← Book details Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 87

Sashe 33

Abdul Nasser Alfah Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Bayan shigarta gida Anty na ganinta ta ajiye babyn tana nufota cikin masifa zata mareta muhseen yayi saurin tarewa,
"Haba Anty bazaki ji komi ba saidai kihau dukanta,ai ko bakiji bayanin ta ba bakin daki babbar budurwa irin wannan ba,ta wuce bugu ai"
Hararasa tayi tana cewa"tare mata zakai,kigaya man gidan ubanda kika tsaya daman kin tsaranine don kitai yawonki ko,to wlh baruwana dadai irin haka gara ki koma gida yafiye mun kwanciyar hankali."
Uncle yahya yashigo yasamu tana ta balbalin masifa fiyah banda kuka babu abunda take,don bayan bakincikin Alfah ga wani nan tana kwankwada,meyasa anty bata da uxiri koda yaushe.
"Dadina dake bakya da hkr,ko halin data shigo ai kinduba kitambayi lafiya,amman zaki tusata da masifa haba jamila yarinya namaki abun kirki kina neman kureta,safiyya faba yarinya bace tasan kata tanada hankali,bazatayi abunda tasan ranta danaku zaibaci ba.haba wlh banson wannan halin."
Muhseen cikin jin haushin bata ma sahibarsa rai da akai yace"dafa marinta zatai da ban tare ba."
"Mari!jamila saifiyyar zaki mara,lallai kin kyauta ai"
Tashi fiyah tayi tabar wajen cike da bakin ciki tana jiyo muhseen yana mata bayanin abunda yafaru.
Bata tsaya jin abunda antyn za tace ba ta shige ta kulle kofarta,ta kudurci da sassafe zata bar mata gidanta ai hakurinta ya kure,Anty jamila bata da uziri kokadan,indai kayi abu bata jiran bayani zata hau balbalin bala i.to tunkan ta koreni nizan kori kaina,ainaga mata moriya tunda gobe suna ko."
Wannan dare safiyya bata runtsa shi yadda ya kamata ba,kamar yadda Abdoul ya kwana yana cikin wani yanayi na tunani,sunanta yazauna daram cikin ransa.amman zafin kalamanta sun hana sunan yin tasiri aransa,ko kallon malik bai sake ba tun daya dawo.
Sai yakoma ainahin Alfah dinsa na kwanakin baya,wani bangare na zuciyarsa yana tuno masa da wani sashe daya riga ya binne tun shekara shidda baya,saiyakejin kamar feelings na kauna da shauki na soyayya atare dashi,bawai yana yiwa wataba aa yanajinsa atare dashi yana bukatar wadda zai sharing wannan feelings din da ita amman wacece?kenan har xuciyarsa tayi sanyin da zai iya kallon mace da sunan kauna?Aa impossible nayi bikin binne soyayya shekara shidda baya,yana ma mace kallon namiji rabonda dayaji yana son mace kusadashi ko yaji yana bukatar kasancewarta garesa tun wancen lokacin,wanda yakejin kansa koda yaushe cikin shauki da mararin zamanta cikin rayuwarsa.
Yau lamarin ya canza masa,kasancewarta gefensa,kukanta sautin muryarta kalamanta sun ja hankalinsa ainun wajen juyoda lamarinsa baya,wani shauki daya danne tsawon lokaci yake niyyar tasowa,duk da yadda tariga ta bata ransa ta cusa haushinta hakan bai hana wannan abun tasiri akansa ba.
Mirginawa yayi yana runtse idonsa yanajin wani yanayi kamar zaiyyi kuka,amman ba kukan bane yanajin kamar yayi dariya amma ba dariyar bace,yanajin dukan jikinsa yana macewa,sannan tsikar jikinsa tana tashi salon numfashinsa yana canzawa.
Filo ya rarumo ya makalkaleshi yana jan numfashi,ya tattare jikinsa ya dunkulesa waje guda,jujjuya kansa yake yana jiyo wasu kalamai da suka shude suna mashi ansa kuwwa cikin kunne,baiyyi auneba yaji hawayensa suna silalowa suna bin kuncinsa idonsa arufe amman hawayen basu fasa fitanba.
Bakinsa ne yake kerma kamar zaifurta wani abu,amman kirjinsa yayi masa nauyi rubdaciki ya koma yana murtsike murtsike kamar mai ciwon ciki,saida bakinsa ya furta wannan suna ya samu sukuni.

*"ZAKIYYAH!!!"*

wani gauron numfashi ya sauke yana tashi zaune kansa yasa cikin kafafunsa yana zubar da kwallah.
Tun bayan barinsa gida yacireta aransa,daidai da rana guda baiyi tunaninta ba bai tuno komi nata ba,baya kallon mace balle ta tuna mashi da ita,shiyasa ya yiwa mata wata irin tsana.wadda har yau yakejin baidaina tsanar suba,don sune silar jefa rayuwarsa cikin garari da damuwa.
Amman yau anwayi gari shine yake magana da wata,yake hada jikinsa da wata yake daukar wata cikin motarsa.tsawon zamansa hakan bata taba faruwaba,ko dacan zakiyya kurin yake dauka duk da tarin bataliyar matan dake binsa.kusancinsa da yarinyar nan yau yasaka yaji komi na zakiyya yana dawo mashi..........cikin muryar kuka yace"why zakiya,why why me???."
Wannan dare dai Abdoul haka yagansa baisamu sukuni ba saida ya karanta qur ani,sannan yasamu salama har bacci ya daukeshi.

Itako fiyah kiri da muzu baccin yace baisan haka ba,tasha kukanta ta gode waAllah.don gabaki daya tarasa inda natsuwarta ta nufa,duk irin Abunda Abdoul yayi mata yau maimakon taji haushinsa kamar yadda ta dawo da abun,amman abun sai yagagareta data hangoshi sanda yake sunkuyowa yana bude mata kofa zataji gabaki daya hankalinta ya tashi,har lokacin tanajin gashinsa ga fuskarta..........mulmula kurin take agefe guda ga hirarta da zakiyya da irin alkawarin data daukar mata cewar zata mallaka mata Abdoul dinta zata dawo mata da soyayyarta.to taya?ta tanbayi kanta wata xuciyar tace ta yadda kika ansa mata ta haka zaki yi kihadasu ki sasanta su.
Ga haushin Anty ga na Alfah amman jitake na Alfah baikai na Anty girma ba,duk da kalamansa sun take na antyn girma da munu aman ta kasa ganin bakinsu ayanxu,sabanin lokacin dayake gaya mata su.
Tun daren fiyah ta gama hada akwatinta,don data gama abunda xatai saidai ta nemeta ta rasa shikuma wancen muhseen din ya gaji yabarta,inma don yabata wayace aiba rokonsa tayi ba bakuma zata bayar ba,kwata kwata baya cikin shirginta.
Zuciyarta tace mata"to saiwa yake cikin shirginki?badai Abdoul din dakika gama yiwa wata alkawarin hadasu ba?"
"Mtss mezan da dangiya nikau safiyyah,ai inajin ko maza sukenan shida muhseen bana son su bana aurensu gara na mutu ahaka."
Still xuciyarta tace"inkince Abdoul dan giya ne shikuma muhseen mezai hana kisoshi?"
Dirkowa tai daga kan gadon tana cewa"ohh ina ruwanki ne kirabu dani don Allah."
(🤣🤣🤣)
Zaman dirshen tayi kasa tana tagumi.
Tunani ta shiga yi daga sanda ya fito daga mota dawowar da yayi daga office,shigarsa tayi kyau rubutun rigarsa ya dauki hankalinta *ME&YOU* lumshe ido tayi tana silalewa kasa ta kwanta bia tayils din dakin.
"Nida kai ko,uhmmm saidai idan kaida zakiyya"
Idonta alumshe tana tuna sanda yake tsane mata hawayenta,kamshin turatensa mai shegen shiga kwalwa ya kasa barin hancinta.komi nashi mai tsadane.

_kuma duk dan iskan kwartonki daya biyoki nan gidan saina guntile mashi kafa alqur,an_
Chapter 33 · 0% Book details