ga inna balaraba da wata abokiyar wasansu da ta iso daga can garin su baba dutsi.inda mamanshi mai sunan fiyah take xaune.
Suna yayi kyau sosai anraba jakunkuna da hoton little safiyya,sunan da takwarar tata ta zaba mata kenan.
Zuwa magaruba kowa ya wuce gida sai su inna dasu hasana daketa faman gyaram gida,duk yinin yau fiyah zuciyarta bata da sukuni jitake matakin data dauka na daina zuwa gidan kamar bazata iya aikatashi ba,daga jiya zuwa yau wani irin yanayi take tsintar xuciyarta aciki,amman tayi iyakar kokarinta wajen dannewa,don ma gwamace wajen boye damuwa.
Wayarta duk yau nata kunna ta ba,balle ma malik ya kirata yayi mata dadin baki,saida gidan yazama need sanan su inna suka tafi,amman anbar hasana don washe gari su kama ayi soye.

💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Malik bayan yadawo daga wajen dady yayi mashi bayanin da zakiyya tayiwa fiyah,yace komi kenan in sungama tattaumawar idan da bukayar yashigo ciki sai yazo ya gaya mashi.
Office ya wuce wajen Abdoul don ya yi alqawarin koyanaso kobaiso sai sunje bikon fiyah,don yakira wayarta yafi sau goma amman anar gudace wayar kashe take.
Gaidashi ake tayi tunda yashiga company har ya samu isa office din Alfah,wanda saika rantse wata duniyace daban saboda yadda yatsaru iyakar tsaruwa.
Aiki yake kan compute ga bako kuma suna magana dashi,ciki ya wuce can cikin kiryar office din don har wani madaidaicin gado ke akwai.
Bayan ya sallame mutumen ya biyosa har cikin dakin ya samai yayi shame shame yana shan iskar AC.
"Ince dai lfy?"
Shan mur malik yayi ya cakude fuskarsa yace"zuwa nai na daukeka idan anyi sallar isha,i zamuje bikon safiyyah"
Tsaki yaja ya na juyawa zaifice b'igit malik yayi ya sha gabansa babu walwala afuskarsa alamun babu wasa yace"Alfah kabar wannan abun,dagaske nake saimunje dakai aikaine musabbabin komi yarinya tana maka abun alkairi........shiru yayi baison tona abun dasukeyi.
Kallonsa yayi yana shafa sumarsa zuwa kasumbarsa yace"metayi mani na alkairin?zagin nawa kokuwa rashin kunyar,aa kila kirana datake dangiya shine abun alkairin,kaga ABDOUL-MALIK karka janyo muyi rigimar da muka jima bamuyi ba nace bazanje ba final"
Ganin shan mur dinsa baiyyi nasara ba yasa ya saki fuskarsa don yatabbata idan ya matsanta zai rikice mashi ne.
"Kaga sorry Alfah,kayi hkr ka rakani to ba dole ma sai kunyi magana ba nizaka raka don Allah."
Cure hannunsa yayi daga kafadarsa ya fice yana tattara abunda zai dauka malik yafito ya daukar mashi jikkar system dinsa,yana cewa"muje yallabai ai kai hukumane saida lallashi"
Bashiri dariya ta kubce mashi ya jefesa da biron hannunsa,sukai dariya sannan suka fito sakatarensa ya rufe office din.
A mota guda sukatai Abdoul ybar tashi nan company,malik babu abunda yake mashi dadi irin canzawar Alfah lokaci guda,duk da yasan bazai taba dawowa kamar wancen lokacin ba,amman kaso sittin daga cikin halayensa sundawo saidai saurin fushin da ya zame masa jiki yanzu wanda ya hade da zafin xuciyarsa,shima nan gaba idan komi ya daidaita yana saka ran fiyah zata gyarasa,inhar Allah yasa suka daidaita kansu.
Shiyake ta mashi hidima tunda suka dawo tunda ga kan ruwan wanka tea dayake sha idan ya fito,kayan sakawa daddare jansa da hira yana sashi ariya baishirya ba.
Wasu riga da wando ne ya fiddo masu masifar kyau,don tunda yadawo daga Australia bai saka suba kuma suna daga cikin sabbin kayan sa daya dawo dasu.
Wandon ruwan kasa brown amman light,sai rigar coffee brown mai hannun links,ya feshesu da turare yana murmushi,tabbas yasan fiyah ta ganshi yau duk kauda kanta saita rude,don ba yabon kai ba abokinsa karshene wajen kyau da daukar wanka.
"Wai saikace wanda zaije zance?"
Dariya malik yayi yace aransa kacanko daidai amman afili sai yace"aa nidai zaka raka nayo bikon qanwata,nasan fushi tayi dani tunda har yanzu her phone is switch off."
"U hmm"
"Don Allah yallabai karkace bazaka rakani ba,nikadai ban iya zuwa,ban san gidan ba"
"Uh zanyi maka kwatance zaka gane"
"Ohhh rankayadade wlh nafison muje tare plsssss kaimun wannan alfarmar"
Kafada yada ga yace "is okay zanje"
Wata kara ya fasa yana daka tsalle murmushi Alfah yayi yana nunasa da hannu"u malik"
Fita yayi shima ya je yashirya suka fita sallar isha,i zanso kuga yadda kayan nan suka hau Alfah,kamshi kurin yake bugawa kamar wani sabon ango.
Bay a sunyi sallar isha,i masallaci sannan malik yafiddo wata jibgegiyar car,wadda sai Alfah yayi wata bai hauba,daman suna dawowa yasaka maigadi ya gogeta don ma rufe tae ba kura tayi sosai ba.
Sanan suka dauki haya Alfah na son fesin cap ita yasaka bisa kansa,ya rufe idinsa da ita,imagining yake yadda haduwar tasu zata kasance,zaiso yaga wadannan idanuwan nata kamar anzuba oil aciki suna daukar ido yaga ya zasuyi,murmushi ya kubce mashi kodawace fuska zata anshesu,yasan shidai mai laifine bama lallai ta kallai ba,amman bazaije yadawo bai saka idonsa cikin nata ba.
Malik kamar anzuba mashi kankara cikin rai ganin yadda aminin nasa yake cikin annashuwa,alamar dai fiyah ta samu wani waje ta zauna aransa.

Munata fira bayan mungama ayyukan mu Anty na can itada umcle yahya suna kallo falo,nida hasana da princess dina muna dakina muna ta hira da daroya,amman har cikin kokon raina banjin dadi,wata irin kewa nakeji wadda banson menake ma kewar ba.saina dauko wayata da niyyar kunna wa saina fa saboda nasan yaya malik zai neman.ikuma so nake na nuna mashi nayi fushi suduka susan babu wani abu cikin raina balle in har nabar zuwa inda suke wani yazargi bzan iya hakanba.princess dake mamulan hannu na kalla hasana kuwa ansa waya take,saukowa nai na nufi falon don anata mama tasha.
"Anty little yunwa takeji,tun dazu fa baki tua da ita ba"
Ansarta tayitana cewa"keta gado shegen tsotso,don haka da wuri zan fara bata cerelac ko priso."
Uncle yahya dake ansa waya ya harareta naji yace"ok Abdoul saika iso"
Kashe wa yayi duk sai naji na zargu wane abdoul din kenan,koda yake ai basu san juna ba kuma bata zaton zai iya zuwa yadda yake jida kansa........"safiyya wanda ya bankeki shekaran jiyane zaizo dubaki jeki gyara falon saukar bakin don Allah."
Wucewa nai jikina yana wana irin sanyi,xuciyata banda zillo babu abunda take,ni narasa wannan sabon yanayi nawa.Anty naji tana tambayarsa"waye kuma haka uncle,badai da biyu xaizo ba don ni nariga nayiwa kanwata miji"
Dariya yayi yace"inma da uku yazo jamila miye naki,ita mace ai Allurace cikin ruwa mairabo yake dauka,kuma shi abokinane sosai rabuwarmu tun school yasa abotar ta rushe,banda wani good friend banda shi,kuma dashi da muhseen babu wanda nake ma bakin cikin samun safiyya,don kuwa duk wanda yasameta zanyi murna su duka duk nawane,kuma kowane babu na banza cikinsu abunda zakiyi mata kawai shine addua da fatan alkairi"
"Uhm,shikenan amman ni gaskiya ina bayan muhseen kuma zan cigaba dayi mashi canpen"
Wucewa nai inajin zuciyata tana karkarwa,wai waye yace dasu wannan arrogant din yana sonta,shi wannan wacece ma zata soshi inbanda zakiyyar,yadda yake dashegen miskilanci da fadin raiAllah yasawake mun auren dangiya.

Mrs bb e
Mom muhseen.
[9/17, 3:38 PM] Fauziya Madaki: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........30
Chapter 36 · 0% Book details